Mark 9
Litafi Mai-tsarki · Tap a verse to see its cross-references.
1Sai ya ce masu, “Hakika, ina gaya maku, akwai wasun ku anan da ba za su mutu ba, sai sun ga mulkin Allah ya bayyana da iko.” 2Bayan kwana shida Yesu ya dauki Bitrus, da Yakubu, da Yahaya, ya kai su kan wani dutse mai tsawo, su kadai. Sai kamaninsa ya sake a gabansu. 3Sai tufafinsa ya zama fari fat, yadda ba mai rinin da zai iya rininsa haka a duniya. 4Sai Iliya da Musa suka bayyana gare su, suna magana da Yesu. 5Sai Bitrus ya amsa ya ce, malam, bari mu da muke anan mu kafa bukka uku, daya ta ka, daya ta Musa, da ta Iliya, 6Ya rasa abin da zai fada ne, don sun tsorota kwarai.) 7Sai ga wani gajimare ya zo ya rufe su, aka kuma ji wata murya daga gajimaren, “ta ce Wannan shine kaunataccen Dana, Ku saurare shi. 8Nan take da suka duba, ba su ga kowa ba, sai Yesu shi kadai. 9Suna cikin gangarowa daga dutsen, sai ya kwabe su kada su gaya wa kowa abin da suka gani, sai bayan da Dan Mutum ya tashi daga mattatu. 10Sai suka bar zancen a tsakaninsu, amma suka tamabayi junansu “mene ne tashin matattu” ke nufi. 11Suka tambaye shi yaya malaman attaura suka ce Iliya zai fara zuwa?” 12Ya ce masu, laile ne Iliya ya fara zuwa ya raya dukan abubuwan. Don me a ka rubuta cewa Dan Mutum, zai sha wuya iri iri a kuma ki shi? 13Amma ina gaya muku Iliya ya riga, ya zo, amma sun yi masa abin da suke so su yi kamar yadda littatafai suka yi magana a kansa.” 14Sa'adda suka dawo wurin sauran almajiran, suka ga taron jama'a masu yawa suna ta muhawara tare da manyan malaman attaura. 15Da ganin sa, sai dukan taron yayi mamaki kwarai da gaske, suka dungumo wurinsa a guje, suna gaishe shi. 16Ya tambayi almajiransa, “ Wacce muhawara ce kuke yi da su?” 17Daya daga cikin taron ya amsa masa”malam, ga shi na kawo maka dana don yana da beben aljani. 18Duk lokacin da ya tasar masa yakan buga shi har kasa, na kuma yi wa almajiranka magana su fitar sun kasa. 19Ya amsa masu ya ce ya ku mutanen zamaninnan marasa bangaskiya, har yaushe zan kasance tare da ku ina jimrewa? ku dai kawo mini shi. 20Sai suka kawo masa yaron. Da ruhun ya ga Yesu, nan da nan ya buge yaron jikinsa na rawa. Sai yaron ya fadi yana ta birgima, bakinsa yana kumfa. 21Yesu ya tambayi mahaifin yaron, Tun yaushe wannan abu ya same shi? Mahaifin yaron ya ce tun yana karami. 22Ya kuwa sha jefa shi a ruwa da wuta, don ya halakar da shi. Idan zaka iya yin wani abu, ka ji tausayinmu ka taimakemu. 23Yesu ya ce masa, “In zan iya? Ai dukan abu mai yiwuwa ne, ga duk wanda ya gaskata. 24Nan da nan mahaifin yaron ya daga murya ya ce, Na ba da gaskiya. A kore mini rashin bangaskiyata. 25Da Yesu ya ga taron na dungumowa a guje, sai ya tsawata wa bakin aljanin ya ce masa, “kai, beben aljani na umarce ka, ka fita daga wannan yaron kar ka sake shigar sa. 26Sai wannan aljanin ya daga murya ya fita ya rabu da wannan yaron. Sai yaro ya zama kamar mattacce, sai sauran mutanen suka ce, “Ai, yaron ya mutu. 27Yesu ya kama hannunsa, ya daga shi, sai yaron ya mike tsaye. 28Da Yesu ya shiga gida, sai almajiransa suka tambaye shi a kadaice, me ya sa muka kasa fitar da shi?” 29Ya ce masu, “Ai, irin wannan ba ya fita sai da addu'a.” 30Sai suka ratsa cikin Galili, amma ba ya son kowa ya san inda suke. 31Da yake koyar da almajiransa, ya ce masu lokaci na zuwa da za'a ba da Dan mutum a hannun mutane, za su kuwa kashe shi, sa'adda aka kashe shi kuma, bayan kwana uku zai tashi. 32Amma fa ba su fahimci maganar ba, suna kuma jin tsoron tambayarsa. 33Sai suka zo kafarnahum. A lokacin da ya ke cikin gida, ya tambayi Al'majiransa, Menene ku ke magana a kansa a hanya? 34Amma suka yi shiru. don suna gardama da junansu akan hanya, a kan wane ne mafi girma. 35Sai ya zauna, ya kira al'majiransa goma sha biyu, yace masu duk wanda ya ke so ya zama na fari, dole ya kankantar da kansa, sa'annan ya bautawa sauran duka. 36Sai ya dauko karamin yaro a hannunsa ya sa shi a tsakiyarsu. Ya rumgome shi a kafadarsa ya ce masu. 37Dukan wanda ya karbi dan karamin yaron nan a cikin sunana ni ya karba, kuma dukan wanda ya karbi wani, ni ya karba, bai kuma karbeni ni kadai ba, duk da wanda ya aiko ni.” 38Sai Yahaya ya ce masa, Malam mun ga wani yana fitar da aljanu da sunanka mun yi kokari mu hana shi domin ba ya tare da mu. 39Sai Yesu ya ce masu ku kyale shi domin babu wanda zai yi irin wannan babban aikin, sa'annan ya fadi wasu maganganu mara sa kyau a kanmu. 40Duk wanda ba ya gaba da mu, na mu ne. 41Duk wanda ya ba ku ruwa ku sha domin kuna na Almasihu, gaskiya nake fada maku ba za ya rasa ladansa ba. 42Amma duk wanda ya sa kananan nan tuntube, ya fi kyau a rataya masa dutsen nika a jefa shi a cikin teku. 43Idan har hannun ka zai sa ka yi tuntube, zai fi kyau ka yanke shi. Domin zai fi kyau ka shiga aljanna da hannu daya da ka shiga jahannama da hannu biyu. 44(Inda tsutsotsi basu mutuwa, wutar kuma bata mutuwa). 45Idan kafarka za ta sa ka yi tuntube, ka yanke ta ka yar. Zai fi kyau ka shiga aljanna da kafa daya da ka shiga jahannama da kafa biyu. 46(Inda tsutsotsi basu mutuwa, wutar kuma bata mutuwa). 47Idan idonka zai sa ka yi tuntube, ka kwakule shi ka yar, domin gwamma ka shiga mulkin Allah da ido daya, da a jefa ka cikin wuta da idanu biyu. 48Inda tsutsotsi basu mutuwa, wutar kuma bata mutuwa. 49Domin da wuta za a tsarkake kowa. 50Gishiri yana da kyau, amma idan ya rasa zakinsa, ta ya ya za ka sa shi yayi zaki kuma? Ku kasance da zaki, kuma ku yi zaman lafiya da kowa.
Did you know?
The Transfiguration and Teaching on the Way
- After six days, Jesus took Peter, James, and John up a high mountain by themselves, and he was transfigured before them. Peter, originally called Simon, was a fisherman from Bethsaida on the Sea of Galilee. James, the elder brother of John and a son of Zebedee, was also a fisherman and was present with Peter and John at the transfiguration.Sources: the Bible text itself · Simon Peter · James (Son of Zebedee)
- On the high mountain, Elijah, the Tishbite and the Elias of the New Testament, appeared with Moses, talking with Jesus. As they came down, the disciples asked why the scribes say that Elijah must come first. Jesus replied that Elijah does indeed come first and that he has already come.Sources: the Bible text itself · Elijah
- Jesus and the disciples passed through Galilee, but he did not want anyone to know, because he was teaching them, and they came to Capernaum. Capernaum, Nahum’s town, was a Galilean city that became Jesus’ own city after his expulsion from Nazareth. The Jews called an upland plain among the mountains of Naphtali Galil, and the region came to be called Galilee of the Gentiles.Sources: the Bible text itself · Capernaum · Galilee
Notes written with AI assistance from open sources (Theographic Bible Metadata, CC BY-SA 4.0; Easton’s Bible Dictionary, public domain) and reviewed before publishing.
Places in this chapter
- Galilee · 32.760, 35.527 · verse 30
Only places identified with high confidence are shown (90% or more according to the scholarly sources compiled by OpenBible). Period map: DARE (Digital Atlas of the Roman Empire), CC BY 4.0; modern map: © OpenStreetMap contributors; places: OpenBible.info (CC BY 4.0).
Credits and license for this translation
Litafi Mai-tsarki The New Testament in the Hausa language of Nigeria copyright © 2020 Door43 World Missions Community Language: Hausa Translation by: Alakirawa, Bayan, Chrispher Ishaya, Dabere, Dacuhus Timothy Danjuma, Danjay, Danjuma Alfred H, Euang Hediza Naohammed, Franklyn Ukazu Udochukwu, Gideon, Gokop, Habibu, James, Kiash Dachung Butus, Lazarus, Nadaki M. Philip, Nenching, Paul, Rebecca, Rev. Ayuba Taiba, Rev. Cain Yusuf Daniel, Rev. Dalhatu Dambo Ayuba, Rev. Dr. Tambanya Yahaya, Rev. Dr. Yakubu Hassan, Rev. Hannatu Samuel Ndberhukwu, Rev. Ibrahim Kassim, Rev. M. Dan'Amarya, Rev. Yakuba Ayuba Contributor: Dacuhus Timothy Danjuma, Euang Hediza Naohammed, Kiash Dachung Butus, Nadaki M. Philip, Rev. Ayuba Taiba, Rev. Cain Yusuf Daniel, Rev. Dalhatu Dambo Ayuba, Rev. Dr. Tambanya Yahaya, Rev. Dr. Yakubu Hassan, Rev. Hannatu Samuel Ndberhukwu, Rev. Ibrahim Kassim, Rev. M. Dan'Amarya, Rev. Yakuba Ayuba This translation is made available to you under the terms of the Creative Commons Attribution Share-Alike license 4.0. You have permission to share and redistribute this Bible translation in any format and to make reasonable revisions and adaptations of this translation, provided that: You include the above copyright and source information. If you make any changes to the text, you must indicate that you did so in a way that makes it clear that the original licensor is not necessarily endorsing your changes. If you redistribute this text, you must distribute your contributions under the same license as the original. Pictures included with Scriptures and other documents on this site are licensed just for use with those Scriptures and documents. For other uses, please contact the respective copyright owners. Note that in addition to the rules above, revising and adapting God's Word involves a great responsibility to be true to God's Word. See Revelation 22:18-19. 2020-06-19
Source: http://ebible.org/hauulb/ · eBible.org