Nations Bible

1 Crónicas 5

Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ · Toca un versículo para ver sus referencias cruzadas.

Zuriyar Ruben

1’Ya’yan Ruben maza ɗan farin Isra’ila (shi ne ɗan fari, amma sa’ad da ya ƙazantar da gadon auren mahaifinsa, sai aka ba wa ’yancin ɗan farinsa wa ’ya’yan Yusuf maza ɗan Isra’ila; don kada a lissafta shi a tarihin zuriya bisa ga matsayin haihuwarsa, 2ko da yake Yahuda shi ne mafi ƙarfi cikin ’yan’uwansa kuma mai mulki ya fito daga gare shi, ’yancin zaman ɗan fari na Yusuf ne), 3’ya’yan Ruben ɗan farin Isra’ila maza su ne,

Hanok, Fallu, Hezron da Karmi.

4Zuriyar Yowel su ne,

Shemahiya, Gog,

Shimeyi, 5Mika,

Reyahiya, Ba’al,

6da Beyera, wanda Tiglat-Fileser sarkin Assuriya ya ɗauka zuwa zaman bauta. Beyera shi ne shugaban mutanen Ruben.

7Danginsu bisa ga iyalansu da aka jera bisa ga tarihin zuriyarsu su ne,

Yehiyel shi ne sarki, akwai Zakariya, 8da Bela ɗan Azaz. Azaz ɗan Shema daga dangin Yowel.

Yowel ya yi zama a yankin Arower har zuwa Nebo da Ba’al-Meyon. 9Ta waje gabas sun zauna a ƙasar har zuwa bakin hamadan da ya nausa zuwa Kogin Yuferites, domin dabbobinsu sun ƙaru a Gileyad.

10A zamanin Shawulu zuriyar Ruben sun yi yaƙi da Hagirawa, suka ci su da yaƙi, suka zauna a wuraren zaman Hagirawan ko’ina a dukan yankin gabashin Gileyad.

Zuriyar Gad

11Mutanen Gad sun zauna kusa da mutanen Ruben a Bashan, har zuwa Saleka.

12Yowel shi ne babba, sai Shafan na biyu, sa’an nan Yanai da Shafat, su ne tushen Bashan.

13Danginsu, bisa ga iyalai su ne,

Mika’ilu, Meshullam, Sheba, Yorai, Yakan, Ziya da Eber, su bakwai ne duka.

14Waɗannan su ne ’ya’yan Abihayil ɗan Huri, ɗan Yarowa, ɗan Gileyad, ɗan Mika’ilu, ɗan Yeshishai, ɗan Yado, ɗan Buz.

15Ahi ɗan Abiyel, ɗan Guni, shi ne kan iyalinsu.

16Mutanen Gad sun zauna a Bashan da ƙauyukan da suke kurkusa da shi, da kuma a dukan makiyayan Sharon har zuwa iyaka inda suka kai.

17Dukan waɗannan sun shiga tarihin zuriya a lokacin mulkin Yotam sarkin Yahuda da Yerobowam sarkin Isra’ila.

18Mutanen Ruben, mutanen Gad da rabin kabilar Manasse sun kasance da mutane 44,760 shiryayyu don aikin soja, jarumawan da za su iya riƙe garkuwa da takobi, waɗanda suke iya yin amfani da baka, waɗanda kuma aka horar don yaƙi. 19Suka yi yaƙi da Hagirawa, Yetur, Nafish da Nodab. 20Aka taimake su a yaƙin, Allah kuma ya ba da Hagirawa da dukan abokansu gare su, domin sun yi kuka gare shi a lokacin yaƙin. Ya amsa addu’o’insu, domin sun dogara gare shi. 21Suka ƙwace dabbobin Hagirawa, raƙuma dubu hamsin, tumaki dubu ɗari biyu da hamsin da kuma jakuna dubu biyu. Suka kuma kame mutane dubu ɗari ɗaya, 22waɗansu suka mutu, domin yaƙin na Allah ne. Suka zauna a ƙasar har lokacin da aka kai su zaman bauta.

Rabin kabilar Manasse

23Mutanen rabin kabilar Manasse sun yi yawa; suka zauna a ƙasar daga Bashan har zuwa Ba’al-Hermon, wato, zuwa Senir (Dutsen Hermon).

24Waɗannan su ne kawunan iyalansu. Efer, Ishi, Eliyel, Azriyel, Irmiya, Hodawiya da Yadiyel. Su jarumawa ne, sanannu, su ne kuma kawunan iyalansu. 25Amma ba su yi aminci da Allahn kakanninsu ba, suka kuma yi karuwanci ga waɗansu allolin mutanen ƙasar, waɗanda Allah ya hallaka a gabansu. 26Saboda haka Allah na Isra’ila ya zuga ruhun Ful sarkin Assuriya (wato, Tiglat-Fileser sarkin Assuriya), wanda ya kwashe mutanen Ruben, mutanen Gad da rabin kabilar Manasse zuwa zaman bauta. Ya kwashe su zuwa Hala, Habor, Hara da kuma kogin Gozan, inda suke har wa yau.

¿Sabías que…?

Las tribus orientales de Israel

  • Aunque Rubén era el hijo primogénito de Jacob, perdió sus derechos de primogenitura debido a su mala conducta. La primogenitura fue transferida a los hijos de José, mientras que el liderazgo tribal provino con el tiempo de Judá.Fuentes: el propio texto bíblico · Reuben · Joseph (son of Jacob)
  • Las tribus de Rubén, Gad y la media tribu de Manasés se establecieron al este del río Jordán, en los pastizales de Galaad y Basán. Cuando su ejército conjunto de más de 44.000 guerreros clamó a Dios en la batalla, derrotaron a los agarenos y capturaron inmensos rebaños de ganado.Fuentes: el propio texto bíblico · Gilead · Bashan
  • Debido a su posterior infidelidad a Dios, las tribus que vivían al este del Jordán fueron llevadas al exilio por Tiglat-pileser, rey de Asiria, a quien los registros bíblicos también llaman Pul.Fuentes: el propio texto bíblico · Tilgath-pilneser

Notas escritas con ayuda de IA a partir de fuentes abiertas (Theographic Bible Metadata, CC BY-SA 4.0; Easton’s Bible Dictionary, dominio público) y revisadas antes de publicarse.

Lugares de este capítulo

  • Assyria · 36.359, 43.153 · versículos 6, 26
  • Euphrates · Hoy: Euphrates River · 31.004, 47.442 · versículo 9
  • Gilead · Hoy: Gilead 1 · 32.187, 35.692 · versículos 9, 10, 16
  • Bashan · 32.781, 35.935 · versículos 11, 12, 16, 23
  • Mount Hermon · 33.400, 35.850 · versículo 23
  • Senir · Hoy: Mount Hermon · 33.400, 35.850 · versículo 23

Solo aparecen lugares identificados con alta confianza (90 % o más según las fuentes académicas reunidas por OpenBible). Mapa de la época: DARE (Digital Atlas of the Roman Empire), CC BY 4.0; mapa actual: © colaboradores de OpenStreetMap; lugares: OpenBible.info (CC BY 4.0).

Créditos y licencia de esta traducción
Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™
Hausa: Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ (Bible) of Nigeria
copyright © 2009, 2020 Biblica, Inc.
Language: Hausa
Contributor: Biblica, Inc.
An sami wannan aiki a sauƙaƙe a ƙarƙashin lasisin Ƙasa da ƙasa na Lasisin Creative Commons Attribution-ShareAlike 4.0 na Ƙasa da ƙasa (CC BY-SA). Don a ga kwafin wannan lasisi, a ziyarci: http://creativecommons.org/licenses/by-sa/4.0 ko kuma a aika ta wasiƙa zuwa ga Creative Commons, PO Box 1866, Mountain View, CA 94042, USA.
“Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista ta hannun Biblica, Inc., kuma yin amfani da tambarin Biblica® na bukata rubutaccen izinin Biblica, Inc. A ƙarƙashin sharaɗin lasisin CC BY-SA, za ka iya kwafa ka kuma sāke raba wannan aikin da ba a gyaggyara ba muddin ba ka taɓa tambarin nan na Biblica® ba. Idan ka gyara wani kwafi ko ka juya wannan aiki, ta wurin kirkiro da aikin da aka samu, dole ne ka ka cire tambarin Biblica®. A aikin da aka samo, dole ne ka nuna canje-canjen da ka yi, ka kuma nuna aikin haka: “Ainihi aikin ta hannun Biblica, Inc. yana nan kyauta a www.biblica.com da buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki.”
Dole sharaɗin neman izini ya fita a kan kan magana ko kuma a shafi neman izinin aiki kamar haka:
Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™
Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc.
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™
Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc.
“Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini.
“Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission.
Dole kuma a samo aikin da ka yi daga ainihin aikin a ƙarƙashin wannan lasisi (CC BY-SA).
Idan za ka so ka sanar da Biblica, Inc. dangane da juyinka na wannan aiki, sai ka tuntuɓe mu a https://open.bible/contact-us.
This work is made available under the Creative Commons Attribution-ShareAlike 4‪.0 International License (CC BY-SA). To view a copy of this license, visit http://creativecommons.org/licenses/by-sa/4‪.0 or send a letter to Creative Commons, PO Box 1866, Mountain View, CA 94042, USA.
Biblica® is a trademark registered by Biblica, Inc., and use of the Biblica® trademark requires the written permission of Biblica, Inc. Under the terms of the CC BY-SA license, you may copy and redistribute this unmodified work as long as you keep the Biblica® trademark intact. If you modify a copy or translate this work, thereby creating a derivative work, you must remove the Biblica® trademark. On the derivative work, you must indicate what changes you have made and attribute the work as follows: “The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible.”
Notice of copyright must appear on the title or copyright page of the work as follows:
Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™
Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc.
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™
Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc.
“Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini.
“Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission.
You must also make your derivative work available under the same license (CC BY-SA).
If you would like to notify Biblica, Inc. regarding your translation of this work, please contact us at https://open.bible/contact-us.
This translation is made available to you under the terms of the
Creative Commons Attribution Share-Alike license 4.0.
You have permission to share and redistribute this Bible translation in any format and to make reasonable revisions and adaptations of this translation, provided that:
You include the above copyright and source information.
If you make any changes to the text, you must indicate that you did so in a way that makes it clear that the original licensor is not necessarily endorsing your changes.
If you redistribute this text, you must distribute your contributions under the same license as the original.
Pictures included with Scriptures and other documents on this site are licensed just for use with those Scriptures and documents.
For other uses, please contact the respective copyright owners.
Note that in addition to the rules above, revising and adapting God's Word involves a great responsibility to be true to God's Word. See Revelation 22:18-19.
2025-05-03

Fuente: http://ebible.org/hausa/ · eBible.org

Habla con nosotros

Cuéntanos desde dónde lees, cómo te ha ayudado la Biblia o qué podemos mejorar. Leemos todos los mensajes.