Nations Bible

John 14

Litafi Mai-tsarki · Tap a verse to see its cross-references.

1“Kada zuciyarku ta bachi. Kun gaskata da Allah, sai kuma ku gaskata da ni. 2A gidan Ubana akwai wurin zama dayawa. Da ba haka ba, da na fada maku, domin zan tafi in shirya maku wuri. 3In kuwa na je na shirya maku wuri, zan dawo in karbe ku zuwa wurina domin inda nake kuma ku kasance. 4Kun san hanya inda zan tafi.” 5Toma ya ce wa Yesu, “Ubangiji, bamu san inda za ka tafi ba, yaya za mu san hanyar?” 6Yesu ya ce masa, “Ni ne hanya, ni ne gaskiya, ni ne rai; Ba mai zuwa wurin Uba sai ta wurina. 7Da kun san ni, da kun san Ubana kuma. Amma daga yanzu kun san shi, kuma kun gan shi.” 8Filibus ya ce wa Yesu, “Ubangiji, ka nuna mana Uban, wannan za ya ishe mu.” 9Yesu ya ce masa, “Ina tare da ku da dadewa, amma har yanzu baka san ni ba, Filibus? Duk wanda ya gan ni, ya ga Uban. Yaya za ka ce, 'Nuna mana Uban'? 10Baka gaskata cewa Ina cikin Uban, Uban kuma yana ciki na ba? Maganganun da nake fada maku, ba da ikona nake fadi ba, amma Uban ne da yake zaune a ciki na yake yin ayyukansa. 11Ku gaskata ni cewa ina cikin Uban, Uban kuma na ciki na, ko kuwa ku bada gaskiya domin ayyukan kansu. 12“Lalle hakika, ina gaya maku, duk wanda ya gaskata ni zai yi ayyukan da nake yi, kuma zai yi ayyuka fiye da wadannan, domin zan tafi wurin Uba. 13Duk abinda kuka roka da sunana, zan yi shi domin a daukaka Uban cikin Dan. 14Idan kuka roke ni komai cikin sunana, zan yi shi. 15“Idan kuna kaunata, za ku kiyaye dokokina. 16Sa, annan zan yi addu'a ga Uba, zai kuwa baku wani mai ta'aziya domin ya kasance tare daku har abada. 17Ruhun gaskiya. Wanda duniya ba zata iya karba ba, domin bata gan shi ba, ko ta san shi. Amma ku kun san shi, domin yana tare da ku, zai kuma kasance a cikin ku. 18Ba zan barku ku kadai ba; zan dawo wurin ku. 19Sauran dan gajeren lokaci, duniya kuma ba zata ka ra gani na ba, amma ku kuna gani na. Saboda ina raye, kuma zaku rayu. 20A wannan rana zaku sani ina cikin Ubana, ku kuma kuna ciki na, ni ma ina cikin ku. 21Shi wanda yake da dokokina yake kuma bin su, shine ke kauna ta, kuma shi wanda ke kauna ta Ubana zai kaunace shi, Ni ma kuma zan kaunace shi in kuma bayyana kaina gare shi.” 22Yahuza (ba Iskariyoti ba) ya ce ma Yesu, “Ubangiji, meyasa za ka bayyana kanka a gare mu, ba ga duniya ba?” 23Yesu ya amsa ya ce masa,”Kowa yake kauna ta, zai kiyaye maganata. Ubana kuwa zai kaunace shi, za mu zo wurinsa mu zauna tare da shi. 24Shi wanda baya kauna ta, ba ya kiyaye maganganuna. Maganar da kuke ji ba daga gareni take ba, amma daga Uba wanda ya aiko ni take. 25Na fada maku wadannan abubuwa, sa'adda nake tare da ku. 26Saidai, mai ta'aziyar- Ruhu Mai Tsarki wanda Uba zai aiko cikin sunana, zai koya maku kome, kuma zai tunashe ku dukan abinda na fada maku. 27Na bar ku da salama; ina ba ku salamata. Ba kamar yadda duniya ke bayarwa Nake bayarwa ba. Kada zuciyarku ta baci, kuma kada ku tsorata. 28Kun ji dai na fada maku, 'zan tafi, kuma Zan dawo gare ku'. Idan kuna kaunata, za ku yi farinciki domin za ni wurin Uban, gama Uban ya fi ni girma. 29Yanzu na fada maku kafin ya faru, domin idan ya faru, ku gaskata. 30Ba zan kara magana mai yawa da ku ba, domin mai mulkin duniyan nan yana zuwa. Bashi da iko a kai na, 31amma domin duniya ta san cewa ina kaunar Uban, Ina yin daidai abinda Uban ya Umarce ni. Mu tashi mu tafi daga nan.

Artistic illustration — an interpretation, not a historical record.

Did you know?

Jesus, the Way to the Father

  • Thomas, one of the twelve, tells Jesus that the disciples do not know where he is going, so they cannot know the way. He was also called Didymus, the Greek equivalent of his Hebrew name, which means "twin." Easton's Bible Dictionary (1897) notes that what is known of him is recorded in the fourth Gospel, including this exchange.Sources: the Bible text itself · Thomas
  • Philip, also one of the twelve and a native of Bethsaida, the city of Andrew and Peter, asks Jesus to show them the Father. Jesus replies that he has been with them all this time and that anyone who has seen him has seen the Father. Easton's Bible Dictionary (1897) cites this exchange among the passages suggesting that Philip held a prominent place among the apostles.Sources: the Bible text itself · Phillip the Apostle
  • The disciple who asks why Jesus will reveal himself to the disciples and not to the world is called Judas, not Iscariot, to distinguish him from Judas Iscariot, son of Simon, a man of Kerioth, who betrayed Jesus. Easton's Bible Dictionary (1897) says John is probably referring to the same apostle called Lebbaeus in Matthew, Thaddaeus in Mark, and Judas the brother of James in Luke, and it identifies him as Jude, the author of the epistle.Sources: the Bible text itself · Lebbaeus Thaddaeus · Judas Iscariot

Notes written with AI assistance from open sources (Theographic Bible Metadata, CC BY-SA 4.0; Easton’s Bible Dictionary, public domain) and reviewed before publishing.

Credits and license for this translation
Litafi Mai-tsarki
The New Testament in the Hausa language of Nigeria
copyright © 2020 Door43 World Missions Community
Language: Hausa
Translation by: Alakirawa, Bayan, Chrispher Ishaya, Dabere, Dacuhus Timothy Danjuma, Danjay, Danjuma Alfred H, Euang Hediza Naohammed, Franklyn Ukazu Udochukwu, Gideon, Gokop, Habibu, James, Kiash Dachung Butus, Lazarus, Nadaki M. Philip, Nenching, Paul, Rebecca, Rev. Ayuba Taiba, Rev. Cain Yusuf Daniel, Rev. Dalhatu Dambo Ayuba, Rev. Dr. Tambanya Yahaya, Rev. Dr. Yakubu Hassan, Rev. Hannatu Samuel Ndberhukwu, Rev. Ibrahim Kassim, Rev. M. Dan'Amarya, Rev. Yakuba Ayuba
Contributor: Dacuhus Timothy Danjuma, Euang Hediza Naohammed, Kiash Dachung Butus, Nadaki M. Philip, Rev. Ayuba Taiba, Rev. Cain Yusuf Daniel, Rev. Dalhatu Dambo Ayuba, Rev. Dr. Tambanya Yahaya, Rev. Dr. Yakubu Hassan, Rev. Hannatu Samuel Ndberhukwu, Rev. Ibrahim Kassim, Rev. M. Dan'Amarya, Rev. Yakuba Ayuba
This translation is made available to you under the terms of the
Creative Commons Attribution Share-Alike license 4.0.
You have permission to share and redistribute this Bible translation in any format and to make reasonable revisions and adaptations of this translation, provided that:
You include the above copyright and source information.
If you make any changes to the text, you must indicate that you did so in a way that makes it clear that the original licensor is not necessarily endorsing your changes.
If you redistribute this text, you must distribute your contributions under the same license as the original.
Pictures included with Scriptures and other documents on this site are licensed just for use with those Scriptures and documents.
For other uses, please contact the respective copyright owners.
Note that in addition to the rules above, revising and adapting God's Word involves a great responsibility to be true to God's Word. See Revelation 22:18-19.
2020-06-19

Source: http://ebible.org/hauulb/ · eBible.org

Talk to us

Tell us where you read from, how the Bible has helped you, or what we could improve. We read every message.