John 16
Litafi Mai-tsarki · Tap a verse to see its cross-references.
1“Na fada maku wannan ne domin kada kuyi tuntube. 2Zasu fitar da ku daga majami'u. Amma, sa'a tana zuwa, wadda idan wani ya kasheku, zai yi zaton aikin Allah yake yi. 3Za suyi haka ne kuwa domin ba su san Uban ko ni ba. 4Na fada maku wadannan abubuwa ne domin in lokacin da zasu faru yayi, ku tuna na fada maku.” Ban fada maku wadannan abubuwa ba tun da farko, domin ina tare da ku. 5Yanzu kuwa za ni wurin wanda ya aiko ni, duk da haka a cikinku, ba wanda ya tambaye ni, 'Ina za ka?' 6Amma saboda na fada maku wadannan abubuwa, bakin ciki ya cika zuciyarku. 7Amma ina gaya maku gaskiya: zai fi ye maku in na tafi. Domin in ban tafi ba, Mai Ta'aziyya ba zai zo gare ku ba, in kuwa na tafi, zan aiko shi gare ku. 8Idan kuwa ya zo, Mai Ta'aziyyar zai fadarkar da duniya a kan zunubi, da adalci, da kuma hukunci. 9Game da zunubi, domin basu gaskata da ni ba, 10Game da adalci, domin za ni wurin Uba, kuma ba za ku sake ganina ba, 11game da hukunci kuma, domin an yanke wa mai mulki duniyan nan hukunci. 12“Akwai abubuwa da yawa da zan gaya maku, amma ba za ku iya fahimta a yanzu ba. 13Saboda haka, sa'adda Ruhu na gaskiya ya zo, zai bishe ku a cikin dukan gaskiyar, domin ba zai yi magana don kansa ba, sai dai duk abin da ya ji, shi zai fada, zai kuma sanar da ku al'amuran da zasu faru. 14Zai daukaka ni, domin zai dauko abubuwa dake nawa ya sanar da ku. 15Duk abinda Uba yake da shi, nawa ne. Domin wannan ne nace zai dauko abubuwa da yake nawa ya sanar da ku. 16“Bayan dan lokaci kadan, ba zaku kara ganina kuma ba. bayan dan lokaci kadan kuma, zaku gan ni.” 17Sai wadansu almajiransa sukace wa juna, “Me nene wannan da yake fadi mana, 'Bayan dan lokaci kadan ba zaku gan ni ba, bayan dan lokaci kadan kuma zaku gan ni?' da kuma, ' zan tafi wurin Uba'?” 18Saboda haka sukace, “Me nene wannan da yake fada, 'Bayan dan lokaci kadan'? Bamu san abinda yake fada mana ba.” 19Yesu kuwa ya ga suna so su tambaye shi, sai ya ce masu, “Wato kuna tambayar juna ne abinda nake nufi da cewa, “Bayan dan lokaci kadan ba zaku gan ni ba, bayan dan lokaci kadan kuma zaku gan ni'? 20Hakika, hakika, ina gaya maku, zaku yi kuka da makoki, amma duniya za ta yi farin ciki, zaku cika da bakin ciki, amma bakin cikinku zai koma farin ciki. 21Mace takan ji zafi lokacin da take nakuda don lokacin haihuwa ya zo. Amma da zarar ta haifi jinjirin nan, ba ta kara tunawa da zafin, domin ta na fariciki an haifi mutum a duniya. 22To yanzu dai kuna bakin ciki, amma zan sake ganinku, kuma ba wanda zai iya kwace maku wannan farin ciki. 23A rannan, ba zaku tambaye ni komai ba. Hakika hakika, ina gaya maku, komai kuka roki Uba a cikin sunana zai ba ku shi. 24Harwa yau, ba ku roki komai cikin sunana ba. Ku roka, zaku karba, domin farin cikin ku ya zama cikakke.” 25“Na fada maku wadannan abubuwa cikin karin magana. Amma sa'a tana zuwa da ba zan kara fada maku komai ba cikin karin magana, amaimakon haka zan gaya maku komai a sarari game da Uba. 26A ranar nan, zaku yi roko a cikin sunana kuma bance maku zan yi addu'a ga Uba a madadinku ba, 27domin Uba da kansa yana kaunarku, domin kun kaunace ni, kun kuma gaskata daga wurin Uban na fito. 28Daga wurin Uban na fito, kuma na shigo duniya. Har wa yau, kuma zan bar duniya in koma wurin Uba.” 29Almajiransa sukace, duba, “Yanzu kake magana a sarari, ba cikin karin magana ba! 30Yanzu mun sani ka san komai, ba sai wani ya tambaye ka ba. Ta haka muka gaskata daga wurin Allah ka fito.” 31Yesu ya amsa masu yace, “Ashe, yanzu kun gaskata? 32Duba, sa'a na zuwa, I, sa'ar ta yi, da za a warwatsa ku, kowa ya koma gidansa, kuma ku bar ni ni kadai. Duk da haka kuwa ba ni kadai nake ba, domin Ubana yana tare da ni. 33Na fada maku wannan ne domin a ciki na ku sami salama. A duniya kuna shan tsanani, amma ku karfafa: na yi nasara da duniya,”

Did you know?
Departure, the Advocate, and joy after grief
- Event notes place this chapter in the Upper Room Discourse, a one-day episode within Holy Week, which those notes list as eight days.Sources: Upper Room Discourse · Holy Week
- Jesus tells the disciples they will be put out of the synagogues. He adds that a time is coming when anyone who kills them will think he is offering a service to God, because they have not known the Father or him.Sources: the Bible text itself
- He says it is for their benefit that he is going away, because unless he goes, the Advocate will not come. When the Spirit of truth comes, he will guide them into all truth, not speaking on his own but saying what he hears and declaring what is to come.Sources: the Bible text itself
Notes written with AI assistance from open sources (Theographic Bible Metadata, CC BY-SA 4.0; Easton’s Bible Dictionary, public domain) and reviewed before publishing.
Credits and license for this translation
Litafi Mai-tsarki The New Testament in the Hausa language of Nigeria copyright © 2020 Door43 World Missions Community Language: Hausa Translation by: Alakirawa, Bayan, Chrispher Ishaya, Dabere, Dacuhus Timothy Danjuma, Danjay, Danjuma Alfred H, Euang Hediza Naohammed, Franklyn Ukazu Udochukwu, Gideon, Gokop, Habibu, James, Kiash Dachung Butus, Lazarus, Nadaki M. Philip, Nenching, Paul, Rebecca, Rev. Ayuba Taiba, Rev. Cain Yusuf Daniel, Rev. Dalhatu Dambo Ayuba, Rev. Dr. Tambanya Yahaya, Rev. Dr. Yakubu Hassan, Rev. Hannatu Samuel Ndberhukwu, Rev. Ibrahim Kassim, Rev. M. Dan'Amarya, Rev. Yakuba Ayuba Contributor: Dacuhus Timothy Danjuma, Euang Hediza Naohammed, Kiash Dachung Butus, Nadaki M. Philip, Rev. Ayuba Taiba, Rev. Cain Yusuf Daniel, Rev. Dalhatu Dambo Ayuba, Rev. Dr. Tambanya Yahaya, Rev. Dr. Yakubu Hassan, Rev. Hannatu Samuel Ndberhukwu, Rev. Ibrahim Kassim, Rev. M. Dan'Amarya, Rev. Yakuba Ayuba This translation is made available to you under the terms of the Creative Commons Attribution Share-Alike license 4.0. You have permission to share and redistribute this Bible translation in any format and to make reasonable revisions and adaptations of this translation, provided that: You include the above copyright and source information. If you make any changes to the text, you must indicate that you did so in a way that makes it clear that the original licensor is not necessarily endorsing your changes. If you redistribute this text, you must distribute your contributions under the same license as the original. Pictures included with Scriptures and other documents on this site are licensed just for use with those Scriptures and documents. For other uses, please contact the respective copyright owners. Note that in addition to the rules above, revising and adapting God's Word involves a great responsibility to be true to God's Word. See Revelation 22:18-19. 2020-06-19
Source: http://ebible.org/hauulb/ · eBible.org