Galatians 2
Litafi Mai-tsarki · Tap a verse to see its cross-references.
1Daga nan, bayan shekara goma sha hudu na koma Urushalima tare da Barnaba. Na kuma dauki Titus tare da ni. 2Na koma ne domin Allah ya nuna mani in koma. Sai na gabatar masu shelar bisharan da nake yi a cikin al'ummai. (Amma a kebe na yi magana da wadanda aka dauka muhimman shugabanni). Na yi haka ne domin in tabbatar da cewa ba gudun banza nake yi ba, ko kuma na yi gudun banza. 3Amma ko Titus wanda yake tare da ni, Baheline, ba wanda ya tilasta masa ya yi kaciya. 4Wannan maganar ta taso ne daga 'yan'uwan karya da suka zo cikinmu a boye su ga 'yancin mu a cikin Yesu Almsihu. Sun yi marmarin su maishe mu bayi ga doka. 5Ba mu mika kanmu biyayya gare su ba ko da na sa'a daya, domin gaskiyar bishara ta kasance babu canzawa domin ku. 6Amma su wadanda a ke ganin su da muhimmanci ba su taimaka mani da komai ba. Ko su wanene su bai dame ni ba. Allah ba ya karbar wanda mutane suka fi so. 7Maimakon haka, suka ga an danka mani shelar bishara ga wadanda ba su da kaciya. Kamar yadda aka ba Bitrus shelar bishara ga masu kaciya. 8Gama Allah wanda yake yin aiki a cikin Bitrus domin manzanci zuwa ga masu kaciya, haka kuma yake aiki ciki na zuwa ga al'ummai. 9Da Yakubu, Kefas, da Yahaya, wadanda a ke gani masu gina ikilisiya, suka fahimci alherin da aka ba ni, suka bamu hannun dama na zumunci ni da Barnaba, Sun yi haka ne kawai domin mu mu tafi zuwa wurin al'ummai, su kuma su je wurin masu kaciya. 10Suna kuma so mu tuna da matalauta. Ni ma ina da aniyar yin haka. 11Da Kefas ya kai Antakiya, na yi tsayayya da shi a gabansa domin shine ke da kuskure. 12Da ma Kefas yana cin abinci tare da al'ummai kafin zuwan wasu mutane daga wurin Yakubu. Amma da wadannan mutane suka iso, sai ya dena kuma ya ware kansa daga al'umman. Yana jin tsoron wadannan mutanen da ke bukatar kaciya. 13Hakannan ma sauran Yahudawa da suke tare da shi sun bi munafurcin sa. A sakamakon haka Barnaba ma ya bi munafurcin su. 14Da na ga basu bin gaskiyar da take cikin bisharar, na gaya wa Kefas a gaban su duka, “Idan kai Bayahude ne kana rayuwar ka ta al'ummai a maimakon rayuwar Yahudawa, to ta yaya za ka tilasta wa al'ummai su yi zaman Yahudawa? “ 15Mu da muke Yahudawa daga haihuwa, ba ''Al'ummai masu zunubi ba.'' 16Ku sani fa, babu wanda za a baratar ta ayyukan shari'a. A maimakon haka an baratar da su ta wurin bangaskiya cikin Yesu Almasihu. Mun zo ga cikin Almasihu Yesu domin mu samu baratarwa ta bangaskiya cikin Almasihu, kuma ba ta ayyukan shari'a ba. Domin ta ayyukan shari'a babu wanda zai samu baratarwa. 17Amma idan mun nemi Allah ya baratar da mu cikin Almasihu, mun samu kanmu masu zunubi kenan, Almasihu ya zama bawan zunubi ne? Ko kadan! 18Idan na sake gina dogara ta a kan shari'a, dogarar da na juya wa baya, na nuna kai na mai karya shari'a kenan. 19Ta wurin shari'a na mutu ga shari'a, domin in yi rayuwa irin ta Allah. 20An giciye ni tare da Almasihu, ba nine ke rayuwa ba kuma, amma Almasihu ke rayuwa a cikina. Rayuwar da nake yi a yanzu a cikin jiki, ina yin ta ne, ta wurin bangaskiya ga dan Allah, wanda ya kaunace ni ya ba da kansa domina. 21Ban yi watsi da alherin Allah ba, domin idan adalci ya wanzu ta wurin shari'a, ashe Almasihu ya mutu a banza kenan.

Did you know?
Gentiles, Fellowship, and a Clash at Antioch
- Titus went with Paul and Barnabas to Jerusalem. Easton's Bible Dictionary (1897) says he appears to have been a Gentile and that his name never appears in Acts. Paul writes that Titus, though a Greek, was not compelled to be circumcised.Sources: Titus · the Bible text itself
- The later clash took place at Antioch in Syria, on the Orontes, some three hundred miles north of Jerusalem. The city ranked third among the cities of the Roman Empire, after Rome and Alexandria, and it was there that believers were first called Christians.Sources: Antioch (Syria) · the Bible text itself
- Easton's Bible Dictionary (1897) describes James, named with Cephas and John as one of the pillars, as head of the church at Jerusalem, where he presided at the council on the Gentiles. Paul says that before certain men came from James, Cephas used to eat with the Gentiles, but then drew back for fear of the circumcision group.Sources: James (Brother of Jesus) · the Bible text itself
Notes written with AI assistance from open sources (Theographic Bible Metadata, CC BY-SA 4.0; Easton’s Bible Dictionary, public domain) and reviewed before publishing.
Places in this chapter
- Jerusalem · 31.777, 35.234 · verse 1
- Antioch · Today: Antioch on the Orontes · 36.227, 36.172 · verse 11
Only places identified with high confidence are shown (90% or more according to the scholarly sources compiled by OpenBible). Period map: DARE (Digital Atlas of the Roman Empire), CC BY 4.0; modern map: © OpenStreetMap contributors; places: OpenBible.info (CC BY 4.0).
Credits and license for this translation
Litafi Mai-tsarki The New Testament in the Hausa language of Nigeria copyright © 2020 Door43 World Missions Community Language: Hausa Translation by: Alakirawa, Bayan, Chrispher Ishaya, Dabere, Dacuhus Timothy Danjuma, Danjay, Danjuma Alfred H, Euang Hediza Naohammed, Franklyn Ukazu Udochukwu, Gideon, Gokop, Habibu, James, Kiash Dachung Butus, Lazarus, Nadaki M. Philip, Nenching, Paul, Rebecca, Rev. Ayuba Taiba, Rev. Cain Yusuf Daniel, Rev. Dalhatu Dambo Ayuba, Rev. Dr. Tambanya Yahaya, Rev. Dr. Yakubu Hassan, Rev. Hannatu Samuel Ndberhukwu, Rev. Ibrahim Kassim, Rev. M. Dan'Amarya, Rev. Yakuba Ayuba Contributor: Dacuhus Timothy Danjuma, Euang Hediza Naohammed, Kiash Dachung Butus, Nadaki M. Philip, Rev. Ayuba Taiba, Rev. Cain Yusuf Daniel, Rev. Dalhatu Dambo Ayuba, Rev. Dr. Tambanya Yahaya, Rev. Dr. Yakubu Hassan, Rev. Hannatu Samuel Ndberhukwu, Rev. Ibrahim Kassim, Rev. M. Dan'Amarya, Rev. Yakuba Ayuba This translation is made available to you under the terms of the Creative Commons Attribution Share-Alike license 4.0. You have permission to share and redistribute this Bible translation in any format and to make reasonable revisions and adaptations of this translation, provided that: You include the above copyright and source information. If you make any changes to the text, you must indicate that you did so in a way that makes it clear that the original licensor is not necessarily endorsing your changes. If you redistribute this text, you must distribute your contributions under the same license as the original. Pictures included with Scriptures and other documents on this site are licensed just for use with those Scriptures and documents. For other uses, please contact the respective copyright owners. Note that in addition to the rules above, revising and adapting God's Word involves a great responsibility to be true to God's Word. See Revelation 22:18-19. 2020-06-19
Source: http://ebible.org/hauulb/ · eBible.org