2 Corinthians 6
Litafi Mai-tsarki · Tap a verse to see its cross-references.
1haka, tundashike muna aiki tare, na roke ku kar ku yi watsi da alherin Allah. 2Domin ya ce, “A lokacin alheri na saurare ku, kuma a ranar ceto na agaje ku.” Yanzu ne fa, lokacin alheri. Duba, yanzu ne ranar ceto. 3Ba mu sa sanadin faduwa a gaban kowannen ku, domin ba mu so hidimarmu ta zama marar amfani. 4Maimakon haka, mun tabbatar da kan mu ta wurin dukan ayyukanmu, cewa mu bayin Allah ne. Mu bayinsa ne ta wurin yawan jimiri, azaba, kunci, wahala, 5duka, kurkuku, tarzoma, cikin aiki tukuru, cikin rashin barci yawancin dare, cikin yunwa, 6cikin tsarki, ilimi, hakuri, kirki, cikin Ruhu Mai tsarki, da sahihiyar kauna. 7Mu bayinsa ne cikin kalmar gaskiya, cikin ikon Allah. Muna kuma da makamai na adalci, a hanun dama da hagu. 8Muna aiki cikin daraja da rashin daraja, kushe da yabo. Ana zargin mu a kan mu mayaudara ne, duk da haka mu masu gaskiya ne. 9Muna aiki kamar ba a san mu ba, gashi kuwa mu sanannu ne. Muna aiki kamar masu mutuwa-duba! -har yanzu muna raye. Muna aiki kamar wadanda aka hukunta, amma ba hukuncin kisa ba. 10Muna aiki kamar muna bakinciki, amma a koyaushe muna farinciki. Muna aiki kamar matalauta, amma muna azurta mutane dayawa. Muna aiki kamar ba mu da komai, amma mun mallaki komai. 11Mun fada maku dukan gaskiyar, Korantiyawa, kuma zuciyar mu a bude ta ke. 12Ba mu kange zukatan ku ba, ku ne kuka kange zukatanku a gare mu. 13Yanzu a sabanin haka-Ina magana da ku kamar yara-ku bude mana zukatanku. 14Kada ku yi cudanya da marasa bangaskiya. Wace tarayya ke tsakanin adalci da take shari'a? Ko kuma wace zumunta ce ke tsakanin haske da duhu? 15Wace yarjejeniya ke tsakanin Almasihu da Ibilis? ko kuma me ya hada masu bangaskiya da marasa bangaskiya? 16ko wace yarjejeniya ce a tsakanin haikalin Allah da gumaka? Domin kuwa mu haikali ne na Allah mai rai, kamar yadda Allah ya ce: ''Zan zauna a cikin su, in kuma yi tafiya a tsakanin su. Zan zama Allahnsu, su kuma za su zama mutanena.” 17Sabili da haka, ''Ku fito daga cikin su, kuma ku zama kebabbu,'' in ji Ubangiji. ''Kada ku taba kazamin abu, zan kuma karbe ku. 18Zan zama Uba a gare ku, ku kuma za ku zama 'ya'ya maza da mata a gare ni,'' in ji Ubangiji Mai iko duka.

Did you know?
Open Hearts in the Day of Salvation
- The chapter urges its hearers not to receive God’s grace in vain. It quotes God as saying that he heard them in a time of favor and helped them in a day of salvation, then applies those words at once: now is the time of favor, and now is the day of salvation.Sources: the Bible text itself
- The speakers commend themselves as servants of God through great endurance in troubles, hardships, and calamities, in beatings, imprisonments, and riots, and in labor, sleepless nights, and hunger, as well as in purity, knowledge, patience, kindness, the Holy Spirit, and sincere love. They also speak of weapons of righteousness in the right hand and in the left, and of sharp contrasts: dying, yet living on; punished, yet not killed; poor, yet making many rich; having nothing, yet possessing everything.Sources: the Bible text itself
- They speak freely to the Corinthians, saying that their own hearts are open wide while the Corinthians’ affection is restrained, and, as a fair exchange, they ask them, as children, to open their hearts also. They warn them not to be unequally yoked with unbelievers, contrasting righteousness with wickedness, light with darkness, Christ with Belial, a believer with an unbeliever, and the temple of God with idols. The chapter says that we are the temple of the living God, and it includes the Lord’s call to come out from among them, be separate, and touch no unclean thing.Sources: the Bible text itself
Notes written with AI assistance from open sources (Theographic Bible Metadata, CC BY-SA 4.0; Easton’s Bible Dictionary, public domain) and reviewed before publishing.
Credits and license for this translation
Litafi Mai-tsarki The New Testament in the Hausa language of Nigeria copyright © 2020 Door43 World Missions Community Language: Hausa Translation by: Alakirawa, Bayan, Chrispher Ishaya, Dabere, Dacuhus Timothy Danjuma, Danjay, Danjuma Alfred H, Euang Hediza Naohammed, Franklyn Ukazu Udochukwu, Gideon, Gokop, Habibu, James, Kiash Dachung Butus, Lazarus, Nadaki M. Philip, Nenching, Paul, Rebecca, Rev. Ayuba Taiba, Rev. Cain Yusuf Daniel, Rev. Dalhatu Dambo Ayuba, Rev. Dr. Tambanya Yahaya, Rev. Dr. Yakubu Hassan, Rev. Hannatu Samuel Ndberhukwu, Rev. Ibrahim Kassim, Rev. M. Dan'Amarya, Rev. Yakuba Ayuba Contributor: Dacuhus Timothy Danjuma, Euang Hediza Naohammed, Kiash Dachung Butus, Nadaki M. Philip, Rev. Ayuba Taiba, Rev. Cain Yusuf Daniel, Rev. Dalhatu Dambo Ayuba, Rev. Dr. Tambanya Yahaya, Rev. Dr. Yakubu Hassan, Rev. Hannatu Samuel Ndberhukwu, Rev. Ibrahim Kassim, Rev. M. Dan'Amarya, Rev. Yakuba Ayuba This translation is made available to you under the terms of the Creative Commons Attribution Share-Alike license 4.0. You have permission to share and redistribute this Bible translation in any format and to make reasonable revisions and adaptations of this translation, provided that: You include the above copyright and source information. If you make any changes to the text, you must indicate that you did so in a way that makes it clear that the original licensor is not necessarily endorsing your changes. If you redistribute this text, you must distribute your contributions under the same license as the original. Pictures included with Scriptures and other documents on this site are licensed just for use with those Scriptures and documents. For other uses, please contact the respective copyright owners. Note that in addition to the rules above, revising and adapting God's Word involves a great responsibility to be true to God's Word. See Revelation 22:18-19. 2020-06-19
Source: http://ebible.org/hauulb/ · eBible.org