Nations Bible

Hebrews 8

Litafi Mai-tsarki · Tap a verse to see its cross-references.

1Yanzu abin da muke kokarin cewa shine: Muna da babban firist wanda ke zaune a hannun dama na kursiyi mai martaba dake sammai. 2Shi kuwa bawa ne a wannan wuri mai tsarki, haikali na gaskiya wanda Allah ya shirya ba wani bil'adama ba. 3Kowanne babban firist kuwa yana mika bayebaye da hadayu. Don haka ya kamata a sami abin hadaya. 4Da a ce Almasihu yana duniya ba zai zama firist ba ko kadan. 5Domin a kwai masu mika hadaya bisa ga shari'a. Suna hidimar misalin abubuwan da suke inuwar sama. Kamar yadda Allah ya yi wa Musa gargadi yayin da ya ke shirin gina Alfarwa: ''Duba'' Allah ya ce, ''kayi komai bisa ga salon da aka koya maka a bisa dutse.” 6Amma yanzu hidimar da Almasihu ya karba ta dara tasu dukka, domin kuwa shine matsakancin muhimmin alkawari, wanda aka kammala a kan muhimman alkawura. 7Domin kuwa idan alkawarin fari ba shi da laifi babu anfanin neman alkawari na biyu. 8Da Allah ya sami laifi akan mutane, sai ya ce ''Zan sake sabon alkawari da gidan Isra'ila da kuma gidan Yahuza. 9kuma ba zai zama kamar yadda nayi da kakanninku ba, kamar yadda na rike su a hannu har Na fidda su daga kasar Masar. Basu kuma ci gaba da Alkawarina ba, ni kuwa na yi watsi da su,'' inji Ubangiji. 10Gama wanna shine alkawarin da zan yi da gidan Isra'ila bayan wadannan kwanaki, Inji Ubangiji. Zan sa shari'a ta a bakinsu in kuma rubuta ta a zuciyarsu, Zan kuma zama Allah a garesu, su kuma su zama jama'ata. 11Ba za su kuma koyar da makwabta ko yan'uwansu cewa, ''ku san Ubangiji'' gama dukkanin su za su san ni, daga karami har zuwa babba. 12Zan kuma nuna tausayi ga ayyukan su na rashin adalci, ba kuma zan kara tunawa da zunubansu ba. 13A kan fadin ''sabo'' ya mayar da alkawarin fari tsoho. Wannan kuma da aka ambata tsoho na shirin bacewa.

Artistic illustration — an interpretation, not a historical record.

Did you know?

The True Tabernacle and a New Covenant

  • Hebrews 8 calls the place where the priests serve a copy and shadow of what is in heaven. That is why Moses, when he was about to build the tabernacle, was warned to make everything according to the pattern shown him on the mountain.Sources: the Bible text itself
  • The new covenant promised to the house of Israel and the house of Judah is set against the covenant made with their fathers when they were led out of Egypt, the land of the Nile.Sources: the Bible text itself · Egypt
  • By speaking of a new covenant, the chapter says the first has been made obsolete, and that what is obsolete and aging will soon disappear.Sources: the Bible text itself

Notes written with AI assistance from open sources (Theographic Bible Metadata, CC BY-SA 4.0; Easton’s Bible Dictionary, public domain) and reviewed before publishing.

Places in this chapter

  • Egypt · 30.129, 31.308 · verse 9

Only places identified with high confidence are shown (90% or more according to the scholarly sources compiled by OpenBible). Period map: DARE (Digital Atlas of the Roman Empire), CC BY 4.0; modern map: © OpenStreetMap contributors; places: OpenBible.info (CC BY 4.0).

Credits and license for this translation
Litafi Mai-tsarki
The New Testament in the Hausa language of Nigeria
copyright © 2020 Door43 World Missions Community
Language: Hausa
Translation by: Alakirawa, Bayan, Chrispher Ishaya, Dabere, Dacuhus Timothy Danjuma, Danjay, Danjuma Alfred H, Euang Hediza Naohammed, Franklyn Ukazu Udochukwu, Gideon, Gokop, Habibu, James, Kiash Dachung Butus, Lazarus, Nadaki M. Philip, Nenching, Paul, Rebecca, Rev. Ayuba Taiba, Rev. Cain Yusuf Daniel, Rev. Dalhatu Dambo Ayuba, Rev. Dr. Tambanya Yahaya, Rev. Dr. Yakubu Hassan, Rev. Hannatu Samuel Ndberhukwu, Rev. Ibrahim Kassim, Rev. M. Dan'Amarya, Rev. Yakuba Ayuba
Contributor: Dacuhus Timothy Danjuma, Euang Hediza Naohammed, Kiash Dachung Butus, Nadaki M. Philip, Rev. Ayuba Taiba, Rev. Cain Yusuf Daniel, Rev. Dalhatu Dambo Ayuba, Rev. Dr. Tambanya Yahaya, Rev. Dr. Yakubu Hassan, Rev. Hannatu Samuel Ndberhukwu, Rev. Ibrahim Kassim, Rev. M. Dan'Amarya, Rev. Yakuba Ayuba
This translation is made available to you under the terms of the
Creative Commons Attribution Share-Alike license 4.0.
You have permission to share and redistribute this Bible translation in any format and to make reasonable revisions and adaptations of this translation, provided that:
You include the above copyright and source information.
If you make any changes to the text, you must indicate that you did so in a way that makes it clear that the original licensor is not necessarily endorsing your changes.
If you redistribute this text, you must distribute your contributions under the same license as the original.
Pictures included with Scriptures and other documents on this site are licensed just for use with those Scriptures and documents.
For other uses, please contact the respective copyright owners.
Note that in addition to the rules above, revising and adapting God's Word involves a great responsibility to be true to God's Word. See Revelation 22:18-19.
2020-06-19

Source: http://ebible.org/hauulb/ · eBible.org

Talk to us

Tell us where you read from, how the Bible has helped you, or what we could improve. We read every message.