Revelation 22
Litafi Mai-tsarki · Tap a verse to see its cross-references.
1Sai mala'ika ya nuna mani kogin ruwan rai, ruwa mai tsabta. Yana fitowa daga cikin kursiyin Allah da na Dan-Rago 2ta tsakiyar titin birnin. A kowanne gefen kogin akwai itacen rai, mai ba da 'ya'ya iri goma sha biyu, kowanne wata. Ganyayen itacen kuma domin warkar da al'ummai ne. 3Babu sauran la'ana nan gaba. Kursiyin Allah da na Dan Rago za su kasance a cikin birnin, bayinsa kuma za su yi masa bauta. 4Za su ga fuskarsa, sunansa kuma zai kasance a goshinsu. 5Babu sauran dare; ba za su bukaci hasken fitila ko hasken rana ba gama Ubangiji Allah zai haskaka su. Za su yi mulki har abada abadin. 6Mala'ika ya ce mani, “Wadannan kalmomi amintattu ne da gaskiya. Ubangiji, Allah na ruhohin annabawa, ya aiki mala'ikansa ya nuna wa bayinsa abin da lallai zai faru ba da dadewa ba”. 7“Duba! Ina zuwa ba da dadewa ba! Mai albarka ne wanda ya yi biyayya da kalmomin littafin nan.” 8Ni, Yahaya, nine na ji na kuma ga wadannan abubuwa. Sa'adda na ji na gan su, sai na fadi gaban kafaffun mala'ikan da ya nuna mani wadannan abubuwa domin in yi masa sujada. 9Ya ce mani, “Kada ka yi haka! Ni abokin bauta ne tare da kai, tare da 'yan'uwanka annabawa, da wadanda ke biyayya da kalmomin littafin nan. Yi sujada ga Allah!” 10Ya ce mani, “Kada ka rufe kalmomin anabcin littafin nan, gama lokaci ya kusa. 11Wanda yake mara adalci, bari ya cigaba da yin rashin adalci. Wanda yake mai kazanta bari ya cigaba da kazantar da kansa. Wanda yake mai adalci bari ya cigaba da yin adalci. Wanda yake mai-tsarki, bari yaci gaba da tsarki.” 12“Duba! Ina zuwa ba da dadewa ba. Sakamakona na tare da ni, zan saka wa kowa gwargwadon aikin da ya yi. 13Nine Alpha da Omega, farko da karshe, mafarin abu da karshensa. 14Masu albarka ne wadanda suka wanke rigunansu domin su sami izini su ci daga itacen rai su kuma shiga birnin ta kofofinsa. 15A waje akwai karnuka, masu sihiri, masu bautar gumaka, fasikai, masu kisan kai, da duk wanda yake kaunar aikata rashin gaskiya. 16Ni, Yesu na aiko mala'ikana ya shaida maku wadannan abubuwa saboda ikilisiyoyi. Nine tushe da zuriyar Dauda, tauraron asubahi mai-haske.” 17Ruhu da Amarya suka ce, “Zo!” Bari wanda ya ji ya ce, “Zo!” Kowanne mai jin kishi, da kowanne mai bukatar ta, bari ya sami ruwan rai kyauta. 18Ina shaida wa duk mai jin kalmomin anabcin wannan littafi: Idan wani ya kara a kansu, Allah zai kara masa annoban da ke rubuce a cikin littafin. 19Idan wani ya rage daga kalmomin wannan littafin anabci, Allah zai rage rabonsa daga cikin itacen rai daga cikin birni mai-tsarki, wadanda aka rubuta cikin wannan littafi. 20Shi wanda ya shaida wadannan abubuwa ya ce, “I! Ina zuwa ba da dadewa ba.” Amin! Zo, Ubangiji Yesu! 21Alherin Ubangiji Yesu ya kasance tare da kowanne dayanku. Amin.
Did you know?
The city of life and the Lord who is coming
- The angel shows a river of the water of life, clear as crystal, flowing from the throne of God and of the Lamb down the middle of the city’s main street, with a tree of life on either side bearing twelve kinds of fruit, a fresh crop each month, and leaves for the healing of the nations. The chapter also says there will no longer be any curse or night, for the Lord God will shine on his servants, and they will reign forever and ever.Sources: the Bible text itself
- Jesus calls himself the Root and the Offspring of David, and the bright Morning Star. The entry on David introduces him as Beloved, the eighth and youngest son of Jesse, a citizen of Bethlehem, whose early work was tending his father’s sheep on the uplands of Judah.Sources: the Bible text itself · David
- The speaker says, “I am John, who heard and saw these things,” and tells how he fell down to worship at the feet of the angel who had shown them to him. The angel refused, calling himself a fellow servant with John and with John’s brothers the prophets, and with those who keep the words of this book, and said, “Worship God!”Sources: the Bible text itself
Notes written with AI assistance from open sources (Theographic Bible Metadata, CC BY-SA 4.0; Easton’s Bible Dictionary, public domain) and reviewed before publishing.
Credits and license for this translation
Litafi Mai-tsarki The New Testament in the Hausa language of Nigeria copyright © 2020 Door43 World Missions Community Language: Hausa Translation by: Alakirawa, Bayan, Chrispher Ishaya, Dabere, Dacuhus Timothy Danjuma, Danjay, Danjuma Alfred H, Euang Hediza Naohammed, Franklyn Ukazu Udochukwu, Gideon, Gokop, Habibu, James, Kiash Dachung Butus, Lazarus, Nadaki M. Philip, Nenching, Paul, Rebecca, Rev. Ayuba Taiba, Rev. Cain Yusuf Daniel, Rev. Dalhatu Dambo Ayuba, Rev. Dr. Tambanya Yahaya, Rev. Dr. Yakubu Hassan, Rev. Hannatu Samuel Ndberhukwu, Rev. Ibrahim Kassim, Rev. M. Dan'Amarya, Rev. Yakuba Ayuba Contributor: Dacuhus Timothy Danjuma, Euang Hediza Naohammed, Kiash Dachung Butus, Nadaki M. Philip, Rev. Ayuba Taiba, Rev. Cain Yusuf Daniel, Rev. Dalhatu Dambo Ayuba, Rev. Dr. Tambanya Yahaya, Rev. Dr. Yakubu Hassan, Rev. Hannatu Samuel Ndberhukwu, Rev. Ibrahim Kassim, Rev. M. Dan'Amarya, Rev. Yakuba Ayuba This translation is made available to you under the terms of the Creative Commons Attribution Share-Alike license 4.0. You have permission to share and redistribute this Bible translation in any format and to make reasonable revisions and adaptations of this translation, provided that: You include the above copyright and source information. If you make any changes to the text, you must indicate that you did so in a way that makes it clear that the original licensor is not necessarily endorsing your changes. If you redistribute this text, you must distribute your contributions under the same license as the original. Pictures included with Scriptures and other documents on this site are licensed just for use with those Scriptures and documents. For other uses, please contact the respective copyright owners. Note that in addition to the rules above, revising and adapting God's Word involves a great responsibility to be true to God's Word. See Revelation 22:18-19. 2020-06-19
Source: http://ebible.org/hauulb/ · eBible.org