Nations Bible

John 18

Litafi Mai-tsarki · Tap a verse to see its cross-references.

1Bayan Yesu ya fadi wadannan maganganu, ya fita shi da almajiransa zuwa daya barayin kwarin Kidiron, inda wani lambu ya ke, ya kuma shiga da almajiransa. 2Yahuza ma wanda zai bashe shi ya san wurin, domin Yesu ya saba zuwa wurin da almajiransa. 3Yahuza kuwa, bayan ya dauko kungiyar soja daga manyan firistoci, da Farisawa, da 'yan majalisa, suka zo wurin, rike da fitilu, da cociloli, da makamai. 4Sai Yesu, da ya san duk abinda ke faruwa da shi, yayiwo gaba, yace masu, ''Wa kuke nema'' 5Suka amsa masa su ka ce, ''Yesu Banazare'' Yesu yace masu, Ni ne'' Yahuza kuma, wanda ya bashe shi, yana tsaye tare da sojojin. 6Sa'adda ya ce masu, ''Ni ne'', suka koma da baya, suka fadi a kasa. 7Ya sake tambayarsu kuma, ''Wa ku ke nema?'' su ka ce, ''Yesu Banazare.'' 8Yesu ya amsa, ''Ai, na gaya maku cewa, Ni ne. In kuwa ni ku ke nema, ku bar wadannan su tafi abinsu;'' 9Wannan kuwa domin maganar daya fada ta cika, ''Daga cikin wadanda ka ba ni, ko daya bai bace mani ba.'' 10Saminu Bitrus kuwa, da ya ke yana da takobi, ya zaro ya kai wa bawan babban firist sara, ya dauke masa kunnensa na dama, sunan bawan Malkus ne. 11Yesu ya ce wa Bitrus, ''Mai da takobin ka kubenta. Ba zan sha kokon da Uba ya ba ni ba.'? 12Sai sojojin da hafsan, da 'yan majalisar Yahudawa, suka kama Yesu, suka daure shi. 13Da fari suka tafi da shi wurin Hanana, don shi surukin Kayafa ne, wanda ya ke shi ne babban firist a shekaran nan. 14Kayafa kuma shi ne ya ba Yahudawa shawara, cewa ya fiye masu mutum daya ya mutu domin mutane. 15Saminu bitrus ya bi bayan Yesu, haka kuma wani almajirin yayi. Almajirin nan kuwa sananne ne ga babban firist, sai ya shiga har farfajiyar babban firist din tara da Yesu; 16Amma bitrus kuwa ya tsaya a bakin kofa daga waje. Sai daya almajirin da ya ke sananne ga babban firist ya fita, yayi magana da macen da ta ke tsaron kofar, sa'an nan ya shigo da Bitrus. 17Sai yarinyar mai tsaron kofar ta ce wa Bitrus, ''kai ma ba kana cikin almajiran mutumin nan ba?'' Yace ''bani ba.'' 18To, barorin da dogaran Haikali suna tsaye a wurin, sun kuwa hura wutar gawayi, suna jin dumi, gama ana sanyi. Bitrus ma yana tsaye tare da su yana jin dumin. 19babban firist ya tambayi Yesu game da almajiransa da koyarwarsa kuma. 20Yesu ya amsa masa, Ai, na yi wa duniya magana a bayyane. Na kuma sha koyarwa a majami'u da Haikali in da Yahudawa duka sukan taru. Ban fadi komai a boye ba. 21Don me kake tambaya ta? Ka tambayi wadanda suka saurare ni a kan abinda na fada, ai, sun san abinda na fada. 22Sa'adda Yesu ya fadi wannan, wani daga cikin 'yan majalisar da ke tsaye a wurin ya nushi Yesu, yace, ''Kana amsa wa babban firist haka.'' 23Yesu ya amsa masa yace, ''Idan na fadi mugun abu to, ka bada shaida kan hakan. In kuwa dai dai na fada, to, dan me za ka nushe ni?'' 24Sai Hanana ya aika daYesu a daure wurin Kayafa, babban firist. 25To Saminu Bitrus yana tsaye yana jin dumin. Mutanen kuwa suka ce masa, ''Anya kai ma ba cikin almajiransa ka ke ba?'' Sai yayi musu yace, ''A'a, ba na ciki.'' 26Sai wani daga cikin bayin babban firist, wato dan'uwan wanda Bitrus ya fillewa kunne, yace, ''Ashe, ban gan ka tare da shi a lambun ba? 27Bitrus ya sake yin musu, nan da nan kuwa zakara yayi cara. 28Daga wurin Kayafa kuma suka kai Yesu fadar Gwamna. Da asuba ne kuwa, su kansu ba su shiga fadar Gwamnan ba, wai don kada su kazantu su kasa cin jibin Ketarewa. 29Sai bilatus fa ya fita zuwa wurinsu, yace, 'Wane zargi ku ke kawowa akan mutumin nan?' 30''Sai suka amsa suka ce, ''idan da mutumin nan bai yi mugun abu ba, me zai sa mu yi kararsa a wurin ka'' 31bilatus yace masu, ''Ku tafi da shi da kan ku mana, ku hukunta shi bisa ga shari'arku!'' Sai Yahudawa su kace masa, ''Ai, ba mu da ikon zartar da hukuncin kisa akan kowa.'' 32Sun fadi Wannan ne don a cika maganar da Yesu yayi, wadda ta kwatanta irin mutuwar da zai yi. 33Sai bilatus ya sake shiga cikin fadar Gwamnan, ya kira Yesu ya ce masa, ''kai sarkin Yahudawa ne?'' 34Yesu ya amsa, '' wannan fadarka ce, ko kuwa wadansu ne suka ce da ni haka a wurinka?'' 35Bilatus ya amsa “Ni ba Bayahude bane, ko kuwa?'' Ai, jama'arka ne da manyan firistoci suka bashe ka gareni. ''Me ka yi?'' 36Yesu ya amsa, ''Mulkina ba na duniya nan ba ne. Da mulkina na duniyan nan ne da barorina za su yi yaki kada a bashe ni ga Yahudawa. To, mulkina ba daga nan ya ke ba.'' 37Sai Bilatus yace masa, ''Wato ashe, sarki ne kai?'' Yesu ya amsa, ''Yadda ka fada, ni sarki ne. Domin wannan dalili aka haife ni, domin kuma wannan dalili na zo cikin duniya, don in bada shaida game da gaskiya. Kowane mai kaunar gaskiya kuma yakan saurari muryata.'' 38Bilatus yace masa, ''Menene gaskiya?'' Bayan da ya fadi haka, ya sake fitowa wurin Yahudawa, yace masu, ''Ni kam, ban sami mutumin nan da wani laifi ba. 39Amma dai kuna da wata al'ada, in Idin Ketarewa ya yi, na kan sakar maku mutum daya. To, kuna so in sakar maku sarkin Yahudawa?'' 40Sai suka sake daukar kururuwa suna cewa, ''A; a, ba wannan mutum ba, sai dai Barabbas.'' Barabbas din nan kuwa dan fashi ne.

Artistic illustration — an interpretation, not a historical record.

Did you know?

The Arrest and the Trials

  • Jesus went out with his disciples across the Kidron Valley and entered a garden that Judas, his betrayer, already knew, because Jesus had often met the disciples there. Easton's Bible Dictionary (1897) calls the Kidron “the black torrent,” the brook flowing through the ravine below Jerusalem’s eastern wall.Sources: the Bible text itself · Brook Kidron
  • The soldiers and officers brought Jesus first to Annas, father-in-law of Caiaphas, the high priest that year, and Annas then sent him, still bound, to Caiaphas. Easton's Bible Dictionary (1897) says Annas had been high priest from A.D. 7 to 14 and was deposed by the Roman procurator, yet, because Mosaic law held the office for life, the Jews may still have regarded him as legally high priest. The same dictionary identifies Caiaphas as a Sadducee who served throughout Pilate’s administration and who had advised that it would be better if one man died for the people.Sources: the Bible text itself · Annas · Caiaphas
  • Pontius Pilate, the sixth Roman procurator of Judea (A.D. 26–36), kept headquarters at Caesarea but often went up to Jerusalem; that early morning he came out of the Praetorium because the Jews would not enter and risk being defiled, unable to eat the Passover. He offered to release one prisoner at the Passover, calling it their custom, but they demanded Barabbas. This chapter calls Barabbas an insurrectionist, while Easton's Bible Dictionary (1897) calls him a notorious robber and explains the name as “son of Abba” or “son of a father.”Sources: the Bible text itself · Pontius Pilate · Barabbas

Notes written with AI assistance from open sources (Theographic Bible Metadata, CC BY-SA 4.0; Easton’s Bible Dictionary, public domain) and reviewed before publishing.

Places in this chapter

  • Kidron · Today: Kidron River · 31.780, 35.240 · verse 1
  • Nazareth · 32.702, 35.298 · verses 5, 7

Only places identified with high confidence are shown (90% or more according to the scholarly sources compiled by OpenBible). Period map: DARE (Digital Atlas of the Roman Empire), CC BY 4.0; modern map: © OpenStreetMap contributors; places: OpenBible.info (CC BY 4.0).

Credits and license for this translation
Litafi Mai-tsarki
The New Testament in the Hausa language of Nigeria
copyright © 2020 Door43 World Missions Community
Language: Hausa
Translation by: Alakirawa, Bayan, Chrispher Ishaya, Dabere, Dacuhus Timothy Danjuma, Danjay, Danjuma Alfred H, Euang Hediza Naohammed, Franklyn Ukazu Udochukwu, Gideon, Gokop, Habibu, James, Kiash Dachung Butus, Lazarus, Nadaki M. Philip, Nenching, Paul, Rebecca, Rev. Ayuba Taiba, Rev. Cain Yusuf Daniel, Rev. Dalhatu Dambo Ayuba, Rev. Dr. Tambanya Yahaya, Rev. Dr. Yakubu Hassan, Rev. Hannatu Samuel Ndberhukwu, Rev. Ibrahim Kassim, Rev. M. Dan'Amarya, Rev. Yakuba Ayuba
Contributor: Dacuhus Timothy Danjuma, Euang Hediza Naohammed, Kiash Dachung Butus, Nadaki M. Philip, Rev. Ayuba Taiba, Rev. Cain Yusuf Daniel, Rev. Dalhatu Dambo Ayuba, Rev. Dr. Tambanya Yahaya, Rev. Dr. Yakubu Hassan, Rev. Hannatu Samuel Ndberhukwu, Rev. Ibrahim Kassim, Rev. M. Dan'Amarya, Rev. Yakuba Ayuba
This translation is made available to you under the terms of the
Creative Commons Attribution Share-Alike license 4.0.
You have permission to share and redistribute this Bible translation in any format and to make reasonable revisions and adaptations of this translation, provided that:
You include the above copyright and source information.
If you make any changes to the text, you must indicate that you did so in a way that makes it clear that the original licensor is not necessarily endorsing your changes.
If you redistribute this text, you must distribute your contributions under the same license as the original.
Pictures included with Scriptures and other documents on this site are licensed just for use with those Scriptures and documents.
For other uses, please contact the respective copyright owners.
Note that in addition to the rules above, revising and adapting God's Word involves a great responsibility to be true to God's Word. See Revelation 22:18-19.
2020-06-19

Source: http://ebible.org/hauulb/ · eBible.org

Talk to us

Tell us where you read from, how the Bible has helped you, or what we could improve. We read every message.