Nations Bible

Hebrews 4

Litafi Mai-tsarki · Tap a verse to see its cross-references.

1Saboda haka, sai muyi lura kwarai don kada wani ya kasa kai ga shiga hutun da aka alkawarta maku na Allah. 2Don mun ji albishir game da hutun Allah kamar yadda aka fada masu. Amma wancan sakon bai anfana ga wadanda suka ji ba tare da sun bada gaskiya ga sakon ba. 3Ai mu, wadanda muka gaskata-mune zamu shiga wannan hutun, kamar yadda ya ce, “Yadda na yi rantsuwa cikin fushina, baza su shiga hutu na ba.” Ya fadi hakan, ko da yake ya gama aikin hallittarsa tun daga farkon duniya. 4Domin yayi fadi a wani wuri game da rana ta bakwai, “Allah ya huta a rana ta bakwai daga dukkan ayyukansa.” 5Ya sake cewa, “Baza su taba shiga hutu na ba.” 6Saboda haka, tun da hutun Allah na kebe domin masu su shiga, kuma tun da Isra'ilawa da yawa wadanda suka ji sakon nan mai kyau game da hutunsa ba su shiga ba saboda rashin biyayya, 7Allah ya sake shirya wata rana da ake kira, “Yau.” Ya sa wannan rana sa'adda yayi magana ta wurin Dauda, wanda ya ce tun da dadewa da aka fara fada, “Yau idan kun ji muryarsa, kada ku taurare zukatanku.” 8Don idan Joshua ya ba su hutu, da Allah ba zai sake magana a kan wata rana ba. 9Saboda haka, akwai hutun asabar kebabbe ga mutanen Allah. 10Don shi wanda ya shiga hutun Allah shi kansa ma ya huta daga ayyukansa, kamar yadda Allah yayi da nasa. 11Saboda haka muyi marmarin shiga wancan hutun, don kada kowa ya fadi ga irin rashin biyayyar da suka yi. 12Maganar Allah kuwa rayayyiyace, kuma mai ci, fiye da takobi mai kaifi-biyu. Takan ratsa har tsakanin rai da ruhu, kuma tana kaiwa bargo. Takan iya bincika tunanin zuciya da manufarta. 13Babu halittaccen abu da ke boye a idon Allah. Sai dai, kome a sarari yake, kuma a bayyane yake a idonsa wanda lallai ne zamu bada lissafin kanmu a gare shi. 14Da yake muna da babban firist wanda ya ratsa sammai, Yesu Dan Allah, sai mu riki bangaskiyarmu da karfi. 15Domin babban firist namu ba marar tausayi ga kasawarmu bane, amma wanda aka jarraba ne ta ko wanne hali irin yadda aka yi mana, sai dai ba'a same shi da zunubi ba. 16Sai mu zo wurin kursiyin alheri gabagadi, domin a yi mana jinkai mu kuwa sami alherin da zai taimake mu a lokacin bukata.

Artistic illustration — an interpretation, not a historical record.

Did you know?

The promise of God’s rest

  • Hebrews 4 sets God’s rest on the seventh day beside a rest the people had not yet entered. It recalls that on the seventh day God rested from all his works, finished since the foundation of the world. Because Joshua did not give them rest, the chapter says, God later spoke of another day, and a Sabbath rest remains for the people of God.Sources: the Bible text itself
  • Those who first heard the good news, the chapter says, gained nothing from the message because they did not share the faith of those who understood it, and they did not enter God’s rest because of disobedience, after God had sworn in anger that they never would. Long afterward he named a day “Today” and spoke through David, urging hearers not to harden their hearts if they heard his voice. That David is identified as the eighth and youngest son of Jesse, a citizen of Bethlehem, who early on tended his father’s sheep on the uplands of Judah.Sources: the Bible text itself · David
  • The same chapter calls the word of God living and active, sharper than any double-edged sword, and able to judge the thoughts and intentions of the heart, and it says nothing in all creation is hidden from God’s sight. It then speaks of Jesus, the Son of God, as a great high priest who has passed through the heavens, tempted in every way as others are, yet without sin, so that people may approach the throne of grace with confidence.Sources: the Bible text itself

Notes written with AI assistance from open sources (Theographic Bible Metadata, CC BY-SA 4.0; Easton’s Bible Dictionary, public domain) and reviewed before publishing.

Credits and license for this translation
Litafi Mai-tsarki
The New Testament in the Hausa language of Nigeria
copyright © 2020 Door43 World Missions Community
Language: Hausa
Translation by: Alakirawa, Bayan, Chrispher Ishaya, Dabere, Dacuhus Timothy Danjuma, Danjay, Danjuma Alfred H, Euang Hediza Naohammed, Franklyn Ukazu Udochukwu, Gideon, Gokop, Habibu, James, Kiash Dachung Butus, Lazarus, Nadaki M. Philip, Nenching, Paul, Rebecca, Rev. Ayuba Taiba, Rev. Cain Yusuf Daniel, Rev. Dalhatu Dambo Ayuba, Rev. Dr. Tambanya Yahaya, Rev. Dr. Yakubu Hassan, Rev. Hannatu Samuel Ndberhukwu, Rev. Ibrahim Kassim, Rev. M. Dan'Amarya, Rev. Yakuba Ayuba
Contributor: Dacuhus Timothy Danjuma, Euang Hediza Naohammed, Kiash Dachung Butus, Nadaki M. Philip, Rev. Ayuba Taiba, Rev. Cain Yusuf Daniel, Rev. Dalhatu Dambo Ayuba, Rev. Dr. Tambanya Yahaya, Rev. Dr. Yakubu Hassan, Rev. Hannatu Samuel Ndberhukwu, Rev. Ibrahim Kassim, Rev. M. Dan'Amarya, Rev. Yakuba Ayuba
This translation is made available to you under the terms of the
Creative Commons Attribution Share-Alike license 4.0.
You have permission to share and redistribute this Bible translation in any format and to make reasonable revisions and adaptations of this translation, provided that:
You include the above copyright and source information.
If you make any changes to the text, you must indicate that you did so in a way that makes it clear that the original licensor is not necessarily endorsing your changes.
If you redistribute this text, you must distribute your contributions under the same license as the original.
Pictures included with Scriptures and other documents on this site are licensed just for use with those Scriptures and documents.
For other uses, please contact the respective copyright owners.
Note that in addition to the rules above, revising and adapting God's Word involves a great responsibility to be true to God's Word. See Revelation 22:18-19.
2020-06-19

Source: http://ebible.org/hauulb/ · eBible.org

Talk to us

Tell us where you read from, how the Bible has helped you, or what we could improve. We read every message.