Nations Bible

Matthew 21

Litafi Mai-tsarki · Tap a verse to see its cross-references.

1Yayinda Yesu da almajiransa suka kusato Urushalima sai suka zo Betafaji wajen dutsen zaitun, sai Yesu ya aiki almajiransa guda biyu, 2yace masu, “Ku shiga kauyen da yake gaban ku zaku iske wata jaka da aholaki tara da ita. Ku kwance su ku kawo mani su. 3Idan wani ya gaya maku wani abu game da haka, sai ku ce, 'Ubangiji ne yake bukatarsu,' mutumin kuwa zai aiko ku da su nan da nan.” 4Anyi wannan kuwa domin a cika annabcin anabin. Yace, 5“Ku cewa diyar Sihiyona, duba, ga sarkinki na zuwa wurin ki, mai tawali'u ne, kuma akan jaki wanda aholaki ne.” 6Sai almajiran suka tafi suka yi kamar yadda Yesu ya umarce su. 7Suka kawo jakar da dan aholakin, suka sa tufafinsu akai, Yesu kuwa ya zauna akan tufafin. 8Yawancin jama'a kuwa suka baza tufafinsu akan hanya, wasu kuma suka yanko ganye daga bishiyoyi suka shimfida su a hanya. 9Taron jama'a da suke gabansa da wadanda suke bayansa, suka ta da murya suna cewa, “Hossana ga dan Dauda! mai albarka ne shi wanda ke zuwa cikin sunan Ubangiji. Hossana ga Ubangiji!” 10Sa'adda Yesu ya shiga Urushalima sai doki ya cika birnin ana cewa, “Wanene wannan?” 11Sai jama'a suka amsa, “Wannan shine Yesu annabi, daga Nazaret ta Galili.” 12Sai Yesu ya shiga haikalin. Ya kori duk wadanda ke saye da sayarwa a cikin ikiilisiya. Ya birkice teburan masu canjin kudi da kujerun masu sayar da tantabaru. 13Ya ce masu, “A rubuce yake, 'Za a kira gidana gidan addu'a,' amma kun mayar dashi kogon 'yan fashi.” 14Sai makafi da guragu suka zo wurin sa a haikalin, ya warkar da su. 15Amma da manyan firistoci da malaman attaura suka ga abubuwan banmamaki da yayi, kuma sa'adda suka ji yara suna tada murya a cikin haikalin suna cewa, “Hossana ga dan Dauda,” sai suka ji haushi. 16Suka ce masa, kana jin abinda wadannan mutanen ke fadi?'' Yesu ya ce masu, “I! Amma ba ku taba karantawa ba, 'daga bakin jarirai da masu shan mama ka sa yabo'?” 17Sai Yesu ya bar su, ya fice daga birnin zuwa Betaniya ya kwana a wurin. 18Washegari da safe yayin da yake komawa birnin, sai yaji yunwa. 19Da ya ga bishiyar baure a bakin hanya, sai yaje wurin amma bai sami kome ba sai dai ganye. Sai ya ce mata, “Kada ki kara yin 'ya'ya har abada.” Sai nan take bishiyar bauren ta bushe. 20Da almajiran suka ga haka, sai suka yi mamaki suka ce, “Kaka bishiyar bauren ta bushe nan da nan?” 21Yesu ya amsa yace masu, “Hakika ina ce maku, in dai kuna da bangaskiya ba ku yi shakka ba, ba abinda aka yi wa bauren nan kadai za kuyi ba har ma za ku cewa tsaunin nan, “Ka ciru ka fada teku,' sai kuwa haka ta kasance. 22Kome kuka roka cikin addu'a, in dai kun gaskanta, za ku samu.” 23Sa'adda Yesu ya shiga haikalin, sai manyan fristocin da shugabannin jama'a suka zo suka same shi yayin da yake koyarwa, suka ce, “Da wane iko kake yin wadannan abubuwa?” 24Yesu ya amsa yace masu, “Ni ma zan yi maku tambaya daya. In kun fada mani, ni ma zan fada maku ko da wane iko nake yin wadannan abubuwa. 25Daga ina baftismar Yahaya ta fito, daga sama ko kuma daga mutune?” Sai suka yi shawara a tsakanin su, suka ce, “In munce, 'daga sama,' zai ce mana, 'don me bamu gaskanta dashi ba?' 26Amma in munce, ' daga mutune,' muna tsoron jama'a, saboda sun san Yahaya annabi ne.” 27Sai suka amsa ma Yesu suka ce, ''Bamu sani ba.” Shi ma yace masu, “Nima bazan gaya maku ko da wane iko nake yin abubuwan nan ba. 28Amma me kuke tunani? Wani mutum yana da 'ya'ya biyu. Ya je wurin na farkon yace, 'Da, je ka kayi aiki yau a cikin gona.' 29Yaron ya amsa yace, 'bazan yi ba,' amma daga baya ya canza tunaninsa ya tafi. 30Sai mutumin ya je wurin da na biyun ya fada masa abu guda. Wannan dan ya amsa ya ce, 'zanje, baba,' amma bai je ba. 31Wanene a cikin 'ya'ya biyun nan yayi nufin ubansa?” Suka ce, “na farkon.” Yesu ya ce masu, “Hakika ina gaya maku, masu karbar haraji da karuwai za su shiga mulkin Allah kafin ku. 32Gama Yahaya ya zo maku a hanyar adalci, amma ba ku gaskata da shi ba, a yayinda masu karbar haraji da karuwai suka gaskata da shi. Ku kuwa, bayan kun ga abin da ya faru, baku ma tuba daga baya ba don ku gaskata da shi. 33Ku saurari wani misalin. Anyi wani mutum, mai gona. Yayi shuka a gonar, ya shinge ta, ya gina ramin matse inabi a cikin gonar, ya kuma gina wata hasumiyar tsaro, sai ya bada hayar gonar ga wadansu manoma. Sai ya tafi wata kasa. 34Da kakar inabi ta yi, sai ya aiki wadansu bayi su karbo masa amfanin gonar. 35Amma manoman suka kama bayin, suka doddoki dayan, suka kashe dayan, suka jejjefe dayan da duwatsu. 36Sai mai gonar ya sake aika wadansu bayinsa da suka fi na farko, amma manoman suka yi masu kamar yadda suka yi wa sauran. 37Bayan wannnan, sai mai gonar ya aika da dansa wurin su yana cewa, 'za su yi wa dana biyayya.' 38Amma da manoman suka ga dan, sai suka ce a tsakanin su, 'wannan shine magajin. Kuzo, mu kashe shi mu gaji gonar.' 39Sai suka dauke shi, suka jefar da shi daga cikin gonar, suka kashe shi. 40To idan me gonar ya zo, me zai yiwa manoman? 41Suka ce masa, “Zai hallaka mugayen manoman nan ta hanya mai tsanani, zai kuma bada gonar haya ga wadansu manoman, mutanen da za su biya, lokacin da inabin ya nuna.” 42Yesu yace masu, “Baku taba karantawa a nassi ba,'' 'Dutsen da magina suka ki ya zama dutse mafi amfani. Wannan daga Ubangijine, kuma abin mamaki ne a idanunmu?' 43Saboda haka ina gaya maku, za a karbe mulkin Allah daga wurin ku a ba wata al'umma da zata bada amfaninsa. 44Duk wanda ya fadi akan dutsen nan zai ragargaje. Amma duk wanda dutsen ya fadawa, zai nike.” 45Da manyan firistocin da farisawan suka ji wannan misalin, sai suka gane da su yake. 46Da suka nemi kama shi, sai suka ji tsoron taron, saboda mutanen sun dauke shi annabi.

Artistic illustration — an interpretation, not a historical record.

Did you know?

Jesus Enters Jerusalem

  • As they approached Jerusalem, Jesus and the disciples came to Bethphage on the Mount of Olives, and from there he sent two disciples to bring a donkey and her colt. Bethphage means “house of the unripe fig”; it lay on the road from Jerusalem to Jericho, very close to Bethany, where he spent the night, and it was the limit of a Sabbath-day’s journey from the city, 2,000 cubits. The Mount of Olives is named for the olive trees clothing its slopes and is a ridge east of Jerusalem, separated from the city by the Kidron valley.Sources: the Bible text itself · Bethphage · Mount of Olives
  • The passage says the entry fulfilled what was spoken through the prophet to the Daughter of Zion: her king would come to her gentle, riding on a donkey, on a colt, the foal of a donkey. Zion was the south-eastern hill of Jerusalem; when David took it from the Jebusites he built a citadel and a palace there, and it became known as the city of David. The crowds going ahead and those following shouted, “Hosanna to the Son of David.”Sources: the Bible text itself · Zion
  • When Jesus entered Jerusalem, the whole city was stirred and asked who he was; the crowds answered that this was Jesus, the prophet from Nazareth in Galilee. Nazareth is not mentioned in the Old Testament and was the home of Joseph and Mary. Easton's Bible Dictionary (1897) says the name is generally taken as a Greek form of a Hebrew word for a “shoot” or “sprout,” though some connect it with the hill behind the town and a word for one who guards or watches; Galilee means “circuit” and was called “Galilee of the Gentiles,” with Upper Galilee distinguished from Lower Galilee farther south.Sources: the Bible text itself · Nazareth · Galilee

Notes written with AI assistance from open sources (Theographic Bible Metadata, CC BY-SA 4.0; Easton’s Bible Dictionary, public domain) and reviewed before publishing.

Places in this chapter

  • Jerusalem · 31.777, 35.234 · verses 1, 10, 18
  • Mount of Olives · 31.778, 35.246 · verse 1
  • Zion · Today: Jerusalem · 31.777, 35.234 · verse 5
  • Galilee · 32.760, 35.527 · verse 11
  • Nazareth · 32.702, 35.298 · verse 11

Only places identified with high confidence are shown (90% or more according to the scholarly sources compiled by OpenBible). Period map: DARE (Digital Atlas of the Roman Empire), CC BY 4.0; modern map: © OpenStreetMap contributors; places: OpenBible.info (CC BY 4.0).

Credits and license for this translation
Litafi Mai-tsarki
The New Testament in the Hausa language of Nigeria
copyright © 2020 Door43 World Missions Community
Language: Hausa
Translation by: Alakirawa, Bayan, Chrispher Ishaya, Dabere, Dacuhus Timothy Danjuma, Danjay, Danjuma Alfred H, Euang Hediza Naohammed, Franklyn Ukazu Udochukwu, Gideon, Gokop, Habibu, James, Kiash Dachung Butus, Lazarus, Nadaki M. Philip, Nenching, Paul, Rebecca, Rev. Ayuba Taiba, Rev. Cain Yusuf Daniel, Rev. Dalhatu Dambo Ayuba, Rev. Dr. Tambanya Yahaya, Rev. Dr. Yakubu Hassan, Rev. Hannatu Samuel Ndberhukwu, Rev. Ibrahim Kassim, Rev. M. Dan'Amarya, Rev. Yakuba Ayuba
Contributor: Dacuhus Timothy Danjuma, Euang Hediza Naohammed, Kiash Dachung Butus, Nadaki M. Philip, Rev. Ayuba Taiba, Rev. Cain Yusuf Daniel, Rev. Dalhatu Dambo Ayuba, Rev. Dr. Tambanya Yahaya, Rev. Dr. Yakubu Hassan, Rev. Hannatu Samuel Ndberhukwu, Rev. Ibrahim Kassim, Rev. M. Dan'Amarya, Rev. Yakuba Ayuba
This translation is made available to you under the terms of the
Creative Commons Attribution Share-Alike license 4.0.
You have permission to share and redistribute this Bible translation in any format and to make reasonable revisions and adaptations of this translation, provided that:
You include the above copyright and source information.
If you make any changes to the text, you must indicate that you did so in a way that makes it clear that the original licensor is not necessarily endorsing your changes.
If you redistribute this text, you must distribute your contributions under the same license as the original.
Pictures included with Scriptures and other documents on this site are licensed just for use with those Scriptures and documents.
For other uses, please contact the respective copyright owners.
Note that in addition to the rules above, revising and adapting God's Word involves a great responsibility to be true to God's Word. See Revelation 22:18-19.
2020-06-19

Source: http://ebible.org/hauulb/ · eBible.org

Talk to us

Tell us where you read from, how the Bible has helped you, or what we could improve. We read every message.