James 4
Litafi Mai-tsarki · Tap a verse to see its cross-references.
1Me ke kawo gaba da rashin jituwa a tsakanin ku? Ba yana tasowa ne daga muguwar sha'awa da ke yaki a cikin ku ba? 2Kuna sha'awa, kuma ba ku da shi. Kuna kisa da kyashi, kuma ba za ku iya samu ba. Kuna danbe da fada. Har wa yau baku samu ba domin baku tambaya ba. 3Kun roka kuma ba a baku ba saboda kuna roko ta hanya mara kyau, kuna so ku yi amfani da shi domin miyagun sha'awoyin ku. 4Ku mazinata! Baku sani ba, abokantaka da duniya, tawaye ne ga Allah? Don haka duk wanda ya shiga abokantaka da duniya ya zama magabcin Allah. 5Ko kuna zaton nassi ya fadi haka a banza ne, “Ruhun nan da ke a cikinmu yana da kishi matuka?” 6Amma Allah ya bayar da karin alheri, shi ya sa nassi ya ce, “Allah yana gaba da mai girman kai, Amma yana ba da alheri ga mai tawaliu.” 7Saboda haka ku mika kan ku ga Allah. Ku yi tsayayya da shaidan, zai kuma guje maku. 8Ku matso kusa da Allah, shi kuma za ya matsa kusa da ku. Wanke hannayen ku, ku masu zunubi, ku tsabtace zukatan ku, ku masu zuciya biyu. 9Ku yi bakin ciki, makoki, da kuka! Ku mayar da dariyar ku ta koma bakin ciki, farin cikinku kuma zuwa ga bakin ciki. 10Ku kaskantar da kanku a gaban Ubangiji, shi kuma za ya daukaka ku. 11Kada ku rika zargin juna, 'yan'uwa. Wanda ya ke zargin dan'uwa ko shari'anta dan'uwansa, yana zargin shari'a kuma yana hukunta shari'a. Idan ka hukunta shari'a, ya nuna ba ka biyayya da shari'ar, amma mai hukunci. 12Mai ba da shari'a da yin hukunci daya ne. Shine mai iya ceto kuma ya hallakar. Kai wanene, da ke hukunta makwafcin ka? 13Saurara, ku da kuke cewa, “Yau ko gobe za mu tafi wancan birnin mu yi shekara guda a wurin, muna kasuwanci, mu kuma yi riba.” 14Wa ya san abin da zai faru gobe, kuma yaya rayuwan ka zai kasance? Kai kamar hazo ne mai bayyana bayan dan lokaci kadan ya bace. 15Maimakon haka, sai ka ce, “Idan Ubangiji ya nufa, za mu rayu kuma mu yi wannan ko wancan.” 16Amma yanzu kana fahariya da shirye shiryen ka na takama. Irin wannan fahariya, mugunta ce. 17Saboda haka ga wanda ya san abin da ya kamata ya aikata amma bai yi ba, ya zama zunubi a gare shi.

Did you know?
Passions, the world, and humility
- The chapter asks what causes conflicts and quarrels among those it addresses and answers that they come from passions at war within them. It says they crave what they do not have, kill and covet but cannot obtain it, and quarrel and fight; they do not have because they do not ask, and when they ask they do not receive, because they ask with wrong motives, so that they may squander it on their pleasures.Sources: the Bible text itself
- It calls them adulteresses and says that friendship with the world is hostility toward God, so that whoever chooses to be a friend of the world renders himself an enemy of God. It quotes the words that God opposes the proud but gives grace to the humble, then tells them to submit to God, resist the devil so that he will flee, draw near to God so that He will draw near, cleanse their hands, and purify their hearts.Sources: the Bible text itself
- Those who say they will go to this or that city, spend a year there, carry on business, and make a profit are told that they do not even know what will happen tomorrow, and that they are a mist that appears for a little while and then vanishes. Instead they ought to say, "If the Lord is willing, we will live and do this or that"; boasting in such proud intentions is called evil, and anyone who knows the right thing to do yet fails to do it is guilty of sin.Sources: the Bible text itself
Notes written with AI assistance from open sources (Theographic Bible Metadata, CC BY-SA 4.0; Easton’s Bible Dictionary, public domain) and reviewed before publishing.
Credits and license for this translation
Litafi Mai-tsarki The New Testament in the Hausa language of Nigeria copyright © 2020 Door43 World Missions Community Language: Hausa Translation by: Alakirawa, Bayan, Chrispher Ishaya, Dabere, Dacuhus Timothy Danjuma, Danjay, Danjuma Alfred H, Euang Hediza Naohammed, Franklyn Ukazu Udochukwu, Gideon, Gokop, Habibu, James, Kiash Dachung Butus, Lazarus, Nadaki M. Philip, Nenching, Paul, Rebecca, Rev. Ayuba Taiba, Rev. Cain Yusuf Daniel, Rev. Dalhatu Dambo Ayuba, Rev. Dr. Tambanya Yahaya, Rev. Dr. Yakubu Hassan, Rev. Hannatu Samuel Ndberhukwu, Rev. Ibrahim Kassim, Rev. M. Dan'Amarya, Rev. Yakuba Ayuba Contributor: Dacuhus Timothy Danjuma, Euang Hediza Naohammed, Kiash Dachung Butus, Nadaki M. Philip, Rev. Ayuba Taiba, Rev. Cain Yusuf Daniel, Rev. Dalhatu Dambo Ayuba, Rev. Dr. Tambanya Yahaya, Rev. Dr. Yakubu Hassan, Rev. Hannatu Samuel Ndberhukwu, Rev. Ibrahim Kassim, Rev. M. Dan'Amarya, Rev. Yakuba Ayuba This translation is made available to you under the terms of the Creative Commons Attribution Share-Alike license 4.0. You have permission to share and redistribute this Bible translation in any format and to make reasonable revisions and adaptations of this translation, provided that: You include the above copyright and source information. If you make any changes to the text, you must indicate that you did so in a way that makes it clear that the original licensor is not necessarily endorsing your changes. If you redistribute this text, you must distribute your contributions under the same license as the original. Pictures included with Scriptures and other documents on this site are licensed just for use with those Scriptures and documents. For other uses, please contact the respective copyright owners. Note that in addition to the rules above, revising and adapting God's Word involves a great responsibility to be true to God's Word. See Revelation 22:18-19. 2020-06-19
Source: http://ebible.org/hauulb/ · eBible.org