Galatians 6
Litafi Mai-tsarki · Tap a verse to see its cross-references.
1'Yan'uwa, idan an kama mutum yana yin wani laifi, ku da kuke da ruhaniya sai ku dawo da mutumin a hanya cikin ruhun tawali'u, ka lura da kanka don kada kai ma ka fada a cikin gwaji. 2Ku dauki damuwar juna, ta yin haka za ku cika shari'ar Almasihu. 3Domin idan kowa ya zacci shi wani abu ne alhali shi ba komai ba ne rudin kansa yake yi. 4Sai kowa ya auna aikin sa. Sa'annan zai sami abin da zai yi takama, ba sai ya kwatanta kansa da wani ba. 5Domin kowa zai dauki nauyin kayansa. 6Wanda aka koya masa maganar, wajibi ne ya ci amfanin abubuwansa masu kyau duka tare da malaminsa. 7Kada fa a yaudare ku ba a yi wa Allah ba'a. Dukan abin da mutum ya dasa, shine abin da zai girba. 8Domin shi wanda ya shuka wa kansa dabi'ar zunubi zai girbi hallaka, amma shi wanda ya shuka cikin Ruhu, zai girbi rai madawwami daga Ruhu. 9Kada mu gaji da aikata nagarta, domin a lokacin da ya dace za mu yi girbi idan ba mu gaji ba. 10Saboda haka, lokacin da muke da zarafi, sai mu yi nagarta ga kowa. Mu yi nagarta mussamman ga wadanda suke na iyalin bangaskiya. 11Dubi yawan wasikun da na rubuta maku da hannuna. 12Wadanda suke so su nuna hali mai kyau cikin jiki suke tilasta ku yin kaciya. Suna yin haka ne kadai saboda kada a tsananta masu saboda gicciyen Almasihu. 13Domin ko su wadanda suke masu kaciya ba su kiyaye shari'a. Maimakon haka suna so ne a yi maku kaciya don su yi fahariya game jikinku. 14Bari kada ya zama ina fahariya sai dai ta gicciyen Ubangijinmu Yesu Almasihu. Ta wurinsa ne aka gicciye duniya a gare ni, ni kuma ga duniya. 15Domin kaciya ko rashin kaciya ba komai ba ne. Maimakon haka, sabon halita ne ke da muhimmanci. 16Ga dukan wadanda za su zauna cikin wannan ka'ida, bari salama da jinkai su kasance tare da su da kuma bisa Isra'ila na Allah. 17Daga yanzu zuwa nan gaba kada wani ya dame ni, domin ina dauke da tabbai na Yesu a jikina. 18Alherin Ubangijinmu Yesu Almasihu ya kasance da ruhun ku, 'yan'uwa. Amin.

Did you know?
Burdens, the Harvest, and the Cross
- The chapter sets two duties side by side. Those who are spiritual should restore with gentleness someone caught in a trespass, and carry one another's burdens, which the letter calls fulfilling the law of Christ. Each person, however, should test his own work and carry his own load, rather than think he is something when he is nothing and boast by comparing himself with someone else.Sources: the Bible text itself
- The writer uses the image of sowing and reaping: God is not to be mocked, and a person reaps what he sows. The one who sows to please the flesh reaps destruction from the flesh; the one who sows to please the Spirit reaps eternal life from the Spirit. Readers are urged not to grow weary in doing good, for in due time they will reap a harvest if they do not give up, and to do good to all, especially to the family of faith.Sources: the Bible text itself
- The writer calls attention to the large letters he is using as he writes with his own hand. He says that some try to compel circumcision in order to make a good outward impression, to avoid persecution for the cross of Christ, and to boast in the flesh of others, though the circumcised do not themselves keep the law. He asks never to boast except in the cross of our Lord Jesus Christ, says that neither circumcision nor uncircumcision means anything and that what counts is a new creation, and states that he bears on his body the marks of Jesus.Sources: the Bible text itself
Notes written with AI assistance from open sources (Theographic Bible Metadata, CC BY-SA 4.0; Easton’s Bible Dictionary, public domain) and reviewed before publishing.
Credits and license for this translation
Litafi Mai-tsarki The New Testament in the Hausa language of Nigeria copyright © 2020 Door43 World Missions Community Language: Hausa Translation by: Alakirawa, Bayan, Chrispher Ishaya, Dabere, Dacuhus Timothy Danjuma, Danjay, Danjuma Alfred H, Euang Hediza Naohammed, Franklyn Ukazu Udochukwu, Gideon, Gokop, Habibu, James, Kiash Dachung Butus, Lazarus, Nadaki M. Philip, Nenching, Paul, Rebecca, Rev. Ayuba Taiba, Rev. Cain Yusuf Daniel, Rev. Dalhatu Dambo Ayuba, Rev. Dr. Tambanya Yahaya, Rev. Dr. Yakubu Hassan, Rev. Hannatu Samuel Ndberhukwu, Rev. Ibrahim Kassim, Rev. M. Dan'Amarya, Rev. Yakuba Ayuba Contributor: Dacuhus Timothy Danjuma, Euang Hediza Naohammed, Kiash Dachung Butus, Nadaki M. Philip, Rev. Ayuba Taiba, Rev. Cain Yusuf Daniel, Rev. Dalhatu Dambo Ayuba, Rev. Dr. Tambanya Yahaya, Rev. Dr. Yakubu Hassan, Rev. Hannatu Samuel Ndberhukwu, Rev. Ibrahim Kassim, Rev. M. Dan'Amarya, Rev. Yakuba Ayuba This translation is made available to you under the terms of the Creative Commons Attribution Share-Alike license 4.0. You have permission to share and redistribute this Bible translation in any format and to make reasonable revisions and adaptations of this translation, provided that: You include the above copyright and source information. If you make any changes to the text, you must indicate that you did so in a way that makes it clear that the original licensor is not necessarily endorsing your changes. If you redistribute this text, you must distribute your contributions under the same license as the original. Pictures included with Scriptures and other documents on this site are licensed just for use with those Scriptures and documents. For other uses, please contact the respective copyright owners. Note that in addition to the rules above, revising and adapting God's Word involves a great responsibility to be true to God's Word. See Revelation 22:18-19. 2020-06-19
Source: http://ebible.org/hauulb/ · eBible.org