Revelation 7
Litafi Mai-tsarki · Tap a verse to see its cross-references.
1Bayan wannan sai na ga mala'iku hudu suna tsaye bisa kusurwoyi hudu na duniya, suka rike iskoki hudu na duniya kamkam domin kada iska ta hura a kan duniya, a kan teku, ko wani itace. 2Sai na ga wani mala'ika na zuwa daga gabas, wanda yake da hatimin Allah mai rai. Ya yi kira da babbar murya da mala'ikun nan hudu da aka basu dama su azabtar da duniya da teku: 3“Kada ku azabtar da duniya, da teku, da itatuwa har sai mun sa hatimi bisa goshin bayin Allahnmu.” 4Sai naji yawan wadanda aka hatimce: 144, 000, wadanda aka hatimce daga kowacce kabilar mutanen Isra'ila: 5dubu goma sha biyu aka hatimce daga kabilar Yahuza, dubu goma sha biyu daga kabilar Ra'ubainu, dubu goma sha biyu daga kabilar Gad, 6dubu goma sha biyu daga kabilar Ashiru, dubu goma sha biyu daga kabilar Naftali, dubu goma sha biyu daga kabilar Manassa. 7Dubu goma sha biyu daga kabilar Saminu, dubu goma sha biyu daga kabilar Lawi, dubu goma sha biyu daga kabilar Issaka, 8dubu goma sha biyu daga kabilar zabaluna, dubu goma sha biyu daga kabilar Yusufu, sai kuma dubu goma sha biyu daga kabilar Bilyaminu aka hatimce. 9Bayan wadannan abubuwa na duba, sai ga wani babban taro wanda ba mai iya kirgawa daga kowacce al'umma, kabila, mutane da harsuna tsaye a gaban kursiyin da gaban Dan Ragon. Suna sanye da fararen tufafi da ganyen dabino a hannuwansu, 10kuma suna kira da murya mai karfi: “Ceto ya tabbata ga Allahnmu wanda ke zaune bisa kursiyi, da kuma Dan Ragon!” 11Dukan mala'iku suna tsaitsaye kewaye da kursiyin kuma kewaye da dattawan nan da kuma rayayyun halittun nan hudu, suka kwanta rib da ciki da fuskokinsu a gaban kursiyin. Suka yi sujada ga Allah, 12suna cewa, “Amin! yabo, daukaka, hikima, godiya, girma, iko, da karfi su zama na Allahnmu har abada abadin! Amin!” 13Sai daya daga cikin dattawan ya tambaye ni, “Su wanene wadannan, da suke sanye da fararen tufafi, kuma daga ina suka fito?” 14Sai nace masa, “Ya shugaba, “Ka sani,” sai ya ce mani, “Wadannan sune suka fito daga babban tsanani. Sun wanke tufafin su sun maida su farare cikin jinin Dan Ragon. 15Domin wannan dalili, suke gaban kursiyin Allah, kuma suna masa sujada dare da rana cikin haikalinsa. Shi wanda ke zaune bisa kursiyin zai zama runfa a bisan su. 16Ba za su kara jin yunwa ba, ko kishin ruwa ba. Rana ba zata buge su ba, ko kowanne zafi mai kuna. 17Domin Dan Ragon dake tsakiyar kursiyin zai zama makiyayin su, kuma zai bishe su zuwa mabulbulan ruwan rai, kuma Allah zai share dukan hawaye daga idanuwansu.”

Did you know?
The sealed tribes and the great multitude
- Revelation 7 numbers the sealed as 144,000, twelve thousand from each of the tribes of Israel named in the chapter. Israel was another name for Jacob, the second-born of the twin sons of Isaac and Rebekah; Easton's Bible Dictionary (1897) explains Jacob's name as someone who follows on another's heels, or a supplanter.Sources: the Bible text itself · Jacob (Israel)
- Although Reuben was the eldest son of Jacob and Leah, the list of the sealed begins with Judah and then names Reuben. The list also includes both Joseph and Manasseh; Manasseh was Joseph's elder son, and Jacob adopted him and his brother Ephraim as his own sons.Sources: the Bible text itself · Reuben · Manasseh (son of Joseph)
- After the sealing, the vision shows a multitude too large to count, from every nation, tribe, people, and tongue, standing before the throne and the Lamb, wearing white robes and holding palm branches. One of the elders says they have come out of the great tribulation and have washed their robes and made them white in the blood of the Lamb.Sources: the Bible text itself
Notes written with AI assistance from open sources (Theographic Bible Metadata, CC BY-SA 4.0; Easton’s Bible Dictionary, public domain) and reviewed before publishing.
Credits and license for this translation
Litafi Mai-tsarki The New Testament in the Hausa language of Nigeria copyright © 2020 Door43 World Missions Community Language: Hausa Translation by: Alakirawa, Bayan, Chrispher Ishaya, Dabere, Dacuhus Timothy Danjuma, Danjay, Danjuma Alfred H, Euang Hediza Naohammed, Franklyn Ukazu Udochukwu, Gideon, Gokop, Habibu, James, Kiash Dachung Butus, Lazarus, Nadaki M. Philip, Nenching, Paul, Rebecca, Rev. Ayuba Taiba, Rev. Cain Yusuf Daniel, Rev. Dalhatu Dambo Ayuba, Rev. Dr. Tambanya Yahaya, Rev. Dr. Yakubu Hassan, Rev. Hannatu Samuel Ndberhukwu, Rev. Ibrahim Kassim, Rev. M. Dan'Amarya, Rev. Yakuba Ayuba Contributor: Dacuhus Timothy Danjuma, Euang Hediza Naohammed, Kiash Dachung Butus, Nadaki M. Philip, Rev. Ayuba Taiba, Rev. Cain Yusuf Daniel, Rev. Dalhatu Dambo Ayuba, Rev. Dr. Tambanya Yahaya, Rev. Dr. Yakubu Hassan, Rev. Hannatu Samuel Ndberhukwu, Rev. Ibrahim Kassim, Rev. M. Dan'Amarya, Rev. Yakuba Ayuba This translation is made available to you under the terms of the Creative Commons Attribution Share-Alike license 4.0. You have permission to share and redistribute this Bible translation in any format and to make reasonable revisions and adaptations of this translation, provided that: You include the above copyright and source information. If you make any changes to the text, you must indicate that you did so in a way that makes it clear that the original licensor is not necessarily endorsing your changes. If you redistribute this text, you must distribute your contributions under the same license as the original. Pictures included with Scriptures and other documents on this site are licensed just for use with those Scriptures and documents. For other uses, please contact the respective copyright owners. Note that in addition to the rules above, revising and adapting God's Word involves a great responsibility to be true to God's Word. See Revelation 22:18-19. 2020-06-19
Source: http://ebible.org/hauulb/ · eBible.org