1 Crónicas 23
Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ · Toca un versículo para ver sus referencias cruzadas.
Lawiyawa
1Sa’ad da Dawuda ya tsufa yana kuma da cikakken shekaru, ya sa ɗansa Solomon sarki bisa Isra’ila.
2Ya kuma tattara dukan shugabannin Isra’ila a wuri ɗaya, haka kuma ya yi da firistoci da Lawiyawa. 3Aka ƙidaya Lawiyawan da suke ’yan shekaru talatin da haihuwa ko fiye, suka kai wajen mutum dubu talatin da takwas. 4Dawuda ya ce, “Cikin waɗannan, dubu ashirin da huɗu za su lura da aikin haikalin Ubangiji, dubu shida su zama manyan na ma’aikata da alƙalai. 5Dubu huɗu su zama matsaran ƙofofi, dubu huɗu kuma su yabi Ubangiji da kayayyakin bushe-bushe da na kaɗe-kaɗe waɗanda na tanada saboda wannan manufa.”
6Dawuda ya rarraba Lawiyawa ƙungiya-ƙungiya bisa ga ’ya’yan Lawi maza. Gershon, Kohat da Merari.
Gershon
7Na Gershonawa,
Ladan da Shimeyi.
8’Ya’yan Ladan maza su ne,
Yehiyel na farko, Zetam da Yowel, su uku ne duka.
9’Ya’yan Shimeyi maza su ne,
Shelomot, Haziyel da Haran, su uku ne duka.
Waɗannan su ne kawunan iyalan Ladan.
10’Ya’yan Shimeyi maza kuwa su ne,
Yahat, Zina, Yewush da Beriya.
Waɗannan su ne ’ya’yan Shimeyi maza, su huɗu ne duka.
11Yahat shi ne na fari, Ziza kuma na biyu, amma Yewush da Beriya ba su haifi ’ya’ya maza da yawa ba; saboda haka aka ƙidaya su kamar iyali ɗaya a wurin rabon aiki.
Kohatawa
12’Ya’yan Kohat maza su ne,
Amram, Izhar, Hebron da Uzziyel, su huɗu ne duka.
13’Ya’yan Amram maza su ne,
Haruna da Musa.
Haruna shi ne aka keɓe, shi da zuriyarsa har abada, don su tsarkake kayayyakin mafi tsarki, su miƙa hadayu a gaban Ubangiji, su yi hidima a gabansa su kuma furta albarku a cikin sunansa har abada. 14An ƙidaya aka kuma haɗa ’ya’yan Musa maza mutumin Allah a sashen kabilar Lawi.
15’Ya’yan Musa maza su ne,
Gershom da Eliyezer.
16Zuriyar Gershom su ne,
Shebuwel ne ɗan fari.
17Zuriyar Eliyezer su ne,
Rehabiya ne ɗan fari.
Eliyezer ba shi da waɗansu ’ya’ya maza, amma ’ya’yan Rehabiya maza sun yi yawa.
18’Ya’yan Izhar maza su ne,
Shelomit ne ɗan fari.
19’Ya’yan Hebron maza su ne,
Yeriya na fari, Amariya na biyu, Yahaziyel na uku da Yekameyam na huɗu.
20’Ya’yan Uzziyel maza su ne,
Mika na fari da Isshiya na biyu.
Merariyawa
21’Ya’yan Merari maza su ne,
Mali da Mushi.
’Ya’yan Mali maza su ne,
Eleyazar da Kish.
22Eleyazar ya mutu ba ’ya’yan maza, yana da ’ya’ya mata ne kawai. ’Yan’uwansu, ’ya’yan Kish maza, suka aure su.
23’Ya’yan Mushi maza su ne,
Mali, Eder da Yeremot, su uku ne duka.
24Waɗannan ne zuriyar Lawi bisa ga iyalansu, kawunan iyalai kamar yadda aka rubuta su a ƙarƙashin sunayensu aka kuma ƙirga kowa, wato, masu aikin da suke ’yan shekara ashirin da haihuwa ko fiye waɗanda suka yi hidima a cikin haikalin Ubangiji. 25Gama Dawuda ya ce, “Tun da Ubangiji, Allah na Isra’ila, ya ba da hutu ga mutanensa, ya kuma zo ya zauna a Urushalima har abada, 26Lawiyawa ba sa ƙara bukata su ɗauki tabanakul ko kuwa waɗansu kayayyakin da ake amfani da su a hidima.” 27Bisa ga umarnin ƙarshe na Dawuda, za a ƙidaya Lawiyawa daga ’yan shekara ashirin ko fiye.
28Aikin Lawiyawa shi ne su taimaki zuriyar Haruna a hidimar haikalin Ubangiji; su lura da filaye da kuma ɗakunan da suke gefe, su tsarkake dukan kayayyaki masu tsarki, su kuma yi waɗansu ayyuka a gidan Allah. 29Su ne za su lura da burodin da aka ajiye a tebur, lallausan gari don hadaya ta gari, waina marar yisti, toyawa da kwaɓawa, da kuma dukan awon yawa da kuma girman abubuwa. 30Su ne kuma za su tsaya kowace safiya su yi godiya, su kuma yabi Ubangiji. Za su kuma yi haka da yamma 31da kuma a duk sa’ad da aka miƙa hadayun ƙonawa ga Ubangiji a Asabbatai da bukukkuwan Sabon Wata da kuma a ƙayyadaddun bukukkuwa, za su yi hidima a gaban Ubangiji kullum bisa ga yawan da aka tsara da kuma a hanyar da aka tsara musu.
32A haka kuwa Lawiyawa suka yi ayyukansu don Tentin Sujada, don Wuri Mai Tsarki da kuma a ƙarƙashin ’yan’uwansu zuriyar Haruna, saboda hidimar haikalin Ubangiji.

¿Sabías que…?
David Organiza a los Levitas
- Un censo registró a 38.000 levitas de treinta años o más en Israel. David los distribuyó en funciones específicas: 24.000 para supervisar las labores de la casa del Señor, 6.000 como oficiales y jueces, 4.000 como porteros y 4.000 como músicos para alabar a Dios con instrumentos fabricados para ese propósito.Fuentes: el propio texto bíblico
- Dado que el Señor otorgó reposo a Su pueblo y fijó Su morada en Jerusalén, los levitas ya no tenían que transportar el tabernáculo ni sus utensilios. David adaptó sus deberes para asistir a los sacerdotes descendientes de Aarón en el templo y en las alabanzas diarias, estableciendo la edad de servicio a partir de los veinte años.Fuentes: el propio texto bíblico · Jerusalem
- Aunque Aarón y Moisés eran ambos hijos de Amram, del linaje de Coat, sus descendientes tuvieron funciones diferentes. Aarón y su linaje fueron consagrados para siempre al sacerdocio para quemar incienso y bendecir en el nombre del Señor, mientras que los descendientes de Moisés fueron integrados entre las familias levitas generales.Fuentes: el propio texto bíblico · Aaron · Moses
Notas escritas con ayuda de IA a partir de fuentes abiertas (Theographic Bible Metadata, CC BY-SA 4.0; Easton’s Bible Dictionary, dominio público) y revisadas antes de publicarse.
Lugares de este capítulo
- Jerusalem · 31.777, 35.234 · versículo 25
Solo aparecen lugares identificados con alta confianza (90 % o más según las fuentes académicas reunidas por OpenBible). Mapa de la época: DARE (Digital Atlas of the Roman Empire), CC BY 4.0; mapa actual: © colaboradores de OpenStreetMap; lugares: OpenBible.info (CC BY 4.0).
Créditos y licencia de esta traducción
Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Hausa: Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ (Bible) of Nigeria copyright © 2009, 2020 Biblica, Inc. Language: Hausa Contributor: Biblica, Inc. An sami wannan aiki a sauƙaƙe a ƙarƙashin lasisin Ƙasa da ƙasa na Lasisin Creative Commons Attribution-ShareAlike 4.0 na Ƙasa da ƙasa (CC BY-SA). Don a ga kwafin wannan lasisi, a ziyarci: http://creativecommons.org/licenses/by-sa/4.0 ko kuma a aika ta wasiƙa zuwa ga Creative Commons, PO Box 1866, Mountain View, CA 94042, USA. “Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista ta hannun Biblica, Inc., kuma yin amfani da tambarin Biblica® na bukata rubutaccen izinin Biblica, Inc. A ƙarƙashin sharaɗin lasisin CC BY-SA, za ka iya kwafa ka kuma sāke raba wannan aikin da ba a gyaggyara ba muddin ba ka taɓa tambarin nan na Biblica® ba. Idan ka gyara wani kwafi ko ka juya wannan aiki, ta wurin kirkiro da aikin da aka samu, dole ne ka ka cire tambarin Biblica®. A aikin da aka samo, dole ne ka nuna canje-canjen da ka yi, ka kuma nuna aikin haka: “Ainihi aikin ta hannun Biblica, Inc. yana nan kyauta a www.biblica.com da buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki.” Dole sharaɗin neman izini ya fita a kan kan magana ko kuma a shafi neman izinin aiki kamar haka: Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. “Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini. “Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission. Dole kuma a samo aikin da ka yi daga ainihin aikin a ƙarƙashin wannan lasisi (CC BY-SA). Idan za ka so ka sanar da Biblica, Inc. dangane da juyinka na wannan aiki, sai ka tuntuɓe mu a https://open.bible/contact-us. This work is made available under the Creative Commons Attribution-ShareAlike 4.0 International License (CC BY-SA). To view a copy of this license, visit http://creativecommons.org/licenses/by-sa/4.0 or send a letter to Creative Commons, PO Box 1866, Mountain View, CA 94042, USA. Biblica® is a trademark registered by Biblica, Inc., and use of the Biblica® trademark requires the written permission of Biblica, Inc. Under the terms of the CC BY-SA license, you may copy and redistribute this unmodified work as long as you keep the Biblica® trademark intact. If you modify a copy or translate this work, thereby creating a derivative work, you must remove the Biblica® trademark. On the derivative work, you must indicate what changes you have made and attribute the work as follows: “The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible.” Notice of copyright must appear on the title or copyright page of the work as follows: Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. “Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini. “Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission. You must also make your derivative work available under the same license (CC BY-SA). If you would like to notify Biblica, Inc. regarding your translation of this work, please contact us at https://open.bible/contact-us. This translation is made available to you under the terms of the Creative Commons Attribution Share-Alike license 4.0. You have permission to share and redistribute this Bible translation in any format and to make reasonable revisions and adaptations of this translation, provided that: You include the above copyright and source information. If you make any changes to the text, you must indicate that you did so in a way that makes it clear that the original licensor is not necessarily endorsing your changes. If you redistribute this text, you must distribute your contributions under the same license as the original. Pictures included with Scriptures and other documents on this site are licensed just for use with those Scriptures and documents. For other uses, please contact the respective copyright owners. Note that in addition to the rules above, revising and adapting God's Word involves a great responsibility to be true to God's Word. See Revelation 22:18-19. 2025-05-03
Fuente: http://ebible.org/hausa/ · eBible.org