Nations Bible

Revelation 20

Litafi Mai-tsarki · Tap a verse to see its cross-references.

1Sai na ga mala'ika na saukowa daga sama. Yana da makullin rami marar iyaka, yana kuma da babar sarka a hannunsa. 2Sai ya dauki tsohon macijin, wanda shine iblis, ko shaidan, ya daure shi shekaru dubu. 3Ya jefa shi cikin rami marar iyaka, ya rufe shi ya kuma sa hatimi a bisansa. Hakan ya faru ne domin kada ya kara yaudarar al'ummai har sai bayan shekaru dubu. Bayan wannan, dole a sake shi na dan lokaci. 4Sa'annan na ga kursiyoyi. Wadanda ke zaune a bisansu sune wadanda aka ba ikon hukunci. Na kuma ga rayukan wadanda aka fille wa kai saboda shaidar Yesu da maganar Allah. Ba su yi wa dabban sujada ba ko siffarsa, suka ki su karbi alamar a goshinsu ko a hannu. Sun sake rayuwa, suka yi mulki tare da Kristi shekaru dubu. 5Sauran matattun basu sake dawowa da rai ba har sai da shekaru dubu din suka cika. Wannan shine tashin matattu na fari. 6Mai albarka ne mai tsarki ne kuma wanda yake da rabo cikin tashin matattu na fari! Mutuwa ta biyu ba ta da iko akan wadannan. Za su zama firistocin Allah da na Almasihu za su kuma yi mulki tare da shi shekaru dubu. 7Sa'adda shekaru dubu suka zo ga karshe, za a saki shaidan daga kurkukunsa. 8Za ya fito domin ya yaudari al'ummai da ke kursuyoyi hudu na duniya, Gog da Magog ya tattara su domin yaki. Yawan su zai zama kamar yashin teku. 9Suka bazu a fuskar duniya suka kuma kewaye sansanin masu ba da gaskiya, kaunataccen birni. Amma wuta ta sauko daga sama ta lankwame su. 10Shaidan, wanda ya yaudare su, aka jefa shi cikin korama ta farin wuta mai ci, inda aka jefa dabban da makaryacin annabin. Za su sha azaba dare da rana har abada abadin. 11Sai na ga babban kursiyi da wanda ke zaune a kansa. Duniya da sama suka guje wa fuskarsa, amma babu wurin da za su tafi. 12Na ga matattu manya da kanana- suna tsaye gaban kursiyin, aka bude litattafai. Sai aka bude wani littafi - Littafin rai. Aka yi wa matattu shari'a bisa ga abinda aka rubuta cikin litattafan, gwargwadon ayyukansu. 13Teku ta ba da matattun dake cikinta. Mutuwa da hades suka ba da matattun da ke cikinsu, aka yi masu shari'a gwargwadon abin da suka yi. 14Aka jefa mutuwa da hades cikin tafkin wuta. Wannan shine mutuwa ta biyu - tafkin wuta. 15Duk wanda ba a sami sunansa a rubuce cikin littafin rai ba, aka jefar da shi cikin tafkin wuta.

Did you know?

A Thousand Years and the Great White Throne

  • The figure bound for a thousand years is called the dragon, that ancient serpent, the devil, and Satan. Satan means adversary or accuser, and in the New Testament the name is used interchangeably with Diabolos, or the devil; Easton's Bible Dictionary (1897) notes that he is also called the dragon and the old serpent in Revelation 12:9 and 20:2.Sources: Satan · the Bible text itself
  • When the thousand years are complete, the nations assembled for battle are named Gog and Magog. In Genesis, Magog is the second of the sons of Japheth; in Ezekiel, Gog leads a hostile host from the north country, and Magog is a nation that Easton's Bible Dictionary (1897) describes as probably a Scythian or Tartar people, skilled horsemen and experts with the bow.Sources: Magog · Gog · the Bible text itself
  • Jerome, cited by Easton's Bible Dictionary (1897), took Magog to mean fierce and innumerable Scythian nations living beyond the Caucasus and Lake Maeotis, near the Caspian Sea and onward toward India. The same entry treats the vision of Gog and Magog in Revelation 20:8 as, in substance, a reannouncement of Ezekiel's prophecy, and regards proposed links with the Maccabees' wars against Antiochus, with the Chaldeans, or with the Turks as unsatisfactory and inadequate.Sources: Magog · Magog · Gog

Notes written with AI assistance from open sources (Theographic Bible Metadata, CC BY-SA 4.0; Easton’s Bible Dictionary, public domain) and reviewed before publishing.

Places in this chapter

  • Gog · Today: Lydia · 38.488, 28.040 · verse 8

Only places identified with high confidence are shown (90% or more according to the scholarly sources compiled by OpenBible). Period map: DARE (Digital Atlas of the Roman Empire), CC BY 4.0; modern map: © OpenStreetMap contributors; places: OpenBible.info (CC BY 4.0).

Credits and license for this translation
Litafi Mai-tsarki
The New Testament in the Hausa language of Nigeria
copyright © 2020 Door43 World Missions Community
Language: Hausa
Translation by: Alakirawa, Bayan, Chrispher Ishaya, Dabere, Dacuhus Timothy Danjuma, Danjay, Danjuma Alfred H, Euang Hediza Naohammed, Franklyn Ukazu Udochukwu, Gideon, Gokop, Habibu, James, Kiash Dachung Butus, Lazarus, Nadaki M. Philip, Nenching, Paul, Rebecca, Rev. Ayuba Taiba, Rev. Cain Yusuf Daniel, Rev. Dalhatu Dambo Ayuba, Rev. Dr. Tambanya Yahaya, Rev. Dr. Yakubu Hassan, Rev. Hannatu Samuel Ndberhukwu, Rev. Ibrahim Kassim, Rev. M. Dan'Amarya, Rev. Yakuba Ayuba
Contributor: Dacuhus Timothy Danjuma, Euang Hediza Naohammed, Kiash Dachung Butus, Nadaki M. Philip, Rev. Ayuba Taiba, Rev. Cain Yusuf Daniel, Rev. Dalhatu Dambo Ayuba, Rev. Dr. Tambanya Yahaya, Rev. Dr. Yakubu Hassan, Rev. Hannatu Samuel Ndberhukwu, Rev. Ibrahim Kassim, Rev. M. Dan'Amarya, Rev. Yakuba Ayuba
This translation is made available to you under the terms of the
Creative Commons Attribution Share-Alike license 4.0.
You have permission to share and redistribute this Bible translation in any format and to make reasonable revisions and adaptations of this translation, provided that:
You include the above copyright and source information.
If you make any changes to the text, you must indicate that you did so in a way that makes it clear that the original licensor is not necessarily endorsing your changes.
If you redistribute this text, you must distribute your contributions under the same license as the original.
Pictures included with Scriptures and other documents on this site are licensed just for use with those Scriptures and documents.
For other uses, please contact the respective copyright owners.
Note that in addition to the rules above, revising and adapting God's Word involves a great responsibility to be true to God's Word. See Revelation 22:18-19.
2020-06-19

Source: http://ebible.org/hauulb/ · eBible.org

Talk to us

Tell us where you read from, how the Bible has helped you, or what we could improve. We read every message.