Ephesians 2
Litafi Mai-tsarki · Tap a verse to see its cross-references.
1Amma da ku matattu ne cikin zunubanku da laifofinku. 2A cikinsu kuka yi rayuwa bisa ga al'amuran duniyan nan. Kuka biye wa mai sarautar ikokin sararin sama, wannan ruhun ne da ke aiki cikin kangararrun 'ya'ya. 3Da can dukanmu muna cikin wadannan marasa bada gaskiya. Muka biye wa mugun burin jikinmu. Muna aikata halin mutuntaka da na tunaninmu. Bisa ga dabi'a 'ya'ya ne wadanda sun cancanci fushin Allah, kamar wadansu. 4Amma Allah mai yalwar jinkai ne, sabili da matukar kauna da ya kaunace mu. 5Sa'anda muke matattu cikin zunubai, ya kawo mu cikin sabon rai tare da Almasihu. Ta wurin alheri aka cece mu. 6Allah ya tashe mu tare ya kuma sa muka zauna tare a matsayi guda cikin Almasihu Yesu. 7Ya yi wannan domin a zamanai masu zuwa ya nuna mana matukar yalwar arzikin alherinsa ta wurin Yesu. Yana nuna mana wannan ta wurin alherinsa. 8Domin ta wurin alheri aka cece ku ta wurin bangaskiya, wannan ba daga gare ku ba ne, kyauta ce ta Allah. 9Ba daga ayyuka ba, Saboda wannan dalili kada kowa ya yi fahariya. 10Gama mu aikin hannuwansa ne, halitattu cikin Almasihu Yesu domin mu yi kyawawan ayyuka, wadanda tun da Allah ya tanada, mu yi rayuwa a cikinsu. 11Saboda haka ku tuna da ku al'ummai ne a dabi'ar jiki. Ana kiranku “marasa kaciya”, abin da ake kira kaciya cikin jiki wadda hannayen mutane ke yi. 12Gama a lokacin nan a rabe kuke da Almasihu. Ku bare ne ga mutanen Isra'ila. Ku baki ne ga wa'adodi na al'kawarai. Ba ku da tabbaci a kan gobe. Ba ku da Allah a cikin duniya. 13Amma yanzu a cikin Almasihu Yesu ku da da kuke nesa da Allah, an kawo ku kusa da shi ta wurin jinin Almasihu. 14Gama shine salamar mu. Domin ya mai da biyun daya. Cikin jikinsa ne ya rushe katangar gaba da ta raba mu da juna. 15Wato ya kawar da shari'a mai umarnai da sharudda, domin ya halitta sabon mutum daya a cikinsa. Yin haka ya kawo salama. 16Ya yi haka domin ya sulhunta mutum biyu cikin jiki daya ga Allah ta wurin gicciye. Ta wurin gicciye ya kashe gabar da ke tsakaninsu. 17Yesu ya zo ya yi maku shelar salama ku da kuke nesa da ku na kusa. 18Domin ta wurin Yesu dukanmu biyu cikin Ruhu daya muna da hanya zuwa wurin Uba. 19Sabo da haka yanzu ku al'ummai, ko daya, ba bare ba ne. Maimakon haka ku abokai ne tare da kebabbun Allah, abokan aiki. 20Wadanda an gina su bisa tushen manzanni da annabawa. Almasihu Yesu da kansa shine mafificin dutsen ginin. 21A cikinsa dukan ginin ya hade tare, suna kuma girma kamar haikali cikin Ubangiji. 22A cikinsa ne kuma ake gina ku gaba daya kun zama mazaunin Allah a cikin Ruhu.

Did you know?
Made alive and brought near
- Ephesians 2 addresses readers who were dead in their trespasses and sins, conforming to the ways of this world and of the ruler of the power of the air. It says that God, rich in mercy, made them alive with Christ, raised them up with him, and seated them with him in the heavenly realms, and that they have been saved by grace through faith, not from themselves but as the gift of God, not by works, so that no one can boast.Sources: the Bible text itself
- Ephesians 2 reminds readers who are Gentiles in the flesh that they were called uncircumcised by the so-called circumcision, which the chapter describes as done in the body by human hands. It says that at that time they were separate from Christ, alienated from the commonwealth of Israel, and strangers to the covenants of the promise, without hope and without God in the world.Sources: the Bible text itself
- Ephesians 2 calls Christ himself our peace: he made the two one and tore down the dividing wall of hostility, abolishing in his flesh the law of commandments and decrees, to create in himself one new man and reconcile both to God in one body. He preached peace to those far away and those near, and through him both have access to the Father by one Spirit. The readers are no longer strangers and foreigners but fellow citizens with the saints and members of God’s household, built on the apostles and prophets with Christ Jesus as the cornerstone, and in him they too are being built together into a holy temple, a dwelling for God in his Spirit.Sources: the Bible text itself
Notes written with AI assistance from open sources (Theographic Bible Metadata, CC BY-SA 4.0; Easton’s Bible Dictionary, public domain) and reviewed before publishing.
Credits and license for this translation
Litafi Mai-tsarki The New Testament in the Hausa language of Nigeria copyright © 2020 Door43 World Missions Community Language: Hausa Translation by: Alakirawa, Bayan, Chrispher Ishaya, Dabere, Dacuhus Timothy Danjuma, Danjay, Danjuma Alfred H, Euang Hediza Naohammed, Franklyn Ukazu Udochukwu, Gideon, Gokop, Habibu, James, Kiash Dachung Butus, Lazarus, Nadaki M. Philip, Nenching, Paul, Rebecca, Rev. Ayuba Taiba, Rev. Cain Yusuf Daniel, Rev. Dalhatu Dambo Ayuba, Rev. Dr. Tambanya Yahaya, Rev. Dr. Yakubu Hassan, Rev. Hannatu Samuel Ndberhukwu, Rev. Ibrahim Kassim, Rev. M. Dan'Amarya, Rev. Yakuba Ayuba Contributor: Dacuhus Timothy Danjuma, Euang Hediza Naohammed, Kiash Dachung Butus, Nadaki M. Philip, Rev. Ayuba Taiba, Rev. Cain Yusuf Daniel, Rev. Dalhatu Dambo Ayuba, Rev. Dr. Tambanya Yahaya, Rev. Dr. Yakubu Hassan, Rev. Hannatu Samuel Ndberhukwu, Rev. Ibrahim Kassim, Rev. M. Dan'Amarya, Rev. Yakuba Ayuba This translation is made available to you under the terms of the Creative Commons Attribution Share-Alike license 4.0. You have permission to share and redistribute this Bible translation in any format and to make reasonable revisions and adaptations of this translation, provided that: You include the above copyright and source information. If you make any changes to the text, you must indicate that you did so in a way that makes it clear that the original licensor is not necessarily endorsing your changes. If you redistribute this text, you must distribute your contributions under the same license as the original. Pictures included with Scriptures and other documents on this site are licensed just for use with those Scriptures and documents. For other uses, please contact the respective copyright owners. Note that in addition to the rules above, revising and adapting God's Word involves a great responsibility to be true to God's Word. See Revelation 22:18-19. 2020-06-19
Source: http://ebible.org/hauulb/ · eBible.org