2 Thessalonians 2
Litafi Mai-tsarki · Tap a verse to see its cross-references.
1Yanzu game da zuwan Ubangijinmu Yesu Almasihu da taruwarmu domin kasancewa tare da shi; muna rokonku yan'uwa, 2kada kuyi saurin damuwa ko ku gigice saboda wani ruhu ko kuma sako ko kuma wasika da ta yi kamar daga wurin mu, da ke cewa ranar zuwan Ubangiji ta rigaya ta zo. 3Kada wani ya yaudare ku ta kowace hanya. Domin wannan rana baza ta zo ba sai fandarewar nan ta zo kuma an bayyana mutumin tawayen nan wato dan hallaka. 4Wannan shi ne wanda ya ke gaba, yana kuma daukaka kansa fiye da duk abin da ake kira Allah ko kuma ake bautawa. Sakamakon haka yana zama a kursiyin Allah har ma yana cewa shine Allah. 5Baku tuna ba lokacin da nake tare daku na gaya maku wadannan abubuwa? 6Yanzu kun san abinda ke tsaida shi, domin a bayyana shi a lokacin da ya dace. 7Ko yanzu asirin take shari'a ya na aiki, sai dai a kwai wanda ke tsaida shi yanzu har sai an dauke shi. 8Sa'anan za'a bayyana dan tawayen, wanda Ubangiji Yesu zai hallaka shi da numfashin bakinsa. Ubangiji zai mayar da shi ba kome ba ta wurin bayyanuwar zuwansa. 9Mai tawayen nan kuwa, zai zo ne bisa ga aikin shaidan da dukan iko, alamu, da al'ajiban karya, 10da kuma dukan yaudara ta rashin adalci. Wadannan abubuwa za su zama ga wadanda suke hallaka, saboda ba su karbi kaunar gaskiya ba domin su sami ceto. 11Saboda wannan dalilin Allah ya aiko masu da sabani, saboda su yarda da karya. 12Sakamakon shine dukkan su za'a yi masu shari'a, wato wadanda ba su yarda da gaskiya ba suna kuma jin dadin rashin adalci. 13Amma muna masu godiya kulluyaumin ga Allah domin ku, yan'uwa wadanda Ubangiji yake kauna. Ubangiji ya zabe ku a matsayin yayan fari don ceto cikin tsarkakewar Ruhu da gaskatawa da gaskiya. 14Wannan shine abinda ya kira ku gare shi ta wurin bishararmu domin ku sami daukakar Ubangijinmu Yesu Almasihu. 15Saboda haka yan'uwa, ku tsaya da gaske. Ku rike al'adun da aka koya maku, ko ta kalma ko kuma ta wasikarmu. 16Yanzu bari Ubangiji Yesu Almasihu da kansa, da Allah Ubanmu wanda ya kaunace mu ya ba mu madawwamiyar ta'aziya da gabagadi mai kyau domin gaba ta wurin alheri, 17ya ta'azantar da ku ya kuma gina zuciyarku cikin kowane aiki mai kyau da kalma.

Did you know?
The Day of the Lord Has Not Yet Come
- The chapter urges readers not to be easily alarmed by a spirit, a message, or a letter that only seems to come from the authors and claims that the Day of the Lord has already come. It says that day will not arrive until the rebellion occurs and the man of lawlessness is revealed.Sources: the Bible text itself
- Called also the son of destruction, he is described as exalting himself above every so-called god, seating himself in the temple of God, and proclaiming himself to be God. The passage refers to what now restrains him, and to the one who restrains, but it does not name that restraint.Sources: the Bible text itself
- The coming of the lawless one is accompanied by the working of Satan, with every kind of power, sign, and false wonder. Satan means adversary or accuser; in the New Testament the name is used interchangeably with Diabolos, the devil, more than thirty times.Sources: the Bible text itself · Satan
Notes written with AI assistance from open sources (Theographic Bible Metadata, CC BY-SA 4.0; Easton’s Bible Dictionary, public domain) and reviewed before publishing.
Credits and license for this translation
Litafi Mai-tsarki The New Testament in the Hausa language of Nigeria copyright © 2020 Door43 World Missions Community Language: Hausa Translation by: Alakirawa, Bayan, Chrispher Ishaya, Dabere, Dacuhus Timothy Danjuma, Danjay, Danjuma Alfred H, Euang Hediza Naohammed, Franklyn Ukazu Udochukwu, Gideon, Gokop, Habibu, James, Kiash Dachung Butus, Lazarus, Nadaki M. Philip, Nenching, Paul, Rebecca, Rev. Ayuba Taiba, Rev. Cain Yusuf Daniel, Rev. Dalhatu Dambo Ayuba, Rev. Dr. Tambanya Yahaya, Rev. Dr. Yakubu Hassan, Rev. Hannatu Samuel Ndberhukwu, Rev. Ibrahim Kassim, Rev. M. Dan'Amarya, Rev. Yakuba Ayuba Contributor: Dacuhus Timothy Danjuma, Euang Hediza Naohammed, Kiash Dachung Butus, Nadaki M. Philip, Rev. Ayuba Taiba, Rev. Cain Yusuf Daniel, Rev. Dalhatu Dambo Ayuba, Rev. Dr. Tambanya Yahaya, Rev. Dr. Yakubu Hassan, Rev. Hannatu Samuel Ndberhukwu, Rev. Ibrahim Kassim, Rev. M. Dan'Amarya, Rev. Yakuba Ayuba This translation is made available to you under the terms of the Creative Commons Attribution Share-Alike license 4.0. You have permission to share and redistribute this Bible translation in any format and to make reasonable revisions and adaptations of this translation, provided that: You include the above copyright and source information. If you make any changes to the text, you must indicate that you did so in a way that makes it clear that the original licensor is not necessarily endorsing your changes. If you redistribute this text, you must distribute your contributions under the same license as the original. Pictures included with Scriptures and other documents on this site are licensed just for use with those Scriptures and documents. For other uses, please contact the respective copyright owners. Note that in addition to the rules above, revising and adapting God's Word involves a great responsibility to be true to God's Word. See Revelation 22:18-19. 2020-06-19
Source: http://ebible.org/hauulb/ · eBible.org