Nations Bible

Luke 21

Litafi Mai-tsarki · Tap a verse to see its cross-references.

1Yesu ya tada ido sai ya ga mutane masu arziki wadanda suke saka baikonsu a cikin ma'aji. 2Ya ga wata gwauruwa matalauciya tana saka anini biyu a ciki. 3Sai ya ce, “Gaskiya ina gaya maku, wannan matalauciyar gwauruwa ta saka fiye da dukansu. 4Duka wadannan sun bayar da baikonsu daga cikin yalwarsu. Amma wannan gwauruwan, daga cikin talaucin ta, ta saka dukan iyakar kudinta na zaman gari da take da shi.” 5Kamar yadda wadansu suke maganan haikali, yadda aka yi masa ado da duwatsu masu daraja da bayebaye, ya ce, 6“Game da wadannan abubuwa da ku ke gani, rana tana zuwa da ba dutse ko daya da zai zauna kan dan'uwansa da ba za a rushe kasa ba.” 7Sai suka yi masa tambaya, cewa, “Malam, yaushe ne wadannan abubuwan zasu faru? Menene kuma zai zama alama sa'adda wadannan abubuwa suna shirin faruwa?” 8Yesu ya amsa, “Ku yi hankali kada a rude ku. Gama dayawa zasu zo a cikin sunana, suna cewa, 'Ni ne shi,' kuma, 'Lokaci ya yi kusa.' Kada ku bi su. 9Sa'adda ku ka ji game da yakoki da hargitsi, kada ku firgita, dole ne wadannan abubuwa su faru tukuna, amma karshe ba zai faru nan da nan ba.” 10Sa'annan ya ce masu, “Al'umma za ta tasar ma al'umma, mulki kuma za ya tasar wa mulki. 11Za a yi babbar girgizan kasa, a wurare dabam dabam kuma za a yi yunwa da annoba. Za a yi al'amura masu ban tsoro da manyan alamu daga sama. 12Amma kafin abubuwan nan duka, za su kama ku, su kuma tsananta maku, suna mika ku ga majami'u da kuma gidajen kurkuku, za su kawo ku gaban sarakuna da gwamnoni saboda sunana. 13Zai zamar maku zarafin shaida. 14Saboda haka ku kudurta a ranku kada ku shirya yadda za ku amsa, 15gama ni zan ba ku kalmomi da hikima, wadda dukan makiyanku ba za su yi tsayayya ko su karyata ku ba. 16Amma har da mahaifa da 'yan'uwa da dangi da abokai za su bashe ku, su kuma kashe wadansun ku. 17Kowa zai ki ku saboda sunana. 18Amma ba ko gashin kanku da zai hallaka. 19A cikin hankurin ku za ku ribato rayukanku. 20Sa'adda ku ka ga Urushalima tana kewaye da sojoji, sai ku sani da cewa faduwarta ta yi kusa. 21Sai wadanda su ke Yahudiya su gudu zuwa kan tuddai, wadanda suke tsakiyar gari kuma su tafi, kada su bar wadanda suke kauyuka su shigo ciki. 22Gama wadannan ranakun ramako ne, saboda duka abubuwan da aka rubuta su cika. 23Kaiton wadanda suke da juna biyu da masu ba da mama a wannan kwanakin! Gama za a sha kunci mai girma a kasan, da fushi kuma zuwa ga mutanen nan. 24Za su fadi ta kaifin takobi kuma za a kai su cikin bauta ga dukan kasashe, al'ummai za su tattake Urushalima, har ya zuwa lokacin al'ummai ya cika. 25Za a ga alamomi cikin rana da wata da kuma taurari. A duniya kuma, al'ummai za su sha kunci, za su rude saboda rurin teku da rakuman ruwa. 26Mutane za su suma da tsoro da kuma da tunanin abubuwa da za su abko wa duniya. Gama za a girgiza ikokin sammai. 27Sa'annan za su ga Dan Mutum yana zuwa a cikin gajimarai da iko da daukaka mai girma. 28Amma sa'adda wadannan abubuwa suka fara faruwa, tashi saye, sai ku daga kanku sama, saboda ceton ku ya kusato.” 29Yesu ya bada misali, “Duba itacen baure, da duka itatuwa. 30Sa'adda su ke fitar da ganye, za ku gani da kanku cewa bazara ta yi kusa kuma. 31Haka kuma, sa'adda ku ka ga wadannan abubuwa suna faruwa, ku sani cewa mulkin Allah ya yi kusa. 32Gaskiya, na ke gaya maku, wannan zamani ba za ya shude ba, sai duka abubuwan nan sun faru. 33Sama da kasa za su shude, amma maganata ba za ta shude ba. 34Amma ku lura da kanku, domin kada ku nawaita zuciyarku da tararradin duniya da shayeshaye da damuwa ta rayuwa. Gama ranar za ta zo babu shiri 35kamar tarko. Gama zai zo akan kowa da ke rayuwa a fuskar dukan duniya. 36Amma ku zama a fadake kowanne lokaci, kuna addu'a domin ku iya samun karfin tserewa dukan wadannan abubuwa da za su faru, da kuma yadda za ku tsaya a gaban Dan Mutum.” 37Da rana yana koyarwa a cikin haikali, dukan dare kuma yakan tafi dutsen da a ke kira zaitun. 38Dukan mutane suka rika zuwa wurinsa da sassafe domin su ji shi a haikali.

Artistic illustration — an interpretation, not a historical record.

Did you know?

Jerusalem, the temple, and the days ahead

  • A geographical note says that the name Jerusalem is dual in the original and means “possession of peace” or “foundation of peace.” It adds that this form probably refers to the two mountains on which the city was built, Zion and Moriah, or, as some suppose, to the upper and lower city, and it calls Jerusalem a mountain city enthroned on a mountain stronghold. In this chapter Jesus says that city will be surrounded by armies, left desolate, and trodden down by the Gentiles.Sources: Jerusalem · the Bible text itself
  • Jesus tells those who are in Judea to flee to the mountains when they see Jerusalem surrounded by armies. A geographical note explains that, under the Romans in the time of Christ, Judea meant the southernmost of the three divisions of Palestine, distinguished from Galilee and Samaria, though the name was sometimes used for Palestine in general. As a province it included the territories of the tribes of Judah, Benjamin, Dan, Simeon, and part of Ephraim, and it formed part of Syria.Sources: Judea · the Bible text itself
  • The chapter opens not with armies but with a poor widow who puts two small copper coins into the temple treasury. Jesus says she has given more than the rich, who contributed from their surplus, because she put in all she had to live on. The disciples then remark on the beautiful stones and consecrated gifts of the temple, and he answers that not one stone will be left on another.Sources: the Bible text itself

Notes written with AI assistance from open sources (Theographic Bible Metadata, CC BY-SA 4.0; Easton’s Bible Dictionary, public domain) and reviewed before publishing.

Places in this chapter

  • Jerusalem · 31.777, 35.234 · verses 20, 21, 24
  • Judea · Today: Judea 1 · 31.777, 35.234 · verse 21
  • Mount of Olives · 31.778, 35.246 · verse 37

Only places identified with high confidence are shown (90% or more according to the scholarly sources compiled by OpenBible). Period map: DARE (Digital Atlas of the Roman Empire), CC BY 4.0; modern map: © OpenStreetMap contributors; places: OpenBible.info (CC BY 4.0).

Credits and license for this translation
Litafi Mai-tsarki
The New Testament in the Hausa language of Nigeria
copyright © 2020 Door43 World Missions Community
Language: Hausa
Translation by: Alakirawa, Bayan, Chrispher Ishaya, Dabere, Dacuhus Timothy Danjuma, Danjay, Danjuma Alfred H, Euang Hediza Naohammed, Franklyn Ukazu Udochukwu, Gideon, Gokop, Habibu, James, Kiash Dachung Butus, Lazarus, Nadaki M. Philip, Nenching, Paul, Rebecca, Rev. Ayuba Taiba, Rev. Cain Yusuf Daniel, Rev. Dalhatu Dambo Ayuba, Rev. Dr. Tambanya Yahaya, Rev. Dr. Yakubu Hassan, Rev. Hannatu Samuel Ndberhukwu, Rev. Ibrahim Kassim, Rev. M. Dan'Amarya, Rev. Yakuba Ayuba
Contributor: Dacuhus Timothy Danjuma, Euang Hediza Naohammed, Kiash Dachung Butus, Nadaki M. Philip, Rev. Ayuba Taiba, Rev. Cain Yusuf Daniel, Rev. Dalhatu Dambo Ayuba, Rev. Dr. Tambanya Yahaya, Rev. Dr. Yakubu Hassan, Rev. Hannatu Samuel Ndberhukwu, Rev. Ibrahim Kassim, Rev. M. Dan'Amarya, Rev. Yakuba Ayuba
This translation is made available to you under the terms of the
Creative Commons Attribution Share-Alike license 4.0.
You have permission to share and redistribute this Bible translation in any format and to make reasonable revisions and adaptations of this translation, provided that:
You include the above copyright and source information.
If you make any changes to the text, you must indicate that you did so in a way that makes it clear that the original licensor is not necessarily endorsing your changes.
If you redistribute this text, you must distribute your contributions under the same license as the original.
Pictures included with Scriptures and other documents on this site are licensed just for use with those Scriptures and documents.
For other uses, please contact the respective copyright owners.
Note that in addition to the rules above, revising and adapting God's Word involves a great responsibility to be true to God's Word. See Revelation 22:18-19.
2020-06-19

Source: http://ebible.org/hauulb/ · eBible.org

Talk to us

Tell us where you read from, how the Bible has helped you, or what we could improve. We read every message.