Nations Bible

1 Corinthians 6

Litafi Mai-tsarki · Tap a verse to see its cross-references.

1Idan wani a cikin ku yana jayayya da wani, to sai ya tafi kotu gaban alkali marar bada gaskiya, a maimakon gaban masu bi? 2Ko ba ku sani ba, masubi ne za su yiwa duniya shari'a? Kuma idan ku za ku yi wa duniya shari'a, sai ku kasa sasanta al'amura marasa mahimmanci? 3Baku sani ba mu za mu yiwa mala'iku shari'a? Balle shari'ar al'amuran wannan rai? 4Idan kuna shar'anta al'amuran yau da kullum, don me ku ke kai irin wadannan matsaloli gaban wadanda ba 'yan ikilisiya ba? 5Na fadi wannan domin ku kunyata. Babu wani mai hikima a cikin ku ko daya da zai iya sasanta gardama a tsakanin 'yan'uwa? 6Amma kamar yadda yake, mai bi ya na kai karar mai bi a kotu, kuma a gaban mai shari'a wanda ba mai bi ba! 7Kasancewar rashin jituwa a tsakanin Kirista na nuna cewa kun rigaya kun gaza. Don me ba za ka shanye laifi ba? Don me ba za ka yarda a kware ka ba? 8Amma kun yi wa wadansu laifi kun kuma cutar su, su kuwa 'yan'uwanku ne! 9Ba ku sani ba marasa adalci ba za su gaji Mulkin Allah ba? Kada ku gaskata karya. Da fasikai, da masu bautar gumaka, da mazinata, da karuwai maza, da masu ludu, 10da barayi, da masu zari, da mashaya, da masu zage-zage, da 'yan damfara - ba waninsu da zai gaji Mulkin Allah. 11Kuma da haka wadansu a cikinku suke, amma an tsarkake ku, an mika ku ga Allah, an maida tsayuwar ku dai-dai a gaban Allah a cikin sunan Ubangji Yesu Almasihu, kuma ta wurin Ruhun Allahnmu. 12Dukkan abu halal ne a gare ni”, amma ba kowanne abu ne mai amfani ba. “Dukan abu halal ne a gare ni,” amma ba zan yarda wani abu ya mallake ni ba. 13“Abinci don ciki ne, kuma ciki don abinci ne”, amma Allah za ya kawar da su duka. Ba a yi jiki saboda fasikanci ba. Maimakon haka, jiki don Ubangiji ne, kuma Ubangiji zai yi wa jiki tanaji. 14Allah ya tada Ubangiji, kuma za ya tashe mu ta wurin ikonsa. 15Ba ku sani ba jikunanku gabobi ne na Almasihu? Na dauki gabobin Almasihu in hada su da karuwa? Allah ya sawwake! 16Ko baku sani ba dukan wanda yake hade da karuwa, ya zama jiki daya da ita kenan? 17Kamar yadda Littafi ya fadi, “Su biyun za su zama nama daya.” Amma wanda yake hade da Ubangiji ya zama ruhu daya da shi kenan. 18Ku gujewa fasikanci! Kowane zunubi mutum yake aikatawa a waje da jikinsa yake, amma mutum mai fasikanci yana zunubi gaba da jikinsa. 19Ba ku sani ba jikinku haikali ne na Ruhu Mai-tsarki, wanda yake zaune a cikinku, wanda ku ka samu daga wurin Allah? Ba ku sani ba cewa ku ba na kanku ba ne? 20An saye ku da tsada. Don haka, ku daukaka Allah da jikin ku.

Artistic illustration — an interpretation, not a historical record.

Did you know?

Lawsuits, the Kingdom, and the Body

  • The chapter challenges believers who take a grievance against another to law before the unrighteous instead of before the saints. It argues that people who will judge the world, and even angels, should be able to judge trivial everyday cases, and it treats a lawsuit between brothers—especially before unbelievers—as a defeat already suffered.Sources: the Bible text itself
  • It warns that the wicked will not inherit the kingdom of God, naming the sexually immoral, idolaters, adulterers, men who submit to or perform homosexual acts, thieves, the greedy, drunkards, verbal abusers, and swindlers. It then says that some of the readers once were such people, but were washed, sanctified, and justified in the name of the Lord Jesus Christ and by the Spirit of our God.Sources: the Bible text itself
  • Quoted claims—“Everything is permissible for me” and “Food for the stomach and the stomach for food”—are answered with limits: not everything is beneficial, and the body is for the Lord, not for sexual immorality. Uniting with a prostitute is said to make two people one flesh, while uniting with the Lord is one spirit with him; the body is called a temple of the Holy Spirit, and the readers are told they were bought at a price.Sources: the Bible text itself

Notes written with AI assistance from open sources (Theographic Bible Metadata, CC BY-SA 4.0; Easton’s Bible Dictionary, public domain) and reviewed before publishing.

Credits and license for this translation
Litafi Mai-tsarki
The New Testament in the Hausa language of Nigeria
copyright © 2020 Door43 World Missions Community
Language: Hausa
Translation by: Alakirawa, Bayan, Chrispher Ishaya, Dabere, Dacuhus Timothy Danjuma, Danjay, Danjuma Alfred H, Euang Hediza Naohammed, Franklyn Ukazu Udochukwu, Gideon, Gokop, Habibu, James, Kiash Dachung Butus, Lazarus, Nadaki M. Philip, Nenching, Paul, Rebecca, Rev. Ayuba Taiba, Rev. Cain Yusuf Daniel, Rev. Dalhatu Dambo Ayuba, Rev. Dr. Tambanya Yahaya, Rev. Dr. Yakubu Hassan, Rev. Hannatu Samuel Ndberhukwu, Rev. Ibrahim Kassim, Rev. M. Dan'Amarya, Rev. Yakuba Ayuba
Contributor: Dacuhus Timothy Danjuma, Euang Hediza Naohammed, Kiash Dachung Butus, Nadaki M. Philip, Rev. Ayuba Taiba, Rev. Cain Yusuf Daniel, Rev. Dalhatu Dambo Ayuba, Rev. Dr. Tambanya Yahaya, Rev. Dr. Yakubu Hassan, Rev. Hannatu Samuel Ndberhukwu, Rev. Ibrahim Kassim, Rev. M. Dan'Amarya, Rev. Yakuba Ayuba
This translation is made available to you under the terms of the
Creative Commons Attribution Share-Alike license 4.0.
You have permission to share and redistribute this Bible translation in any format and to make reasonable revisions and adaptations of this translation, provided that:
You include the above copyright and source information.
If you make any changes to the text, you must indicate that you did so in a way that makes it clear that the original licensor is not necessarily endorsing your changes.
If you redistribute this text, you must distribute your contributions under the same license as the original.
Pictures included with Scriptures and other documents on this site are licensed just for use with those Scriptures and documents.
For other uses, please contact the respective copyright owners.
Note that in addition to the rules above, revising and adapting God's Word involves a great responsibility to be true to God's Word. See Revelation 22:18-19.
2020-06-19

Source: http://ebible.org/hauulb/ · eBible.org

Talk to us

Tell us where you read from, how the Bible has helped you, or what we could improve. We read every message.