Nations Bible

Romans 5

Litafi Mai-tsarki · Tap a verse to see its cross-references.

1Tun da shike mun sami barata, sabili da bangaskiya, mun sami salama tare da Allah ta wurin Yesu Almasihu. 2. Ta wurin sa kuma mun sami iso zuwa ga alheri inda muke tsayawa albarkacin bangaskiyarmu. Muna murna da gabagadin da Allah ya ba mu game da abin da zai faru, gabagadin da zamu dandana nan gaba cikin daukakar Allah. 3Ba kuwa haka kadai ba, amma muna murna da shan wahalolinmu. Mun san cewa shan wuya na haifar da 4Jimiri, Jimiri kuma na kawo amincewa, amincewa na kawo gabagadi game da abin da zai zo nan gaba. 5Wannan gabagadi wato begen da muke da shi baya kunyatarwa, domin kuwa an kwarara mana kaunar Allah a cikin zuciyarmu ta wurin Ruhu Mai Tsarki, da aka ba mu. 6Domin kuwa ko yayin da muke raunana, Almasihu ya mutu a lokacin da ke dai dai domin marasa ibada. 7To ai kuwa yana da wuya kwarai wani mutum ya yarda ya mutu don mutumin kirki ma. Watakila, wani na iyayin kasada ya yarda ya mutu don nagarin mutum. 8Amma Allah ya tabbatar mana da kaunarsa a gare mu, don kuwa tun muna masu zunubi, Almasihu ya mutu domin mu. 9Balle ma yanzu, da muka barata ta wurin jininsa, za mu sami tsira daga fushin Allah. 10Domin kuwa, in tun muna makiya, aka sulhunta mu da Allah ta wurin mutuwar Dansa, balle ma, yanzu da muka sami sulhu, zamu sami tsira ta wurin ransa. 11Bama haka kadai ba, amma muna murna a cikin Allah ta wurin Ubangijinmu Yesu Almasihu, wanda ta wurinsa ne muka sami wannan sulhu. 12Saboda haka, kamar yadda ta wurin mutum daya zunubi ya shigo cikin duniya, ta haka mutuwa ta shigo ta dalilin zunubi. 13Domin kuwa tun kafin a bada shari'a, zunubi na nan a duniya, amma ba' a lissafin zunubi in da ba shari'a. 14Duk da haka, mutuwa ta mallake tun daga Adamu har Musa, har ma wadanda basu yi zunubin keta umarni irin na Adamu ba, wanda yake misalin mai zuwan nan a gaba. 15Amma kyautar ba kamar keta umarnin take ba. Domin in sabo da laifin mutum dayan nan ne, da yawa suke mutuwa, haka ma alherin sa da baiwarsa ta wurin mutum dayan nan, Yesu Almasihu, sai baiwar ta wadata zuwa ga masu yawa. 16Domin kyautar ba kamar sakamakon wannan da yayi zunubin bace. Ta haka din nan ne, hukuncin nan mai tsanani ya zo sabo da zunubin mutum dayan. Har yanzu dai, wannan baiwa ta yanci ta zo ne bayan laifuffuka masu yawa. 17Domin, idan sabo da laifin mutum dayan nan ne, mutuwa ta mallake, saboda dayan, haka ma wadanda suka karbi alheri mai yawa da kuma baiwar adalci ta wurin ran, Yesu Almasihu. 18Don haka, kamar yadda zunubin dayan ya sa hukunci ya zo kan dukka, haka ma aikin adalci na dayan zai kawo barata da rai ga mutane masu yawa. 19Kuma kamar yadda rashin biyayyar dayan ta sa mutane masu yawan gaske su zama masu zunubi, haka ma ta biyayyar dayan mutane da yawan gaske za su sami adalci. 20Amma shari'a ta zo, inda ta sa zunubi ya habaka. Amma inda zunubi ya habaka, alheri ma ya habaka ribin ribi. 21Wannan ya faru ne, don kamar yadda zunubi yai mallaka zuwa mutuwa, haka kuma alheri ya mallaka zuwa adalci da rai na har abada ta wurin Yesu Almasihu Ubangijin mu.

Artistic illustration — an interpretation, not a historical record.

Did you know?

Adam, Christ, and the Reign of Grace

  • The one man through whom Romans 5 says sin entered the world, and death through sin, is Adam. A reference note calls Adam a Babylonian word meaning red, the general name for a human being in Hebrew and Assyrian, and links it to his being formed from the dust of the earth. The account of his creation and fall is given in the first book of Moses.Sources: Adam · the Bible text itself
  • Romans 5 says death reigned from Adam until Moses, even over those who did not sin in the way Adam transgressed. It adds that sin was already in the world before the law was given, yet sin is not taken into account when there is no law. Adam is called a pattern of the one who was to come.Sources: the Bible text itself
  • The chapter sets that one trespass beside the gift that came by the grace of Jesus Christ. Judgment after a single sin brought condemnation, while the gift after many trespasses brought justification. The law, it says, came in so that the trespass would increase, yet where sin increased, grace increased all the more.Sources: the Bible text itself

Notes written with AI assistance from open sources (Theographic Bible Metadata, CC BY-SA 4.0; Easton’s Bible Dictionary, public domain) and reviewed before publishing.

Credits and license for this translation
Litafi Mai-tsarki
The New Testament in the Hausa language of Nigeria
copyright © 2020 Door43 World Missions Community
Language: Hausa
Translation by: Alakirawa, Bayan, Chrispher Ishaya, Dabere, Dacuhus Timothy Danjuma, Danjay, Danjuma Alfred H, Euang Hediza Naohammed, Franklyn Ukazu Udochukwu, Gideon, Gokop, Habibu, James, Kiash Dachung Butus, Lazarus, Nadaki M. Philip, Nenching, Paul, Rebecca, Rev. Ayuba Taiba, Rev. Cain Yusuf Daniel, Rev. Dalhatu Dambo Ayuba, Rev. Dr. Tambanya Yahaya, Rev. Dr. Yakubu Hassan, Rev. Hannatu Samuel Ndberhukwu, Rev. Ibrahim Kassim, Rev. M. Dan'Amarya, Rev. Yakuba Ayuba
Contributor: Dacuhus Timothy Danjuma, Euang Hediza Naohammed, Kiash Dachung Butus, Nadaki M. Philip, Rev. Ayuba Taiba, Rev. Cain Yusuf Daniel, Rev. Dalhatu Dambo Ayuba, Rev. Dr. Tambanya Yahaya, Rev. Dr. Yakubu Hassan, Rev. Hannatu Samuel Ndberhukwu, Rev. Ibrahim Kassim, Rev. M. Dan'Amarya, Rev. Yakuba Ayuba
This translation is made available to you under the terms of the
Creative Commons Attribution Share-Alike license 4.0.
You have permission to share and redistribute this Bible translation in any format and to make reasonable revisions and adaptations of this translation, provided that:
You include the above copyright and source information.
If you make any changes to the text, you must indicate that you did so in a way that makes it clear that the original licensor is not necessarily endorsing your changes.
If you redistribute this text, you must distribute your contributions under the same license as the original.
Pictures included with Scriptures and other documents on this site are licensed just for use with those Scriptures and documents.
For other uses, please contact the respective copyright owners.
Note that in addition to the rules above, revising and adapting God's Word involves a great responsibility to be true to God's Word. See Revelation 22:18-19.
2020-06-19

Source: http://ebible.org/hauulb/ · eBible.org

Talk to us

Tell us where you read from, how the Bible has helped you, or what we could improve. We read every message.