Nations Bible

Titus 3

Litafi Mai-tsarki · Tap a verse to see its cross-references.

1Ka tuna masu su zama masu sadaukar da kai ga masu mulki da masu iko, suyi masu biyayya, su zama a shirye domin kowane kyakkyawan aiki. 2Ka tuna masu kada su zagi kowa, su gujiwa gardama, su bar mutane su bi hanyarsu, su kuma nuna tawali'u ga dukan mutane. 3Domin a da, mu da kan mu marasa tunani ne kuma masu rashin biyayya. Mun kauce hanya muka zama bayi ga sha'awoyin duniya da annashuwa. Mun yi zama a cikin mugunta da kishi. Mu lalatattu ne kuma muna kiyyaya da junanmu. 4Amma da jinkan Allah mai ceton mu da kaunarsa ga 'yan Adam ta bayyana, 5ba saboda wani aikin adalci da muka yi ba, amma sabili da jinkan sa ne ya cece mu. Ya cece mu ta wurin wankewar sabuwar haihuwa da sabuntuwar Ruhu Mai Tsarki. 6Allah ya zubo mana Ruhu Mai Tsarki a wadace ta wurin Yesu Almasihu mai cetonmu. 7Ya yi wannan saboda, bayan mun samu 'yantarwa ta wurin alherinsa, za mu zama magada a cikin begen rai na har abada. 8Wannan amintaccen sako ne. Ina son kayi magana gabagadi game da wadannan abubuwa, yadda dukan wadanda suka bada gaskiya ga Allah za suyi kudirin yin kyawawan ayyuka da Allah ya mika masu. Waddannan abubuwa masu kyau ne da kuma riba ga dukan mutane. 9Amma ka guji gardandami na wofi, da lissafin asali, da husuma da jayayya game da dokoki. Wadannan abubuwa basu da amfani kuma marasa riba. 10Ka ki duk wani dake kawo tsattsaguwa a tsakaninku, bayan ka tsauta masa sau daya ko biyu, 11ka kuma sani cewa wannan mutumin ya kauce daga hanyar gaskiya, yana zunubi kuma ya kayar da kansa. 12Sa'adda na aiki Artimas da Tikikus zuwa wurin ka, kayi hanzari ka same ni a Nikobolis, a can na yi shirin kasancewa a lokacin hunturu. 13Kayi hanzari ka aiko Zinas wanda shi gwani ne a harkar shari'a, da Afolos ta yadda ba zasu rasa komai ba. 14Ya kamata Jama'armu su koyi yadda zasu yi ayyuka masu kyau da zasu biya bukatu na gaggawa yadda ba za suyi zaman banza ba. 15Dukan wadanda suke tare da ni suna gaishe ka. Ka gai da masu kaunar mu a cikin bangaskiya. Alheri ya kasance tare da dukan ku.

Artistic illustration — an interpretation, not a historical record.

Did you know?

Saved for Good Works

  • Paul asks Titus to come to him at Nicopolis, where he has decided to spend the winter. Easton's Bible Dictionary (1897) says that Nicopolis means "city of victory," and that the city meant here was most probably the one in Epirus, built by Augustus Caesar to commemorate his victory at the battle of Actium in 31 B.C. The subscription at the end of the letter calls it "Nicopolis of Macedonia," but the dictionary regards that identification as probably incorrect.Sources: Nicopolis · the Bible text itself
  • So that Titus can leave, Paul plans to send either Artemas or Tychicus. Easton's Bible Dictionary (1897) calls Tychicus an Asiatic Christian and a "faithful minister in the Lord," who traveled with Paul and is also described as having been with him at Rome, from where Paul sent him to Ephesus. Of Artemas, the same dictionary records only the name.Sources: Tychicus · Artemas · the Bible text itself
  • Paul also asks Titus to equip Zenas the lawyer and Apollos so that they will have everything they need. Easton's Bible Dictionary (1897) knows Zenas only as a disciple called "the lawyer," and says that nothing more is known of him. Apollos, it records, was a Jew born in Alexandria, eloquent and well versed in the Scriptures, whom Aquila and Priscilla instructed more fully before he went on to Corinth.Sources: Zenas · Apollos · the Bible text itself

Notes written with AI assistance from open sources (Theographic Bible Metadata, CC BY-SA 4.0; Easton’s Bible Dictionary, public domain) and reviewed before publishing.

Places in this chapter

  • Nicopolis · 39.023, 20.737 · verse 12

Only places identified with high confidence are shown (90% or more according to the scholarly sources compiled by OpenBible). Period map: DARE (Digital Atlas of the Roman Empire), CC BY 4.0; modern map: © OpenStreetMap contributors; places: OpenBible.info (CC BY 4.0).

Credits and license for this translation
Litafi Mai-tsarki
The New Testament in the Hausa language of Nigeria
copyright © 2020 Door43 World Missions Community
Language: Hausa
Translation by: Alakirawa, Bayan, Chrispher Ishaya, Dabere, Dacuhus Timothy Danjuma, Danjay, Danjuma Alfred H, Euang Hediza Naohammed, Franklyn Ukazu Udochukwu, Gideon, Gokop, Habibu, James, Kiash Dachung Butus, Lazarus, Nadaki M. Philip, Nenching, Paul, Rebecca, Rev. Ayuba Taiba, Rev. Cain Yusuf Daniel, Rev. Dalhatu Dambo Ayuba, Rev. Dr. Tambanya Yahaya, Rev. Dr. Yakubu Hassan, Rev. Hannatu Samuel Ndberhukwu, Rev. Ibrahim Kassim, Rev. M. Dan'Amarya, Rev. Yakuba Ayuba
Contributor: Dacuhus Timothy Danjuma, Euang Hediza Naohammed, Kiash Dachung Butus, Nadaki M. Philip, Rev. Ayuba Taiba, Rev. Cain Yusuf Daniel, Rev. Dalhatu Dambo Ayuba, Rev. Dr. Tambanya Yahaya, Rev. Dr. Yakubu Hassan, Rev. Hannatu Samuel Ndberhukwu, Rev. Ibrahim Kassim, Rev. M. Dan'Amarya, Rev. Yakuba Ayuba
This translation is made available to you under the terms of the
Creative Commons Attribution Share-Alike license 4.0.
You have permission to share and redistribute this Bible translation in any format and to make reasonable revisions and adaptations of this translation, provided that:
You include the above copyright and source information.
If you make any changes to the text, you must indicate that you did so in a way that makes it clear that the original licensor is not necessarily endorsing your changes.
If you redistribute this text, you must distribute your contributions under the same license as the original.
Pictures included with Scriptures and other documents on this site are licensed just for use with those Scriptures and documents.
For other uses, please contact the respective copyright owners.
Note that in addition to the rules above, revising and adapting God's Word involves a great responsibility to be true to God's Word. See Revelation 22:18-19.
2020-06-19

Source: http://ebible.org/hauulb/ · eBible.org

Talk to us

Tell us where you read from, how the Bible has helped you, or what we could improve. We read every message.