Nations Bible

Colossians 3

Litafi Mai-tsarki · Tap a verse to see its cross-references.

1Idan dai Allah ya tashe ku tare da Almasihu, ku nemi abubuwan da ke sama, inda Almasihu ke zaune a hannun dama na Allah. 2Yi tunanin a kan abubuwan da ke sama, ba a kan abubuwan da ke kasa ba. 3Gama ku kun mutu, ranku kuma yana boye tare da Almasihu cikin Allah. 4Sa'anda Almasihu ya bayyana, wanda shine ranku, sa'anan ku kuma zaku bayyana tare da shi cikin daukakarsa. 5Ku kashe sha'awacce-sha'awaccen da suke a duniya - zina da fasikanci, rashin tsarki, muguwar sha'awa, mummunar buri, da kuma kwadayi, wadda shine bautar gumaka. 6Saboda wandannan abubuwa ne fushin Allah ke zuwa a kan marasa biyayya. 7A cikin wadannan abubuwa ne kuka yi rayuwa a da da kuke zauna a cikinsu. 8Amma yanzu dole ku kawar da wadannan - zafin rai, fushi, mugayen manufofi, zage-zage, da kazamar magana daga bakinku. 9Kada ku yi wa juna karya, domin kun tube tsohon mutumin da ayyukansa, 10kun kuma yafa sabon mutum, wanda ake sabontawa cikin sani bisa ga surar wannan da ya hallice shi. 11A nan ne inda babu Baheline da Bayahude, mai kaciya da marar kaciya, bare, baubawa, ko Basikitiye, bawa ko yantacce, amma Almasihu shine duka, yana kuma cikin duka. 12A matsayin ku na zababbun Allah, masu tsarki da kaunatattu sai ku yafa jinkai, ayyukan kirki, saukin kai, kamewa da hakuri. 13Yi hakuri da juna. Ku yi wa juna alheri. Idan wani na da damuwa da wani, ku gafarta kamar yadda Ubangiji ya gafarta maku. 14Fiye da wadanan abubuwa duka, ku kasance da kauna, wanda itace cikakkiyar kammalla. 15Bari salamar Almasihu ta mallaki zukatanku. Sabili da wannan salama ce aka kiraye ku cikin jiki daya. Ku yi godiya. 16Ku bar maganar Almasihu ta zauna a cikinku a yalwace. Da dukan hikima, ku koyar, ku kuma gargadi juna da zabura, wakoki, da wakokin yabo na ruhaniya. Kuna rairawa tare da godiya cikin zukatanku ga Allah. 17Kuma duk abin da zaku yi cikin magana ko aiki ku yi duka cikin sunan Ubangiji Yesu. Kuna yin godiya ga Allah Uba ta wurinsa. 18Mata, ku yi biyayya ga mazajenku, yadda yakamata a cikin Ubangiji. 19Mazaje, ku kaunaci matayenku, kada ku muzguna masu. 20Yaya, ku yi wa iyayen ku biyayya cikin dukan komai, domin wannan yana faranta wa Ubangiji rai. 21Ku Ubanni, kada ku cakuni 'ya'yanku domin kada su karaya. 22Bayi, ku yi wa iyayengijinku na jiki biyayya cikin kowane abu, ba tare da bautan ganin ido ba don faranta wa mutane rai, amma da sahihiyar zuciya. Ji tsoron Ubangiji. 23Duk abin da kuke yi, ku yi aiki daga zuci domin Ubangiji ba domin mutane ba. 24Kun san cewa, zaku karbi sakamako na gado daga wurin Ubangiji. Domin Ubangiji Almasihu kuke bauta wa. 25Domin kowa ya yi rashin adalci zai karbi sakamakon rashin adalcin da ya yi, kuma babu son kai.

Artistic illustration — an interpretation, not a historical record.

Did you know?

New life in one body and at home

  • This chapter pictures a changed life as a change of clothing. Readers are said to have taken off the old self with its practices and put on the new self, which is being renewed in knowledge in the image of its Creator. They are then told to clothe themselves with hearts of compassion, kindness, humility, gentleness, and patience, and to put on love over all these virtues as the bond of perfect unity.Sources: the Bible text itself
  • The chapter lists Greek and Jew, circumcised and uncircumcised, barbarian, Scythian, slave and free, and declares that here none of these distinctions remains, because Christ is all and is in all.Sources: the Bible text itself
  • The chapter then gives instructions for household relationships: wives and husbands, children and parents, and slaves and their earthly masters. Fathers are warned not to provoke their children, so that the children will not become discouraged. Slaves are told to obey with sincerity of heart, not only while they are being watched, and to work with their whole being for the Lord rather than for men, with the promise of an inheritance from the Lord as a reward; whoever does wrong will be repaid, and there is no favoritism.Sources: the Bible text itself

Notes written with AI assistance from open sources (Theographic Bible Metadata, CC BY-SA 4.0; Easton’s Bible Dictionary, public domain) and reviewed before publishing.

Credits and license for this translation
Litafi Mai-tsarki
The New Testament in the Hausa language of Nigeria
copyright © 2020 Door43 World Missions Community
Language: Hausa
Translation by: Alakirawa, Bayan, Chrispher Ishaya, Dabere, Dacuhus Timothy Danjuma, Danjay, Danjuma Alfred H, Euang Hediza Naohammed, Franklyn Ukazu Udochukwu, Gideon, Gokop, Habibu, James, Kiash Dachung Butus, Lazarus, Nadaki M. Philip, Nenching, Paul, Rebecca, Rev. Ayuba Taiba, Rev. Cain Yusuf Daniel, Rev. Dalhatu Dambo Ayuba, Rev. Dr. Tambanya Yahaya, Rev. Dr. Yakubu Hassan, Rev. Hannatu Samuel Ndberhukwu, Rev. Ibrahim Kassim, Rev. M. Dan'Amarya, Rev. Yakuba Ayuba
Contributor: Dacuhus Timothy Danjuma, Euang Hediza Naohammed, Kiash Dachung Butus, Nadaki M. Philip, Rev. Ayuba Taiba, Rev. Cain Yusuf Daniel, Rev. Dalhatu Dambo Ayuba, Rev. Dr. Tambanya Yahaya, Rev. Dr. Yakubu Hassan, Rev. Hannatu Samuel Ndberhukwu, Rev. Ibrahim Kassim, Rev. M. Dan'Amarya, Rev. Yakuba Ayuba
This translation is made available to you under the terms of the
Creative Commons Attribution Share-Alike license 4.0.
You have permission to share and redistribute this Bible translation in any format and to make reasonable revisions and adaptations of this translation, provided that:
You include the above copyright and source information.
If you make any changes to the text, you must indicate that you did so in a way that makes it clear that the original licensor is not necessarily endorsing your changes.
If you redistribute this text, you must distribute your contributions under the same license as the original.
Pictures included with Scriptures and other documents on this site are licensed just for use with those Scriptures and documents.
For other uses, please contact the respective copyright owners.
Note that in addition to the rules above, revising and adapting God's Word involves a great responsibility to be true to God's Word. See Revelation 22:18-19.
2020-06-19

Source: http://ebible.org/hauulb/ · eBible.org

Talk to us

Tell us where you read from, how the Bible has helped you, or what we could improve. We read every message.