Acts 8
Litafi Mai-tsarki · Tap a verse to see its cross-references.
1Bulus ya amince da mutuwarsa. A wannan rana tsanani mai zafi ya fara tasowa akan Iklisiya da take a Urushalima, sai masu bangaskiya duka suka bazu ko ina a cikin garuruwan Yahudiya da Samariya, sai manzannin kadai aka bari. 2Amintattun mutane suka bizne Istifanus suka yi babban makoki game da shi. 3Amma Shawulu ya yi wa Iklisiya mugunta kwarai, ya dinga shiga gida gida yana jawo mutane maza da mata, kuma yana kulle su cikin kurkuku. 4Duk da haka masu bangaskiyar nan da suka warwatsu suka tafi suka dinga yada wa'azin maganar. 5Filibus ya tafi can Samariya ya yi shelar Almasihu. 6Da taron mutane suka ji kuma suka ga alamun da Filibus yake yi, sai suka mai da hankali dukansu domin su ji abinda yake fadi. 7Domin kazaman ruhohi sun fito daga cikin mutane da yawa da suka saurare shi suna kuka da kururuwa; nakasassun mutane dayawa da guragu suka warke. 8Kuma aka yi farin ciki mai girma a birnin. 9Amma akwai wani mutum a cikin birnin da ake kira Siman, wanda tun farko shi masafi ne da kuma dan dabo, yana yi wa mutanen Samariya abubuwan ban mamaki, yayin da yake kiran kansa wani mai muhimmanci. 10Dukan Samariyawa, manya da yara, suna sauraronsa, su kan ce, ''Wannan mutum shine ikon Allahn nan wanda ake kira mai girma.'' 11Suna sauraron sa, domin ya dade yana yi masu abubuwan mamaki da tsafe-tsafensa. 12Amma da suka yi bangaskiya da wa'azin bisharar da Filibus yake yi game da mulkin Allah da sunan Yesu Almasihu, sai aka yi masu Baftisma dukansu maza da mata. 13Har shima Siman da kansa ya ba da gaskiya. Bayan an yi masa Baftisma ya cigaba da bin Filibus, da ya ga ana nuna alamu da manyan ayyuka, sai ya yi mamaki. 14Da manzannin da ke Urushalima suka ji labarin Samariya ta karbi maganar Allah, sai suka aika masu Bitrus da Yahaya. 15Da suka iso, suka yi masu addu'a, domin su karbi Ruhu Mai Tsarki. 16Domin har wannan lokaci, Ruhu Mai Tsarki bai sauko kan kowannensu ba; an dai yi masu baftisma ne kadai cikin sunan Ubangiji Yesu. 17Sai Bitrus da Yahaya suka dora masu hannuwansu, sai suka karbi Ruhu Mai Tsarki. 18Sa'adda Siman yaga ana bayar da Ruhu Mai Tsarki ta wurin dorawar hannuwan manzanni, ya basu kudi. 19Ya ce, “Ku bani wannan iko, ni ma, don duk wanda na dora wa hannu ya karbi Ruhu Mai Tsarki.'' 20Amma Bitrus yace masa, ''Azurfarka ta lalace tare da kai, saboda kana tunanin za ka malaki baiwar Ubangiji da kudi. 21Baka da wani rabo a wannan al'amari, domin zuciyarka ba daidai take da Allah ba. 22Saboda haka ka tuba daga wannan muguntarka, ka kuma yi addu'a ga Ubangiji, domin mai yiwuwa ya gafarta maka game da manufar zuciyarka. 23Domin na gane kana cikin bacin rai da kuma cikin daurin zunubi.'' 24Siman ya amsa ya ce, ''Kayi addu'a ga Ubangiji domina, kada wani daga cikin abubuwan nan da ka fada ya faru da ni.'' 25Sa'anda Bitrus da Yahaya suka bada shaida kuma suka fadi maganar Ubangiji, sun koma Urushalima; akan hanya, suka yi wa'azin bishara a kauyukan samariyawa da yawa. 26Yanzu kuwa Mala'ikan Ubangiji ya yi wa Filibus magana cewa, ''Tashi ka tafi ta kudu da hanyar da ta yi kasa daga Urushalima zuwa Gaza'' (wannan hanyar yana cikin hamada.) 27Ya kuwa tashi ya tafi. Sai ga wani mutum daga Habasha, baba ne mai babban matsayi a karkashin Kandakatu, sarauniyar Habasha. Shine yake mulkin dukan dukiyarta. Ya zo Urushalima domin ya yi ibada. 28Yana komawa zaune cikin karussarsa, kuma yana karanta Littafin annabi Ishaya. 29Ruhun ya ce wa Filibus, ''Ka je kusa da karussar nan.'' 30Sai Filibus ya gudu ya same shi, kuma ya ji shi yana karanta littafin annabi Ishaya, sai ya ce, ''Ka fahimci abin da kake karantawa?'' 31Bahabashen ya ce. ''Yaya zan iya, idan ba wani ya bishe ni ba?'' Ya roki Filibus ya shigo cikin karussar ya zauna tare da shi. 32Wannan kuwa shine nassin da Bahabashen yake karantawa, ''An kai shi kamar tunkiya zuwa mayanka; shiru kuma, kamar dan rago a hannun masu sosayarsa, bai bude baki ba. 33Cikin kaskancinsa aka yi masa shari'a da rashin adalci: Wa zai bada tarihin tsararsa? Domin an dauke ransa daga duniya.'' 34Sai baban ya tambayi Filibus, ya ce, ''Na roke ka, gaya mani, game da wa annabin yake magana? Da kansa, ko kuwa wani mutum dabam?'' 35Filibus ya fara magana; akan littafin Ishaya, ya kuwa yi masa wa'azi akan Yesu. 36Yayin da suke tafiya akan hanya, sai suka iso bakin wani kogi; Baban ya ce, “Duba, ga ruwa anan; me zai hana ayi mani baftisma?” 37Filibus ya ce,” Idan ka gaskanta da zuciya daya, ana iya yi maka baftisma.” Sai Bahabashen ya ce, “Na gaskata Yesu Almasihu shine Dan Allah.” 38Sai Bahabashen ya umarta a tsai da karussar. Sai suka zo wurin ruwa dukan su biyu, Filibus da baban, Filibus kuwa yayi masa baftisma. 39Yayin da suka fito daga cikin ruwan, Ruhun Ubangiji ya dauke Filibus; baban bai sake ganin shi ba, sai ya ci gaba da tafiyar sa yana murna. 40Amma Filibus ya bayyana a Azotus. Ya ratsa wannan yankin yana wa'azin bishara a dukan garuruwan, har sa'anda ya iso Kaisariya.

Did you know?
The message spreads beyond Jerusalem
- After Stephen’s death, a great persecution broke out against the church in Jerusalem, and all except the apostles were scattered through Judea and Samaria. Philip, one of the seven and later called the evangelist, was among them; he went first to Samaria, where the crowds gave their attention to his message about the Christ.Sources: the Bible text itself · Phillip the Evangelist
- Before Philip arrived, Simon had long astounded Samaria by sorcery, and people called him the divine power known as the Great Power. He believed and was baptized, then offered money for the power to give the Holy Spirit by the laying on of hands; the word simony, for buying a spiritual office, is derived from his name.Sources: the Bible text itself · Simon the Sorcerer
- Two roads linked Jerusalem and Gaza; Philip was sent along the one through Hebron and a thinly inhabited district called the desert. There he met an Ethiopian eunuch, treasurer to Candace, queen of the Ethiopians, returning from worship in Jerusalem and reading the prophet Isaiah in his chariot. Candace was a title borne by successive queens of Meroe in Upper Nubia, a wealthy center of trade between Africa and southern Asia.Sources: the Bible text itself · Phillip the Evangelist · Candace
Notes written with AI assistance from open sources (Theographic Bible Metadata, CC BY-SA 4.0; Easton’s Bible Dictionary, public domain) and reviewed before publishing.
Places in this chapter
- Jerusalem · 31.777, 35.234 · verses 1, 14, 25, 26, 27
- Judea · Today: Judea 1 · 31.777, 35.234 · verse 1
- Samaria · Today: Samaria 2 · 32.276, 35.195 · verses 1, 5, 9, 14, 25
- Gaza · Today: Tell Harube · 31.504, 34.464 · verse 26
- Ethiopia · 16.935, 33.751 · verse 27
- Ashdod · Today: Tel Ashdod · 31.757, 34.658 · verse 40
- Caesarea · Today: Caesarea Maritima · 32.500, 34.892 · verse 40
Only places identified with high confidence are shown (90% or more according to the scholarly sources compiled by OpenBible). Period map: DARE (Digital Atlas of the Roman Empire), CC BY 4.0; modern map: © OpenStreetMap contributors; places: OpenBible.info (CC BY 4.0).
Credits and license for this translation
Litafi Mai-tsarki The New Testament in the Hausa language of Nigeria copyright © 2020 Door43 World Missions Community Language: Hausa Translation by: Alakirawa, Bayan, Chrispher Ishaya, Dabere, Dacuhus Timothy Danjuma, Danjay, Danjuma Alfred H, Euang Hediza Naohammed, Franklyn Ukazu Udochukwu, Gideon, Gokop, Habibu, James, Kiash Dachung Butus, Lazarus, Nadaki M. Philip, Nenching, Paul, Rebecca, Rev. Ayuba Taiba, Rev. Cain Yusuf Daniel, Rev. Dalhatu Dambo Ayuba, Rev. Dr. Tambanya Yahaya, Rev. Dr. Yakubu Hassan, Rev. Hannatu Samuel Ndberhukwu, Rev. Ibrahim Kassim, Rev. M. Dan'Amarya, Rev. Yakuba Ayuba Contributor: Dacuhus Timothy Danjuma, Euang Hediza Naohammed, Kiash Dachung Butus, Nadaki M. Philip, Rev. Ayuba Taiba, Rev. Cain Yusuf Daniel, Rev. Dalhatu Dambo Ayuba, Rev. Dr. Tambanya Yahaya, Rev. Dr. Yakubu Hassan, Rev. Hannatu Samuel Ndberhukwu, Rev. Ibrahim Kassim, Rev. M. Dan'Amarya, Rev. Yakuba Ayuba This translation is made available to you under the terms of the Creative Commons Attribution Share-Alike license 4.0. You have permission to share and redistribute this Bible translation in any format and to make reasonable revisions and adaptations of this translation, provided that: You include the above copyright and source information. If you make any changes to the text, you must indicate that you did so in a way that makes it clear that the original licensor is not necessarily endorsing your changes. If you redistribute this text, you must distribute your contributions under the same license as the original. Pictures included with Scriptures and other documents on this site are licensed just for use with those Scriptures and documents. For other uses, please contact the respective copyright owners. Note that in addition to the rules above, revising and adapting God's Word involves a great responsibility to be true to God's Word. See Revelation 22:18-19. 2020-06-19
Source: http://ebible.org/hauulb/ · eBible.org