Hebrews 6
Litafi Mai-tsarki · Tap a verse to see its cross-references.
1Saboda haka, sai mu ci gaba a kan ka'idodin farko na al'amarin Almasihu, har ya zuwa kammala, ba wai mu sake koyar da jigajigan nan na tuba da ibada marar tasiri ba, da na gaskatawa da Allah, 2da kuma na koyarwa a kan wanke-wanke, da dora hannu, da tashin matattu, da dawwamammen hukuci. 3Za mu kuwa ci gaba in Allah ya yarda. 4Domin wadanda aka haskaka zukatansu sarai, har suka dandana baiwar nan Basamaniya, suka kuma sami rabo na Ruhu Mai Tsarki, 5har su ka dandana dadin Maganar Allah, da ikon zamani mai zuwa, 6sa'an nan kuma suka ridda—ba mai yiwuwa ba ne a sake jawo su ga tuba, tun da yake sake gicciye Dan Allah suke yi su da kansu, suka kuma wulakanta shi a sarari. 7Kasa ma da take shanye ruwan da ake yi a kai a kai, take kuma fid da tsire-tsire masu amfani ga wadanda ake nomanta dominsu, Allah yakan sa mata albarka. 8Amma idan tsire-tsirenta kaya ne da kashin yawo, ba ta da amfani ke nan, tana kuma gab da la'antarwa, karshenta dai konewa ne. 9Ko da yake mun fadi haka, a game da ku kam, ya kaunatattu mun tabbata kuna abubuwa mafiya kyau na zancen ceto. 10Gama Allah ba marar adalci ba ne, har da zai ki kula da aikinku, da kuma kaunar sunansa da kuke yi, wajen yi wa tsarkaka hidima, har yanzu ma kuna yi. 11Muna dai bukata kwarai kowannanku ya nuna irin wannan himma ga yin cikkaken bege, tabbatacce, har ya zuwa karshe. 12Don kada ku yi ragwanci, sai dai ku yi koyi da wadanda suka karbi cikar alkawaran nan, ta wurin bangaskiyarsu da hakurinsu. 13Sa'adda Allah ya yi wa Ibrahim alkawari, da yake ba wani wanda ya fi shi girma da zai rantse da shi, sai ya rantse da kansa, 14Ya ce, “Hakika zan yi maka albarka, in kuma ribambamya zuriyarka.” 15Ta haka, Ibrahim bayan da ya jure da hakuri, ya karbi cikar alkawarin. 16Hakika mutane sukan rantse da abin da ya fi su. Rantsuwa kuma ita ce abar da take tabbatarwa da kowacce magana. 17Don haka, sa'adda Allah yake son kara tabbatar wa magadan alkawarin nan dahir, cewa nufinsa ba mai sakewa ba ne sam, sai ya hada da rantsuwa, 18Domin albarkacin abubuwa guda biyun nan marasa sakewa, masu nuna, cewa ba shi yiwuwa Allah ya yi karya, mu da muka gudu muka sami mafaka, mu karfafa kwarai mu riski abin da muka kafa bege a kai. 19Muna da bege, kamar yadda yake ga rai, kafaffe, tabbatacce, shi ne kuma yake shiga har can ciki bayan labulen. 20Inda saboda mu ne Yasu ya riga mu shiga, da yake ya zama Babban Firist na har abada, kwatancin Malkisadak.

Did you know?
Maturity, God's oath, and a priest forever
- A dictionary entry explains the name Abraham as "father of a multitude" and calls him the heir of the promises. Hebrews 6 quotes God's words to him, "I will surely bless you and multiply your descendants," and says that after waiting patiently he obtained the promise.Sources: Abraham · the Bible text itself
- The chapter describes an ordinary custom: people swear by someone greater than themselves, and the oath confirms what was said and ends all argument. Since there was no one greater, God swore by himself, so the heirs of the promise would see that his purpose does not change. The letter speaks of two unchangeable things in which it is impossible for God to lie, and of this hope as an anchor for the soul.Sources: the Bible text itself
- A dictionary entry gives Melchizedek's name as "king of righteousness" and calls him king of Salem. It says that all that is known of him is recorded in Genesis 14:18-20, and that the Old Testament mentions him again only in Psalm 110:4. Hebrews 6 ends with Jesus, as forerunner, entering the inner sanctuary behind the curtain and becoming a high priest forever in Melchizedek's order, a comparison the letter sets out in the next chapter, where Melchizedek is the type of a priest who lives forever.Sources: Melchisedec · the Bible text itself
Notes written with AI assistance from open sources (Theographic Bible Metadata, CC BY-SA 4.0; Easton’s Bible Dictionary, public domain) and reviewed before publishing.
Credits and license for this translation
Litafi Mai-tsarki The New Testament in the Hausa language of Nigeria copyright © 2020 Door43 World Missions Community Language: Hausa Translation by: Alakirawa, Bayan, Chrispher Ishaya, Dabere, Dacuhus Timothy Danjuma, Danjay, Danjuma Alfred H, Euang Hediza Naohammed, Franklyn Ukazu Udochukwu, Gideon, Gokop, Habibu, James, Kiash Dachung Butus, Lazarus, Nadaki M. Philip, Nenching, Paul, Rebecca, Rev. Ayuba Taiba, Rev. Cain Yusuf Daniel, Rev. Dalhatu Dambo Ayuba, Rev. Dr. Tambanya Yahaya, Rev. Dr. Yakubu Hassan, Rev. Hannatu Samuel Ndberhukwu, Rev. Ibrahim Kassim, Rev. M. Dan'Amarya, Rev. Yakuba Ayuba Contributor: Dacuhus Timothy Danjuma, Euang Hediza Naohammed, Kiash Dachung Butus, Nadaki M. Philip, Rev. Ayuba Taiba, Rev. Cain Yusuf Daniel, Rev. Dalhatu Dambo Ayuba, Rev. Dr. Tambanya Yahaya, Rev. Dr. Yakubu Hassan, Rev. Hannatu Samuel Ndberhukwu, Rev. Ibrahim Kassim, Rev. M. Dan'Amarya, Rev. Yakuba Ayuba This translation is made available to you under the terms of the Creative Commons Attribution Share-Alike license 4.0. You have permission to share and redistribute this Bible translation in any format and to make reasonable revisions and adaptations of this translation, provided that: You include the above copyright and source information. If you make any changes to the text, you must indicate that you did so in a way that makes it clear that the original licensor is not necessarily endorsing your changes. If you redistribute this text, you must distribute your contributions under the same license as the original. Pictures included with Scriptures and other documents on this site are licensed just for use with those Scriptures and documents. For other uses, please contact the respective copyright owners. Note that in addition to the rules above, revising and adapting God's Word involves a great responsibility to be true to God's Word. See Revelation 22:18-19. 2020-06-19
Source: http://ebible.org/hauulb/ · eBible.org