Nations Bible

Hebrews 2

Litafi Mai-tsarki · Tap a verse to see its cross-references.

1Saboda haka, lalle ne mu kara mai da hankali musamman da abubuwan da mu ka ji, don kada mu yi sakaci, su sullube mana. 2Idan kuwa maganar nan da aka fada ta bakin mala'iku ta zama tabbatacciya, har kowanne keta umarni da rashin biyayya, suka gamu da sakamakonsu wanda ya kamace su, 3ta kaka za mu tsira, in mun ki kula da ceto mai girma haka? Domin Ubangiji da kansa, shi ne ya fara sanar da shi, wadanda suka saurare shi kuma suka tabbatar mana da shi. 4San'nan kuma Allah da kansa ya shaida ta wasu alamu, da abubuwan al'ajabai, da mu'ajizai iri iri, da kuma baiwar Ruhu Mai Tsarki dabam dabam da ya rarraba kamar yadda ya nufa. 5Ai ba ga mala'iku ba ne Allah ya sa mulkin duniyar nan da za a yi, wanda muke zance. 6Amma wani ya shaida a wani wuri cewa, 'Mutum ma menene, har da za ka tuna da shi? Ko dan mutum ma, har da za ka kula da shi?' 7Ka sa mutum ya gaza mala'iku; Ka nada shi da daukaka da girma. Bisa dukkan hallitta. 8Ka dora shi a kan dukkan halittarka, ka kuma mallakar da kome a karkashin sawayensa. Domin Allah ya mallakar da dukkan abubuwa a karkashinsa. Bai bar kome a kebe ba. Amma kuwa har a yanzu ba mu ga yana sarrafa dukkan abubuwa ba tukuna. 9Amma mun ga wani wanda dan lokaci aka sa shi ya gaza mala'iku, shine Yesu, an nada shi da daukaka da girma, saboda shan wuyarsa ta mutuwa, wanan kuwa duk ta wurin alherin Allah ne Yesu ya mutu saboda kowa. 10Saboda haka, ya dace ga Allah, shi da dukkan abubuwa suka kasance domin sa, ta gare shi, domin ya kawo 'ya'ya masu yawa ga samun daukaka. Domin a kammala cetonsu ta wurin shan wuyarsa. 11Domin da shi mai tsarkakewar da kuma wadanda aka tsarkaken, duk tushensu daya ne. Saboda wanan dalili ne shi ya sa ba ya jin kunyar kiran su 'ya'uwansa. 12Da yace, ''zan sanar da sunanka ga ya'uwana, a tsakiyar taronsu zan yabe ka da waka.'' 13Har wa yau, yace, ''Zan dogara a gare shi.'' Da kuma ''Ga ni nan, ni da 'ya'yan da Allah ya ba ni.'' 14Wato tun da yake 'ya'yan Allah duk suna da nama da jini, Yesu ma ya dauki kamannin haka, ta wurin mutuwa ya hallakar da mai ikon mutuwa, wato Iblis. 15Ya kuma 'yanta duk wadanda tun haihuwarsu suke zaman bauta sabo da tsoron mutuwa. 16Don hakika ba mala'iku yake taimako ba, a'a, zuriyar Ibrahim ne yake taimako. 17Saboda haka, lalle ne ya zama kamar yan'uwansa ta kowacce hanya, domin ya zama babban Firist, mai jinkai, mai aminci kuma na al'amarin Allah, ya kuma mika hadayar sulhu ta gafarta zunuban jama'a. 18Tun da yake Yesu ma da kansa ya sha wahala, sa'adda aka gwada shi, don haka, zai taimaki wadanda ake yi wa gwaji.

Artistic illustration — an interpretation, not a historical record.

Did you know?

Sharing humanity, crowned through suffering

  • Hebrews 2 recalls that the message spoken by angels was binding, and that every transgression and disobedience received its just punishment, then asks how anyone can escape who neglects so great a salvation. That salvation was first announced by the Lord, confirmed to us by those who heard him, and affirmed by God through signs, wonders, various miracles, and gifts of the Holy Spirit distributed according to his will.Sources: the Bible text itself
  • The chapter quotes a testimony that man was made a little lower than the angels, crowned with glory and honor, with everything placed under his feet. When God subjected all things to him, he left nothing outside his control, yet at present we do not see everything subject to him. Jesus, made a little lower than the angels, is now crowned with glory and honor because he suffered death, so that by the grace of God he might taste death for everyone.Sources: the Bible text itself
  • Hebrews 2 says Jesus helps not angels but the descendants of Abraham, and that he had to be made like his brothers in every way so that he might become a merciful and faithful high priest in service to God, to make atonement for the sins of the people. Abraham, son of Terah, is called father of a multitude and described as the heir of the promises.Sources: the Bible text itself · Abraham

Notes written with AI assistance from open sources (Theographic Bible Metadata, CC BY-SA 4.0; Easton’s Bible Dictionary, public domain) and reviewed before publishing.

Credits and license for this translation
Litafi Mai-tsarki
The New Testament in the Hausa language of Nigeria
copyright © 2020 Door43 World Missions Community
Language: Hausa
Translation by: Alakirawa, Bayan, Chrispher Ishaya, Dabere, Dacuhus Timothy Danjuma, Danjay, Danjuma Alfred H, Euang Hediza Naohammed, Franklyn Ukazu Udochukwu, Gideon, Gokop, Habibu, James, Kiash Dachung Butus, Lazarus, Nadaki M. Philip, Nenching, Paul, Rebecca, Rev. Ayuba Taiba, Rev. Cain Yusuf Daniel, Rev. Dalhatu Dambo Ayuba, Rev. Dr. Tambanya Yahaya, Rev. Dr. Yakubu Hassan, Rev. Hannatu Samuel Ndberhukwu, Rev. Ibrahim Kassim, Rev. M. Dan'Amarya, Rev. Yakuba Ayuba
Contributor: Dacuhus Timothy Danjuma, Euang Hediza Naohammed, Kiash Dachung Butus, Nadaki M. Philip, Rev. Ayuba Taiba, Rev. Cain Yusuf Daniel, Rev. Dalhatu Dambo Ayuba, Rev. Dr. Tambanya Yahaya, Rev. Dr. Yakubu Hassan, Rev. Hannatu Samuel Ndberhukwu, Rev. Ibrahim Kassim, Rev. M. Dan'Amarya, Rev. Yakuba Ayuba
This translation is made available to you under the terms of the
Creative Commons Attribution Share-Alike license 4.0.
You have permission to share and redistribute this Bible translation in any format and to make reasonable revisions and adaptations of this translation, provided that:
You include the above copyright and source information.
If you make any changes to the text, you must indicate that you did so in a way that makes it clear that the original licensor is not necessarily endorsing your changes.
If you redistribute this text, you must distribute your contributions under the same license as the original.
Pictures included with Scriptures and other documents on this site are licensed just for use with those Scriptures and documents.
For other uses, please contact the respective copyright owners.
Note that in addition to the rules above, revising and adapting God's Word involves a great responsibility to be true to God's Word. See Revelation 22:18-19.
2020-06-19

Source: http://ebible.org/hauulb/ · eBible.org

Talk to us

Tell us where you read from, how the Bible has helped you, or what we could improve. We read every message.