Nations Bible

Acts 22

Litafi Mai-tsarki · Tap a verse to see its cross-references.

1“Yanuwa da Ubanni, ku saurari kariya ta zuwa gare ku yanzu.” 2Da taron sun ji Bulus na magana a harshen Ibraniyawa sai sun yi tsit. Ya ce, 3Ni Bayahude ne daga garin Tarwasa na Kilikiya, amma a karkashin Gamaliyal aka ilimantar da ni. An horar da ni sosai bisa ga bin hanyar dokokin kakkaninmu. Ina da himma ga bin Allah kamar yadda ku ma kuna da ita. 4Na tsananta wa wannan Hanyan har ga mutuwa; na daure maza da mata sa'annan na jefa su cikin gidan yari. 5Hakannan ma babban firist da dukan dattawa za su ba da shaida cewa na karbi izini daga wurinsu domin 'yan'uwa da ke a Dimashku, saboda in tafi can. Haki na shine in daure mabiyan Hanyan nan, in kawo su Urushalima domin a hukunta su. 6Sa'anda ina cikin tafiya, ina kuma kusa da Dimashku, da tsakar rana sai farat daya ga babban haske daga sama ya haskaka kewaye dani. 7Na fadi kasa sa'anan na ji murya na ce da ni, 'Shawulu, Shawulu, don me kake tsananta mani?' 8Na amsa, 'Wanene kai, Ubangiji?' Ya ce mani, 'Nine Yesu Banazarat wanda kake tsananta wa.' 9Wadanda ke tare da ni sun ga hasken, amma ba su gane muryar wanda ya yi magana da ni ba. 10Na ce, 'Me zan yi ya Ubangiji?” Ubangiji ya ce mani, 'Tashi ka tafi cikin Dimashku, a can za a fada maka abinda wajibi ne ka yi. 11Ban iya ganin wuri ba domin walkiyar hasken, sai na tafi cikin Dimashku ta wurin jagorancin wadanda ke tare da ni. 12A can na sami wani mai suna Ananiya, mai tsoron Allah bisa ga sharia, da kyakyawan suna kuma a gaban Yahudawa da ke zama a can. 13Ya zo gare ni ya ce, 'Dan'uwa Shawulu, karbi ganin gari.' A daidai wannan sa'a na gan shi. 14Sa'annan ya ce, 'Allah na kakkaninmu ya zabe ka ka san nufinsa, ka ga Mai Adalcin nan, ka kuma ji muryar da ke fitowa daga bakinsa. 15Gama za ka zama mashaidinsa ga dukan mutane game da abinda ka gani da wanda ka ji. 16A yanzu me ka ke jira? 'Tashi a yi maka baftisma a wanke zunubanka, kana kira bisa sunansa.' 17Bayan da na dawo Urushalima, sa'anda ina addu'a a cikin haikali, sai na karbi wahayi. 18Na gan shi ya ce mani, 'Gaggauta ka bar Urushalima yanzu, domin ba za su yarda da shaidarka game da ni ba.' 19Na ce, 'Ubangiji, su da kansu sun san yadda na sa su a kurkuku na kuma doddoke wadanda suka gaskanta da kai a kowacce masujada. 20A sa'anda a ke zubar da jinin mashaidinka Istifanus, ina nan tsaye ina goyon baya, ina kuma lura da rigunan wadanda suka kashe shi.' 21Amma ya ce mani, 'Tafi, domin zan aike ka can wurin Al'ummai.' 22Mutanen sun bar shi yayi magana har zuwa ga wannan lokacin. Amma sai suka ta da murya suna cewa, 'A kawar da wannan dan taliki daga duniya: don bai kamata ya rayu ba.' 23Sa'anda suke tadda muryarsu, suna jefar da tufafinsu da kuma baza kura a iska, 24babban hafsan ya umarta a kawo Bulus a farfajiyan. Ya umarta da cewa a bincike shi da bulala, domin ya san dalilin da suka ta da ihu gaba da shi haka. 25Bayan da suka daure shi da tsirkiya, Bulus ya ce wa Jarumin da ke kusa da shi, “Ko daidai ne bisa ga doka a yi wa Barome wanda ma sharia ba ta kashe shi ba bulala?” 26Da Jarumin ya ji haka, ya tafi wurin babban hafsan, yana cewa, “Me kake so ka yi? Gama wanan mutumin dan asalin Roma ne.” 27Babban hafsa ya zo ya ce masa, “Gaya mani, kai dan asalin Roma ne?” Bulus ya ce, “Haka ne.” 28Babban hafsan ya amsa masa, “Da kudi masu yawa na sayi yancin zama dan kasa.” Amma Bulus ya ce, “An haife ni dan kasar Roma. 29“Sai mutanen da sun zo su tuhume shi sun bar shi nan da nan. Babban hafsa shi ma ya tsorata da ya gane Bulus dan asalin Roma ne, domin ya riga ya daure shi. 30Washegari, babban hafsan ya so ya san gaskiyar tuhuma da Yahudawa suke yi a kan Bulus. Sai ya kwance shi daga sarka, ya kuma umarci babban firist da dukan majalisa su sadu. Sai ya kawo Bulus ya sa shi a tsakiyarsu.

Artistic illustration — an interpretation, not a historical record.

Did you know?

Paul's Defense in Jerusalem

  • Paul began his defense in Hebrew, and the crowd grew even quieter. He presented himself as a Jew born in Tarsus of Cilicia, raised in Jerusalem, and educated at the feet of Gamaliel in strict conformity to the law of the fathers. A dictionary entry describes Gamaliel as a learned Pharisee, grandson of the rabbi Hillel, and president of the Sanhedrin during the reigns of Tiberius, Caligula, and Claudius.Sources: the Bible text itself · Gamaliel
  • Paul recalled imprisoning and beating believers, and standing by in approval while he watched over the garments of those who killed Stephen. A dictionary entry calls Stephen, one of the seven deacons, the first Christian martyr, and notes that the stoners laid their clothes at the feet of the young Pharisee Saul of Tarsus, a scene that left a deep impression which Paul recalls in this speech.Sources: the Bible text itself · Stephen
  • The crowd listened until Paul said he would be sent far away to the Gentiles; then they shouted that he was not fit to live, threw off their cloaks, and tossed dust into the air. As they stretched him out to strap him down, he asked the centurion whether it was lawful to flog a Roman citizen without a trial, and told the commander that he had been born a citizen, while the commander had paid a high price for his. A chronology dates this testimony, and his appearance before the Council the next day, to AD 54.Sources: the Bible text itself · Paul gives his testimony · Paul goes before the Council

Notes written with AI assistance from open sources (Theographic Bible Metadata, CC BY-SA 4.0; Easton’s Bible Dictionary, public domain) and reviewed before publishing.

Places in this chapter

  • Cilicia · 36.913, 34.892 · verse 3
  • Jerusalem · 31.777, 35.234 · verses 3, 5, 17, 18
  • Tarsus · 36.913, 34.892 · verse 3
  • Damascus · 33.511, 36.306 · verses 5, 6, 10, 11, 12
  • Nazareth · 32.702, 35.298 · verse 8

Only places identified with high confidence are shown (90% or more according to the scholarly sources compiled by OpenBible). Period map: DARE (Digital Atlas of the Roman Empire), CC BY 4.0; modern map: © OpenStreetMap contributors; places: OpenBible.info (CC BY 4.0).

Credits and license for this translation
Litafi Mai-tsarki
The New Testament in the Hausa language of Nigeria
copyright © 2020 Door43 World Missions Community
Language: Hausa
Translation by: Alakirawa, Bayan, Chrispher Ishaya, Dabere, Dacuhus Timothy Danjuma, Danjay, Danjuma Alfred H, Euang Hediza Naohammed, Franklyn Ukazu Udochukwu, Gideon, Gokop, Habibu, James, Kiash Dachung Butus, Lazarus, Nadaki M. Philip, Nenching, Paul, Rebecca, Rev. Ayuba Taiba, Rev. Cain Yusuf Daniel, Rev. Dalhatu Dambo Ayuba, Rev. Dr. Tambanya Yahaya, Rev. Dr. Yakubu Hassan, Rev. Hannatu Samuel Ndberhukwu, Rev. Ibrahim Kassim, Rev. M. Dan'Amarya, Rev. Yakuba Ayuba
Contributor: Dacuhus Timothy Danjuma, Euang Hediza Naohammed, Kiash Dachung Butus, Nadaki M. Philip, Rev. Ayuba Taiba, Rev. Cain Yusuf Daniel, Rev. Dalhatu Dambo Ayuba, Rev. Dr. Tambanya Yahaya, Rev. Dr. Yakubu Hassan, Rev. Hannatu Samuel Ndberhukwu, Rev. Ibrahim Kassim, Rev. M. Dan'Amarya, Rev. Yakuba Ayuba
This translation is made available to you under the terms of the
Creative Commons Attribution Share-Alike license 4.0.
You have permission to share and redistribute this Bible translation in any format and to make reasonable revisions and adaptations of this translation, provided that:
You include the above copyright and source information.
If you make any changes to the text, you must indicate that you did so in a way that makes it clear that the original licensor is not necessarily endorsing your changes.
If you redistribute this text, you must distribute your contributions under the same license as the original.
Pictures included with Scriptures and other documents on this site are licensed just for use with those Scriptures and documents.
For other uses, please contact the respective copyright owners.
Note that in addition to the rules above, revising and adapting God's Word involves a great responsibility to be true to God's Word. See Revelation 22:18-19.
2020-06-19

Source: http://ebible.org/hauulb/ · eBible.org

Talk to us

Tell us where you read from, how the Bible has helped you, or what we could improve. We read every message.