2 Timothy 3
Litafi Mai-tsarki · Tap a verse to see its cross-references.
1Amma ka san da wannan: a cikin kwanakin karshe za a yi lokuta masu matsananciyar wahala. 2Gama mutane za su zama masu son kansu, masu son kudi, masu Kumburi, da girman kai, masu sabo, marasa biyayya ga iyaye, marasa godiya, da kuma marasa tsarki. 3Za su kasance marasa dabi'a, wadanda basu son jituwa da kowa, masu tsegumi, marasa kamun kai, 'yan tawaye, marasa kaunar nagarta. 4Za su zama masu zagon kasa, taurin kai, masu takama, da masu kaunar anishuwa fiye da kaunar Allah. 5Za su kasance da siffar ibada amma za su musunci ikonta. Ka juya daga wadannan mutanen. 6A cikinsu akwai wadanda suke shiga gidaje suna yaudarar mataye marasa hikima. Wadannan ne mataye wadanda suke cike da zunubi, kuma sun kauce hanya sabili da sha'awoyi dabam daban. 7Wadannan matayen suna ta koyo, amma ba za su taba kai wa ga sanin gaskiya ba. 8Kamar yadda Yannisu da Yambrisu suka yi jayayya da Musa. Haka nan wadannan malaman karya kuma suke yin tsayayya da gaskiya. Mutane ne lalatattu a zuciya, marasa sahihiyar bangaskiya. 9Amma ba za su yi nisa ba. Domin wautarsu za ta bayyana a fili ga kowa, kamar wadannan mutane. 10Amma kai, ka bi koyarwata, da dabi'ata, nufe nufena, da bangaskiyata, da jimriyata, da kaunata, da hakurina, 11da yawan kuncina, da wahalolina, da duk abubuwan da suka faru da ni a Antakiya, da Ikoniya da kuma Listra. Na jure a cikin kuncina. Amma a cikinsu dukka, Ubangiji ya cece ni. 12Duk wadanda su ke so su yi rayuwa ta ibada a cikin Almasihu Yesu za su sha tsanani. 13Miyagun mutane da masu hila za su yi ta kara lalacewa. Za su badda wasu. Su da kansu ma sun bijire. 14Amma kai, ka ci gaba da abubuwan da ka koya kuma ka gaskata da zuciya daya. Ka san daga wurin wanda ka koya. 15Ka san da cewa, tun kana dan karamin yaro ka san wadannan littattafai masu tsarki. Wadannan suna iya mai da kai mai hikima domin ceto ta wurin bangaskiya a cikin Almasihu Yesu. 16Dukkan Nassi hurarre ne daga Allah. Yana da amfani domin koyarwa, domin tsautawa, domin gyara, kuma domin horarwa cikin adalci. 17Wannan domin mutumin Allah ya zama cikakke ne, shiryayye domin dukkan ayyukan nagarta.

Did you know?
Hard times and opposition to the truth
- This chapter compares people who oppose the truth with Jannes and Jambres. A Bible dictionary identifies Jannes as one of the Egyptians who withstood Moses, and Jambres as one of those who opposed Moses in Egypt. The letter says that, like them, these opponents are depraved in mind and disqualified from the faith, and that their folly will be plain to everyone.Sources: Jannes · Jambres · the Bible text itself
- Paul recalls the persecutions and sufferings that came upon him in Antioch, Iconium, and Lystra, and says the Lord rescued him from all those persecutions. On the first missionary journey with Barnabas, Jews in Antioch, in the extreme north of Pisidia, stirred up violent opposition, and the two had to leave; in Iconium they were persecuted by the Jews and fled to Lystra. Iconium was the capital of ancient Lycaonia; Lystra was a town of Lycaonia in Asia Minor, in a wild district.Sources: Antioch (Pisidia) · Iconium · Lystra · the Bible text itself
Notes written with AI assistance from open sources (Theographic Bible Metadata, CC BY-SA 4.0; Easton’s Bible Dictionary, public domain) and reviewed before publishing.
Places in this chapter
- Antioch · Today: Antioch in Pisidia · 38.306, 31.189 · verse 11
- Iconium · Today: Konya · 37.872, 32.492 · verse 11
- Lystra · Today: Tel Lystra · 37.602, 32.338 · verse 11
Only places identified with high confidence are shown (90% or more according to the scholarly sources compiled by OpenBible). Period map: DARE (Digital Atlas of the Roman Empire), CC BY 4.0; modern map: © OpenStreetMap contributors; places: OpenBible.info (CC BY 4.0).
Credits and license for this translation
Litafi Mai-tsarki The New Testament in the Hausa language of Nigeria copyright © 2020 Door43 World Missions Community Language: Hausa Translation by: Alakirawa, Bayan, Chrispher Ishaya, Dabere, Dacuhus Timothy Danjuma, Danjay, Danjuma Alfred H, Euang Hediza Naohammed, Franklyn Ukazu Udochukwu, Gideon, Gokop, Habibu, James, Kiash Dachung Butus, Lazarus, Nadaki M. Philip, Nenching, Paul, Rebecca, Rev. Ayuba Taiba, Rev. Cain Yusuf Daniel, Rev. Dalhatu Dambo Ayuba, Rev. Dr. Tambanya Yahaya, Rev. Dr. Yakubu Hassan, Rev. Hannatu Samuel Ndberhukwu, Rev. Ibrahim Kassim, Rev. M. Dan'Amarya, Rev. Yakuba Ayuba Contributor: Dacuhus Timothy Danjuma, Euang Hediza Naohammed, Kiash Dachung Butus, Nadaki M. Philip, Rev. Ayuba Taiba, Rev. Cain Yusuf Daniel, Rev. Dalhatu Dambo Ayuba, Rev. Dr. Tambanya Yahaya, Rev. Dr. Yakubu Hassan, Rev. Hannatu Samuel Ndberhukwu, Rev. Ibrahim Kassim, Rev. M. Dan'Amarya, Rev. Yakuba Ayuba This translation is made available to you under the terms of the Creative Commons Attribution Share-Alike license 4.0. You have permission to share and redistribute this Bible translation in any format and to make reasonable revisions and adaptations of this translation, provided that: You include the above copyright and source information. If you make any changes to the text, you must indicate that you did so in a way that makes it clear that the original licensor is not necessarily endorsing your changes. If you redistribute this text, you must distribute your contributions under the same license as the original. Pictures included with Scriptures and other documents on this site are licensed just for use with those Scriptures and documents. For other uses, please contact the respective copyright owners. Note that in addition to the rules above, revising and adapting God's Word involves a great responsibility to be true to God's Word. See Revelation 22:18-19. 2020-06-19
Source: http://ebible.org/hauulb/ · eBible.org