Nations Bible

Revelation 3

Litafi Mai-tsarki · Tap a verse to see its cross-references.

1“Zuwa ga mala'ikan ikilisiyar Sardisu rubuta: ' Wadannan ne kalmomin wanda yake rike da ruhohi bakwai na Allah da taurari bakwai. “Na san abin da ka aikata. Ka yi suna cewa kana raye amma kai mattacce ne. 2Ka farka ka karfafa abin da ya rage amma ya kusan mutuwa, domin ban sami ayyukanka cikakku a gaban Allahna ba. 3Domin haka sai ka tuna, da abubuwan da ka karba kuma kaji. Ka yi biyayya da su, ka kuma tuba. Amma idan baka farka ba, zan zo maka kamar barawo, kuma ba zaka farga da sa'ar da zan zo gaba da kai ba. 4Amma akwai sunayen mutane kadan a Sardisu wadanda basu kazantar da tufafinsu ba. Za su yi tafiya tare da ni sanye da fararen tufafi domin sun cancanta. 5Wanda ya yi nasara za a sanya mashi fararen tufafi, kuma ba zan taba share sunansa ba daga Littafin Rai, kuma zan fadi sunansa a gaban Ubana, da kuma gaban mala'ikunsa. 6Bari wanda yake da kunne ya saurari abin da Ruhu ke fadawa ikilisiyoyi.”'” 7Zuwa ga mala'ikan ikilisiyar cikin Filadelfiya rubuta: kalmomin wanda yake maitsarki ne kuma mai gaskiya - yana rike da mabudin Dauda, yana budewa babu mai rufewa, kuma inda ya rufe ba mai budewa. 8Na san abin da ka aikata. Duba, na sa budaddiyar kofa a gabanka wanda ba mai iya rufewa. Na san kana da karamin karfi, duk da haka ka yi biyayya da maganata kuma baka yi musun sunana ba. 9Duba! Wadanda ke na majami'ar Shaidan, wadanda suke cewa su Yahudawa ne; amma maimakon haka karya suke yi. Zan sa su zo su rusuna a kafafunka, kuma za su san cewa ina kaunarka. 10Tun da ka jure cikin hakuri ka kiyaye dokoki na, ni ma zan kiyaye ka daga sa'a ta gwaji da zata sauko kan dukan duniya, domin a gwada mazauna duniya. 11Ina zuwa da sauri. Ka rike abin da kake da shi kamkam domin kada wani ya dauke maka rawani. 12Zan sa wanda ya yi nasara ya zama ginshiki a haikalin Allahna, kuma ba zai taba fita daga cikin sa ba. Zan rubuta sunan Allahna a kansa, sunan birnin Allahna (sabuwar Urushalima, mai saukowa daga sama daga wurin Allahna), da kuma sabon sunana. 13Bari wanda yake da kunne ya ji abin da Ruhu ke gayawa ikilisiyoyi.” 14“Zuwa ga mala'ikan ikilisiyar da ke Lawudikiya rubuta: 'Wadannan sune kalmomin Amin, madogara da mai shaidar gaskiya, mai mulki bisa hallittar Allah. 15Na san abin da ka aikata, ba ka sanyi ko zafi. Naso ko da kana sanyi ko zafi! 16Amma saboda kai tsaka-tsaka ne - ba zafi ba sanyi - na kusa tofar da kai daga bakina. 17Domin ka ce, “Ni mai arziki ne, na mallaki kadarori da yawa, ba na bukatar komai.” Amma ba ka sani ba kana cike da takaici ne, abin tausayi, matalauci, makaho kuma tsirara kake. 18Saurari shawara ta: Ka sayi zinariya a wuri na wadda aka goge da wuta domin ka zama mai arziki, domin ka suturta kanka da fararen tufafi masu kyalli domin kada ka nuna kunyar tsiraicin ka, da mai domin ka shafa wa idanunka ka sami gani. 19Ina horar da duk wanda nake kauna, ina kuma koya masu yadda za su yi rayuwa. Saboda haka, ka himmatu ka tuba. 20Duba, ina tsaye a bakin kofa ina kwankwasawa. Idan wani ya ji muryata ya bude kofar, zan shigo cikin gidansa, in ci tare da shi, shi kuma tare da ni. 21Wanda ya ci nasara, zan bashi dama ya zauna tare da ni bisa kursiyina, kamar yadda nima na ci nasara kuma na zauna da Ubana a kan kursiyinsa. 22Bari wanda yake da kunne ya saurari abin da Ruhu yake fadawa wa ikilisiyoyi.”

Artistic illustration — an interpretation, not a historical record.

Did you know?

Letters to Sardis, Philadelphia, and Laodicea

  • Revelation 3 is a set of letters to churches in three cities of Asia Minor. Sardis, the metropolis of Lydia, stood on the river Pactolus at the foot of Mount Tmolus. Philadelphia, a name that means “brotherly love,” lay about twenty-five miles southeast of Sardis, while Laodicea stood on the Lycus, where Phrygia and Lydia meet, about forty miles east of Ephesus.Sources: Sardis · Philadelphia · Laodicea · the Bible text itself
  • Laodicea was first called Diospolis and then Rhoas. It was later named Laodicea after Laodice, the wife of Antiochus II, king of Syria, who rebuilt it. Easton's Bible Dictionary (1897) calls it one of the most important and flourishing cities of Asia Minor and an early leading center of Christianity; in the letter, that church is said to claim that it is rich, has grown wealthy, and needs nothing.Sources: Laodicea · the Bible text itself
  • The letter to Philadelphia speaks of a “synagogue of Satan” and of people who claim to be Jews but whom it calls liars. Satan means “adversary” or “accuser,” and in the New Testament the name is used interchangeably with the devil.Sources: Satan · the Bible text itself

Notes written with AI assistance from open sources (Theographic Bible Metadata, CC BY-SA 4.0; Easton’s Bible Dictionary, public domain) and reviewed before publishing.

Places in this chapter

  • Sardis · 38.488, 28.040 · verses 1, 4
  • Philadelphia · Today: Alaşehir · 38.350, 28.517 · verse 7
  • Jerusalem · 31.777, 35.234 · verse 12
  • Laodicea · Today: Laodicea on the Lycus · 37.836, 29.108 · verse 14

Only places identified with high confidence are shown (90% or more according to the scholarly sources compiled by OpenBible). Period map: DARE (Digital Atlas of the Roman Empire), CC BY 4.0; modern map: © OpenStreetMap contributors; places: OpenBible.info (CC BY 4.0).

Credits and license for this translation
Litafi Mai-tsarki
The New Testament in the Hausa language of Nigeria
copyright © 2020 Door43 World Missions Community
Language: Hausa
Translation by: Alakirawa, Bayan, Chrispher Ishaya, Dabere, Dacuhus Timothy Danjuma, Danjay, Danjuma Alfred H, Euang Hediza Naohammed, Franklyn Ukazu Udochukwu, Gideon, Gokop, Habibu, James, Kiash Dachung Butus, Lazarus, Nadaki M. Philip, Nenching, Paul, Rebecca, Rev. Ayuba Taiba, Rev. Cain Yusuf Daniel, Rev. Dalhatu Dambo Ayuba, Rev. Dr. Tambanya Yahaya, Rev. Dr. Yakubu Hassan, Rev. Hannatu Samuel Ndberhukwu, Rev. Ibrahim Kassim, Rev. M. Dan'Amarya, Rev. Yakuba Ayuba
Contributor: Dacuhus Timothy Danjuma, Euang Hediza Naohammed, Kiash Dachung Butus, Nadaki M. Philip, Rev. Ayuba Taiba, Rev. Cain Yusuf Daniel, Rev. Dalhatu Dambo Ayuba, Rev. Dr. Tambanya Yahaya, Rev. Dr. Yakubu Hassan, Rev. Hannatu Samuel Ndberhukwu, Rev. Ibrahim Kassim, Rev. M. Dan'Amarya, Rev. Yakuba Ayuba
This translation is made available to you under the terms of the
Creative Commons Attribution Share-Alike license 4.0.
You have permission to share and redistribute this Bible translation in any format and to make reasonable revisions and adaptations of this translation, provided that:
You include the above copyright and source information.
If you make any changes to the text, you must indicate that you did so in a way that makes it clear that the original licensor is not necessarily endorsing your changes.
If you redistribute this text, you must distribute your contributions under the same license as the original.
Pictures included with Scriptures and other documents on this site are licensed just for use with those Scriptures and documents.
For other uses, please contact the respective copyright owners.
Note that in addition to the rules above, revising and adapting God's Word involves a great responsibility to be true to God's Word. See Revelation 22:18-19.
2020-06-19

Source: http://ebible.org/hauulb/ · eBible.org

Talk to us

Tell us where you read from, how the Bible has helped you, or what we could improve. We read every message.