Nations Bible

2 Corinthians 9

Litafi Mai-tsarki · Tap a verse to see its cross-references.

1Game da hidima domin tsarkaka, ya dace in rubuta maku. 2Na san marmarinku, wanda na yi fahariya da shi a gaban mutanen Makidoniya. Na gaya masu Akaya sun riga sun shirya tun bara. Kwazon ku ya sa yawancin su sun shiga aiki. 3To na aiko maku da 'yan'uwa saboda kada fahariyarmu akanku ta zama a banza, domin kuma ku zauna a shirye, kamar yadda na ce za ku yi. 4Idan kuwa ba haka ba, idan wani cikin makidoniyawa ya biyoni kuma ya tarar da baku shirya ba, za mu ji kunya-ba ni cewa komai game da ku-domin ina da gabagadi a kan ku. 5Sai na ga ya dace in turo 'yan'uwa su zo wurin ku kafin lokaci yayi suyi shirye shirye game da gudummuwar da kuka yi alkawari. Wannan ya zama haka ne domin a shirya shi a matsayin bayarwar albarka, ba wani abin kwace ba. 6Batun shine: wanda ya shuka kadan zai girbi kadan, wanda kuma ya shuka da manufar albarka zai girbi albarka 7Bari kowa ya bayar bisa ga yadda ya yi niyya a zuciyarsa. Kada ya bayar da bacin rai ko kamar dole. Gama Allah yana kaunar mai bayarwa da dadin rai. 8Allah na da ikon ya sa kowace albarka ta ribanbanya domin ku, domin, a koyaushe, a cikin dukan abubuwa, ku sami duk abinda kuke bukata. Hakan zai kasance domin ku ribabbanya kowanne kyakkyawan aiki. 9Kamar yadda aka rubuta, ''Ya rarraba arzikinsa, ya bada shi ga matalauta. Adalcinsa ya dawwama har abada.'' 10Shi wanda ke bayar da iri ga mai shuka da gurasa domin abinci, zai bayar ya kuma ribabbanya maku iri domin shuka. Zai sa girbin adalcinku ya karu. 11Za ku wadata ta kowace hanya domin ku zama masu bayarwa, wannan kuwa zai sa a yi wa Allah godiya ta wurin mu. 12Aiwatar da wannan hidima ba biyan bukatun tsarkaka kawai take yi ba. Tana kuma ribanbanya zuwa ayyuka masu yawa na bada godiya ga Allah. 13Domin an gwada ku an tabbatar da ku akan wannan hidima, za ku kuma daukaka Allah ta wurin biyayyar ku ga shaidar bisharar Almasihu. Za ku kuma daukaka Allah ta wurin yalwar bayarwarku gare su da kowa duka. 14Suna marmarin ganin ku, suna kuma yi maku addu'a. Suna yin haka saboda alherin Allah mai girma da ke bisan ku. 15Godiya ga Allah domin kyautarsa wadda ta fi gaban bayyanawa.

Artistic illustration — an interpretation, not a historical record.

Did you know?

Generosity between Achaia and Macedonia

  • Macedonia was a Roman province lying north of Greece, and Achaia was the other of the two provinces into which the Romans divided Greece, applying that name to the whole Peloponnesus and the south. Writing to believers in Achaia, Paul says he has been boasting to the Macedonians that they were ready to give.Sources: Macedonia · Achaia · the Bible text itself
  • Paul says that since the previous year the people of Achaia had been ready to give, and that their zeal had stirred most of the Macedonians to do the same. He is sending the brothers ahead so that his boast about them will not prove empty if any Macedonians come with him and find them unprepared.Sources: the Bible text itself
  • The name Achaia originally referred to a narrow strip of territory in Greece, northwest of the Peloponnesus. In the New Testament the name is always used in the later, wider sense that the Romans gave it, for the southern province as a whole.Sources: Achaia

Notes written with AI assistance from open sources (Theographic Bible Metadata, CC BY-SA 4.0; Easton’s Bible Dictionary, public domain) and reviewed before publishing.

Places in this chapter

  • Jerusalem · 31.777, 35.234 · verses 1, 12
  • Achaia · 38.720, 22.540 · verse 2
  • Macedonia · 41.600, 22.540 · verses 2, 4

Only places identified with high confidence are shown (90% or more according to the scholarly sources compiled by OpenBible). Period map: DARE (Digital Atlas of the Roman Empire), CC BY 4.0; modern map: © OpenStreetMap contributors; places: OpenBible.info (CC BY 4.0).

Credits and license for this translation
Litafi Mai-tsarki
The New Testament in the Hausa language of Nigeria
copyright © 2020 Door43 World Missions Community
Language: Hausa
Translation by: Alakirawa, Bayan, Chrispher Ishaya, Dabere, Dacuhus Timothy Danjuma, Danjay, Danjuma Alfred H, Euang Hediza Naohammed, Franklyn Ukazu Udochukwu, Gideon, Gokop, Habibu, James, Kiash Dachung Butus, Lazarus, Nadaki M. Philip, Nenching, Paul, Rebecca, Rev. Ayuba Taiba, Rev. Cain Yusuf Daniel, Rev. Dalhatu Dambo Ayuba, Rev. Dr. Tambanya Yahaya, Rev. Dr. Yakubu Hassan, Rev. Hannatu Samuel Ndberhukwu, Rev. Ibrahim Kassim, Rev. M. Dan'Amarya, Rev. Yakuba Ayuba
Contributor: Dacuhus Timothy Danjuma, Euang Hediza Naohammed, Kiash Dachung Butus, Nadaki M. Philip, Rev. Ayuba Taiba, Rev. Cain Yusuf Daniel, Rev. Dalhatu Dambo Ayuba, Rev. Dr. Tambanya Yahaya, Rev. Dr. Yakubu Hassan, Rev. Hannatu Samuel Ndberhukwu, Rev. Ibrahim Kassim, Rev. M. Dan'Amarya, Rev. Yakuba Ayuba
This translation is made available to you under the terms of the
Creative Commons Attribution Share-Alike license 4.0.
You have permission to share and redistribute this Bible translation in any format and to make reasonable revisions and adaptations of this translation, provided that:
You include the above copyright and source information.
If you make any changes to the text, you must indicate that you did so in a way that makes it clear that the original licensor is not necessarily endorsing your changes.
If you redistribute this text, you must distribute your contributions under the same license as the original.
Pictures included with Scriptures and other documents on this site are licensed just for use with those Scriptures and documents.
For other uses, please contact the respective copyright owners.
Note that in addition to the rules above, revising and adapting God's Word involves a great responsibility to be true to God's Word. See Revelation 22:18-19.
2020-06-19

Source: http://ebible.org/hauulb/ · eBible.org

Talk to us

Tell us where you read from, how the Bible has helped you, or what we could improve. We read every message.