Nations Bible

Romans 13

Litafi Mai-tsarki · Tap a verse to see its cross-references.

1Bari kowa yayi biyayya da hukuma, saboda babu wata hukuma sai dai in tazo daga Allah; mahukunta da suke nan kuwa daga Allah ne. 2Saboda da haka duk wanda ya ja hukuma ya ja da dokar Allah; kuma dukan wadanda suka ki hukuma za su sha hukunci. 3Don kuwa mahukunta ba abin tsoro ne ga masu nagarta ba, amma ga masu aikata laifi. Kuna so ku zama marasa tsoron hukuma? Kuyi abu nagari, zaku sami yabo daga yin hakan. 4Saboda shi bawan Allah ne a gare ku don nagarta. Amma in kun yi abu mara kyau, kuyi tsoro, saboda ba ya dauke da takobi ba tare da dalili ba. Don shi bawan Allah ne mai saka wa mugu da fushi. 5Saboda haka dole kuyi biyayya, ba don fushi ba, amma saboda lamiri. 6Saboda wannan ne kuke biyan haraji. Don masu mulki bayin Allah ne, wadanda suke yin haka kullum. 7Ku bawa kowa hakkinsa; haraji ga mai haraji; kudin fito ga mai fito; tsoro ga wanda ya cancanci tsoro; girma ga wanda cancanci girmamawa. 8Kada ku rike bashin kowa, sai dai ku kaunaci juna. Domin duk wanda ya kaunaci dan'uwansa ya cika doka. 9To, “Kada kuyi zina, kada kuyi kisa, kada kuyi sata, kada kuyi kyashi, idan har akwai wata doka kuma, an takaita ta a wannan jimlar: “Ka kaunaci dan'uwanka kamar kanka.” 10Kauna bata cutar da makwabci. Domin haka, kauna tace cikar shari'a. 11Saboda wannan, kun san lokaci yayi, ku farka daga barci. Domin cetonmu yana kusa fiye da yadda muke tsammani. 12Dare yayi nisa, gari ya kusan wayewa. Don haka, sai mu rabu da ayyukan duhu, mu yafa makaman haske. 13Sai muyi tafiya yadda ya kamata, kamar da rana, ba a cikin shashanci ko buguwa ba. Kada kuma muyi tafiya cikin fasikanci da muguwar sha'awa, ba kuma cikin husuma ko kishi ba. 14Amma ku yafa Ubangiji Yesu Almasihu, kada kuwa ku tanadi halin mutumtaka, don biye wa muguwar sha'awarsa.

Did you know?

Authority, Taxes, and the Debt of Love

  • This chapter states that there is no authority except that which is from God, and that the authorities which exist have been appointed by God. Whoever resists authority is described as opposing what God has set in place and as bringing judgment on themselves. Rulers, it says, are not a terror to good conduct, but to bad.Sources: the Bible text itself
  • The ruler is called God’s servant for the good of those addressed, and an agent of retribution to the wrongdoer who does not carry the sword in vain. Submission is presented as necessary not only to avoid punishment but also as a matter of conscience, which is also why taxes are paid to authorities who devote themselves to their work. Each person is to give taxes, revenue, respect, and honor to those to whom they are due.Sources: the Bible text itself
  • The only debt that is to remain is love for one another, for whoever loves his neighbor has fulfilled the law. The commandments against adultery, murder, theft, and coveting, and any other commandments, are summed up in the decree to love one’s neighbor as oneself, because love does no wrong to its neighbor. Readers are told to live this way awake to the hour, laying aside deeds of darkness and clothing themselves with the Lord Jesus Christ, since the night is nearly over and the day has drawn near.Sources: the Bible text itself

Notes written with AI assistance from open sources (Theographic Bible Metadata, CC BY-SA 4.0; Easton’s Bible Dictionary, public domain) and reviewed before publishing.

Credits and license for this translation
Litafi Mai-tsarki
The New Testament in the Hausa language of Nigeria
copyright © 2020 Door43 World Missions Community
Language: Hausa
Translation by: Alakirawa, Bayan, Chrispher Ishaya, Dabere, Dacuhus Timothy Danjuma, Danjay, Danjuma Alfred H, Euang Hediza Naohammed, Franklyn Ukazu Udochukwu, Gideon, Gokop, Habibu, James, Kiash Dachung Butus, Lazarus, Nadaki M. Philip, Nenching, Paul, Rebecca, Rev. Ayuba Taiba, Rev. Cain Yusuf Daniel, Rev. Dalhatu Dambo Ayuba, Rev. Dr. Tambanya Yahaya, Rev. Dr. Yakubu Hassan, Rev. Hannatu Samuel Ndberhukwu, Rev. Ibrahim Kassim, Rev. M. Dan'Amarya, Rev. Yakuba Ayuba
Contributor: Dacuhus Timothy Danjuma, Euang Hediza Naohammed, Kiash Dachung Butus, Nadaki M. Philip, Rev. Ayuba Taiba, Rev. Cain Yusuf Daniel, Rev. Dalhatu Dambo Ayuba, Rev. Dr. Tambanya Yahaya, Rev. Dr. Yakubu Hassan, Rev. Hannatu Samuel Ndberhukwu, Rev. Ibrahim Kassim, Rev. M. Dan'Amarya, Rev. Yakuba Ayuba
This translation is made available to you under the terms of the
Creative Commons Attribution Share-Alike license 4.0.
You have permission to share and redistribute this Bible translation in any format and to make reasonable revisions and adaptations of this translation, provided that:
You include the above copyright and source information.
If you make any changes to the text, you must indicate that you did so in a way that makes it clear that the original licensor is not necessarily endorsing your changes.
If you redistribute this text, you must distribute your contributions under the same license as the original.
Pictures included with Scriptures and other documents on this site are licensed just for use with those Scriptures and documents.
For other uses, please contact the respective copyright owners.
Note that in addition to the rules above, revising and adapting God's Word involves a great responsibility to be true to God's Word. See Revelation 22:18-19.
2020-06-19

Source: http://ebible.org/hauulb/ · eBible.org

Talk to us

Tell us where you read from, how the Bible has helped you, or what we could improve. We read every message.