Luke 13
Litafi Mai-tsarki · Tap a verse to see its cross-references.
1A lokacin, wadansu mutane suka gaya masa game da galilawa wadanda Bilatus ya gauraye jininsu da hadayunsu. 2Sai Yesu ya amsa masu yace “Kuna tsammani wadannan Galilawa sun fi duk sauran Galilawan zunubi ne, da suka sha azaba haka? 3A'a, ina gaya maku. In ba ku tuba ba, dukanku za ku halaka kamarsu. 4Ko kuwa mutane goma sha takwas din nan da suna Siluwam wadanda hasumiya ta fado a kansu ta kashe su, kuna tsamani sun fi duk sauran mutanen Urushalima laifi ne? 5Ina gaya maku ba haka bane. Amma duk wanda ya ki tuba, dukanku za su hallaka” 6Yesu ya fada wannan misali, “Wani mutum yana da baure wanda ya shuka a garkar inabinsa sai ya zo neman 'ya'yan itacen amma bai samu ba. 7Sai mutumin ya ce wa mai kula da garkar, “ka ga, shekara uku kenan nake zuwa neman 'ya'yan wannan baure, amma ban samu ba. A sare shi. Yaya za a bar shi ya tsare wurin a banza? 8Sai mai lura da garkar ya amsa yace, 'Ka dan ba shi lokaci kadan in yi masa kaftu in zuba masa taki. 9In yayi 'ya'ya shekara mai zuwa to, amma in bai yi 'ya'ya ba sai a sare shi!”' 10Wata rana Yesu yana koyarwa a wata majami' a ran Asabaci. 11Sai, ga wata mace a wurin shekarunta goma sha takwas tana da mugun ruhu, duk ta tankware, ba ta iya mikewa. 12Da Yesu ya gan ta, sai ya kira ta ya ce mata, an warkar da ke daga wannan cuta.” 13Sai Yesu ya dora hannunsa a kanta, nan da nan sai ta mike a tsaye ta fara daukaka Allah. 14Amma shugaban majami'a yayi fushi domin Yesu yayi warkarwa a ranar Asabaci. Sai shugaban ya amsa yace wa jama'a, “Akwai ranaku shida da ya kamata a yi aiki. Ku zo domin a warkar da ku amma ba ranar Asabaci ba.” 15Amma Ubangiji ya amsa masa ya ce, “Munafukai! Ashe kowannenku ba ya kwance Jakinsa ko Sa daga turkensa ya kai shi banruwa ran Asabaci? 16Ashe wannan 'yar gidan Ibrahim, wanda shaidan ya daure ta shekara goma sha takwas, wato ba za a iya kwance ta a ranar Asabaci kenan ba? 17Da ya fada wadannan abubuwa, dukansu da suka yi adawa da shi suka kunyata, duk taron kuwa suka yi ta farin ciki da abubuwa masu daraja da yayi. 18Sai Yesu ya ce, “Yaya za a misalta mulkin Allah, kuma da me zan kwatanta shi? 19Yananan kamar kwayar mastad, wanda wani mutum ya dauka ya jefa ta a lambunsa, ta kuma yi girma ta zama gagarumin itace, har tsuntsaye suka yi shekarsu a rassanta.” 20Ya sake cewa, “Da me zan kwatanta mulkin Allah? 21Yana kamar yisti wanda wata mace ta dauka ta cuda da mudu uku na garin alkama don ya kumburar da shi.” 22Yesu ya ziyarci kowanne birni da kauye, a hanyar sa ta zuwa Urushalima yana koyar da su. 23Sai wani ya ce masa, “Ubangiji, wadanda za su sami ceto kadan ne?” Sai ya ce masu, 24“Ku yi kokari ku shiga ta matsatsiyar kofa, domin na ce maku, mutane dayawa za su nemi shiga amma ba za su iya shiga ba. 25In dai maigida ya riga ya tashi ya rufe kofa, sannan za ku tsaya a waje kuna kwankwasa kofar kuna cewa, 'Ubangiji, Ubangiji, bari mu shiga ciki'. Sai ya amsa yace maku, 'Ni ban san ku ba ko daga ina ku ka fito.' 26Sannan za ku ce, 'Mun ci mun sha a gabanka, ka kuma yi koyarwa a kan titunanmu.' 27Amma zai amsa ya ce, “Ina gaya maku, ban san ko daga ina ku ka fito ba, ku tafi daga wurina, dukanku masu aikata mugunta!' 28Za a yi kuka da cizon hakora a lokacin da kun ga Ibrahim, da Ishaku, da Yakubu da dukan annabawa a mulkin Allah amma ku-za a jefar da ku waje. 29Za su zo daga gabas, yamma, kudu, da arewa, za su ci a teburin abinci a mulkin Allah. 30Ku san da wannan, na karshe za su zama na farko, na farko kuma za su zama na karshe.” 31Nan take, wadansu farisiyawa suka zo suka ce masa, “Ka tafi daga nan domin Hirudus yana so ya kashe ka.” 32Yesu ya ce, “Ku tafi ku gaya wa dilan nan cewa, 'Duba, na fitar da aljanu, ina warkarwa yau da gobe, kuma a rana ta uku kuwa zan gama aiki na.' 33Ko da kaka, dole ne in ci gaba da tafiyata yau, da gobe, da kuma jibi, don bai dace a kashe annabi nesa da Urushalima ba. 34Urushalima, Urushalima masu kisan annabawa, masu jifan wadanda aka aiko gare ku. Sau nawa ne ina so in tattara 'ya'yanki kamar yadda kaza take tattara 'ya'yanta a cikin fukafukanta, amma ba ki so wannan ba. 35Duba, an yashe gidanki. Ina kwa gaya maku ba za ku kara ganina ba sai ran da kuka ce, 'Albarka ta tabbata ga mai zuwa da sunan Ubangiji.'”

Did you know?
Repentance on the Way to Jerusalem
- Pontius Pilate was the sixth Roman procurator of Judea, from A.D. 26 to 36. His headquarters were at Caesarea, though he often went up to Jerusalem. Luke 13 opens with the report that he had mixed the blood of some Galileans with their sacrifices; Jesus replies that this does not show they were worse sinners than the other Galileans, and that unless his hearers repent they too will all perish.Sources: Pontius Pilate · the Bible text itself
- Jesus also asks whether the eighteen who were killed when the tower of Siloam collapsed were more sinful than all the others living in Jerusalem, and again says that unless his hearers repent they too will all perish. Siloam, meaning “sent” or “sending,” has been identified with the Birket Silwan in the lower Tyropoeon valley, southeast of the hill of Zion. Water reaches that pool intermittently through a winding underground channel from the Fountain of the Virgin, and John’s Gospel records that Jesus gave sight to a blind man there.Sources: Siloam · the Bible text itself
- While he travels through the towns and villages toward Jerusalem, Jesus laments the city that kills the prophets and stones those sent to her. It is described as a mountain city set on a stronghold; its name, in the dual form, means “possession of peace” or “foundation of peace,” probably referring to Zion and Moriah, the two mountains on which it was built, or, as some suppose, to the upper and lower city. He says he has often longed to gather its children as a hen gathers her chicks under her wings, and Easton's Bible Dictionary (1897) notes that this familiar bird is mentioned only in this lament and in Matthew 23:37.Sources: the Bible text itself · Jerusalem · Josiah
Notes written with AI assistance from open sources (Theographic Bible Metadata, CC BY-SA 4.0; Easton’s Bible Dictionary, public domain) and reviewed before publishing.
Places in this chapter
- Galilee · 32.760, 35.527 · verses 1, 2
- Jerusalem · 31.777, 35.234 · verses 4, 22, 33, 34
- Siloam · Today: Pool of Siloam · 31.771, 35.235 · verse 4
Only places identified with high confidence are shown (90% or more according to the scholarly sources compiled by OpenBible). Period map: DARE (Digital Atlas of the Roman Empire), CC BY 4.0; modern map: © OpenStreetMap contributors; places: OpenBible.info (CC BY 4.0).
Credits and license for this translation
Litafi Mai-tsarki The New Testament in the Hausa language of Nigeria copyright © 2020 Door43 World Missions Community Language: Hausa Translation by: Alakirawa, Bayan, Chrispher Ishaya, Dabere, Dacuhus Timothy Danjuma, Danjay, Danjuma Alfred H, Euang Hediza Naohammed, Franklyn Ukazu Udochukwu, Gideon, Gokop, Habibu, James, Kiash Dachung Butus, Lazarus, Nadaki M. Philip, Nenching, Paul, Rebecca, Rev. Ayuba Taiba, Rev. Cain Yusuf Daniel, Rev. Dalhatu Dambo Ayuba, Rev. Dr. Tambanya Yahaya, Rev. Dr. Yakubu Hassan, Rev. Hannatu Samuel Ndberhukwu, Rev. Ibrahim Kassim, Rev. M. Dan'Amarya, Rev. Yakuba Ayuba Contributor: Dacuhus Timothy Danjuma, Euang Hediza Naohammed, Kiash Dachung Butus, Nadaki M. Philip, Rev. Ayuba Taiba, Rev. Cain Yusuf Daniel, Rev. Dalhatu Dambo Ayuba, Rev. Dr. Tambanya Yahaya, Rev. Dr. Yakubu Hassan, Rev. Hannatu Samuel Ndberhukwu, Rev. Ibrahim Kassim, Rev. M. Dan'Amarya, Rev. Yakuba Ayuba This translation is made available to you under the terms of the Creative Commons Attribution Share-Alike license 4.0. You have permission to share and redistribute this Bible translation in any format and to make reasonable revisions and adaptations of this translation, provided that: You include the above copyright and source information. If you make any changes to the text, you must indicate that you did so in a way that makes it clear that the original licensor is not necessarily endorsing your changes. If you redistribute this text, you must distribute your contributions under the same license as the original. Pictures included with Scriptures and other documents on this site are licensed just for use with those Scriptures and documents. For other uses, please contact the respective copyright owners. Note that in addition to the rules above, revising and adapting God's Word involves a great responsibility to be true to God's Word. See Revelation 22:18-19. 2020-06-19
Source: http://ebible.org/hauulb/ · eBible.org