Nations Bible

1 Corinthians 16

Litafi Mai-tsarki · Tap a verse to see its cross-references.

1Yanzu game da zancen tattara gudunmuwa ga masu bi, kamar yadda na umurci ikilisiyun Galatiya, haka za ku yi. 2A ranar farko ga mako, kowannen ku ya ajiye wani abu, yana tarawa bisa ga iyawarku. Ku yi haka don in na zo ba sai an tattara ba. 3Sa'adda na zo, zan aiki duk wadanda kuka yarda da su da wasiku don su kai sakonku Urushalima. 4Sannan idan ya dace nima in tafi, sai su tafi tare da ni. 5Zan zo wurinku sa'adda na ratsa Makidoniya. Domin zan ratsa ta makidoniya. 6Meyuwa in jima a wurinku, har ma in yi damuna, domin ku taimaka mani game da tafiyata, duk inda za ni. 7Gama ba na so in yi maku gani na gajeren lokaci. Don ina so in dau lokaci tare da ku, idan Ubangiji ya yarda. 8Amma zan tsaya Afisus har ranar Fentikos. 9Gama an bude mani kofa mai fadi, kuma akwai magabta da yawa. 10Sa'adda Timoti ya zo, ku tabbata ya sami sakewa acikinku, tun da aikin Ubangiji yake yi kamar yadda nake yi. 11Kada fa kowa ya rena shi. Ku tabbata kun sallame shi lafiya, domin ya komo gare ni, don ina duban hanyarsa tare da yan'uwa. 12Game da zancen dan'uwanmu Afollos kuwa, na karfafa shi ya ziyarce ku tare da 'yan'uwa. Sai dai baya sha'awar zuwa yanzu. Amma zai zo sa'adda lokaci ya yi. 13Ku zauna a fadake, ku tsaya daram cikin bangaskiya, kuna nuna halin maza, ku yi karfin hali. 14Bari dukan abinda kuke yi ayi shi cikin kauna. 15Kun dai sani iyalin gidan Sitefanas su suka fara tuba a Akaya, kuma sun bada kansu ga yi wa masu bi hidima. Yanzu ina rokonku, 'yan'uwa, 16kuyi biyayya da irin wadannan mutane da duk wanda ke taimakawa a cikin aikin, yana kuma fama tare da mu. 17Na yi farinciki da zuwan Sitefanas, da Fartunatas, da Akaikas. Sun debe mini kewarku. 18Gama sun wartsakar da ruhuna da naku kuma. Don haka, Sai ku kula da irin wadannan mutane. 19Ikilisiyoyin kasar Asiya suna gaishe ku. Akila da Bilkisu, tare da ikilisiyar da take taruwa a gidansu, suna gaishe ku cikin Ubangiji. 20Dukan 'yan'uwa masu bi na gaishe ku. Ku gaida juna da sumba maitsarki. 21Ni Bulus, nake rubuta wannnan da hannuna. 22Duk wanda ba ya kaunar Ubangiji bari ya zama la'ananne. Ubangijinmu, Ka zo! 23Alherin Ubangiji Yesu ya kasance tare da ku. 24Bari kaunata ta kasance tare da ku duka a cikin Almasihu Yesu. [ Amin ].

Artistic illustration — an interpretation, not a historical record.

Did you know?

The collection, the journey, and closing greetings

  • Paul tells the Corinthians to lay aside a portion of their income on the first day of every week for the saints, as he had directed the churches of Galatia, so that no collection would be needed when he came. Galatia, in Asia Minor, was home to people of Celtic origin whom Roman writers called Gauls. The gift was to go to Jerusalem with messengers the church recommended, while Paul would arrive only after passing through Macedonia, a Roman province north of Greece, and might spend the winter with them.Sources: the Bible text itself
  • Paul says he will remain in Ephesus until Pentecost, because a great door for effective work has opened to him even though many oppose him. The churches of the province of Asia send greetings; that Asia was proconsular Asia, a Roman province in western Asia Minor, and Ephesus was its capital. Aquila, a tent-maker from Pontus, and his wife Priscilla—called Prisca in this greeting—had accompanied Paul from Corinth to Ephesus and remained there, and the church that meets in their house greets the Corinthians as well.Sources: the Bible text itself
  • Stephanas and his household were the first converts in Achaia—the Roman province covering the Peloponnesus and southern Greece—and had devoted themselves to the service of the saints. Easton's Bible Dictionary (1897) says that Achaicus, together with Fortunatus and Stephanas, visited Paul at Ephesus to consult him about the church's affairs, and that the three probably brought the Corinthians' letter to the apostle. The same dictionary places Apollos with Paul at Ephesus when this letter was written; Paul strongly urged him to go to Corinth with the brothers, but he was unwilling to go then and would come when he had an opportunity.Sources: the Bible text itself

Notes written with AI assistance from open sources (Theographic Bible Metadata, CC BY-SA 4.0; Easton’s Bible Dictionary, public domain) and reviewed before publishing.

Places in this chapter

  • Galatia · 39.267, 32.983 · verse 1
  • Jerusalem · 31.777, 35.234 · verses 1, 3
  • Macedonia · 41.600, 22.540 · verse 5
  • Ephesus · 37.939, 27.341 · verse 8
  • Achaia · 38.720, 22.540 · verse 15
  • Asia · 38.400, 28.300 · verse 19

Only places identified with high confidence are shown (90% or more according to the scholarly sources compiled by OpenBible). Period map: DARE (Digital Atlas of the Roman Empire), CC BY 4.0; modern map: © OpenStreetMap contributors; places: OpenBible.info (CC BY 4.0).

Credits and license for this translation
Litafi Mai-tsarki
The New Testament in the Hausa language of Nigeria
copyright © 2020 Door43 World Missions Community
Language: Hausa
Translation by: Alakirawa, Bayan, Chrispher Ishaya, Dabere, Dacuhus Timothy Danjuma, Danjay, Danjuma Alfred H, Euang Hediza Naohammed, Franklyn Ukazu Udochukwu, Gideon, Gokop, Habibu, James, Kiash Dachung Butus, Lazarus, Nadaki M. Philip, Nenching, Paul, Rebecca, Rev. Ayuba Taiba, Rev. Cain Yusuf Daniel, Rev. Dalhatu Dambo Ayuba, Rev. Dr. Tambanya Yahaya, Rev. Dr. Yakubu Hassan, Rev. Hannatu Samuel Ndberhukwu, Rev. Ibrahim Kassim, Rev. M. Dan'Amarya, Rev. Yakuba Ayuba
Contributor: Dacuhus Timothy Danjuma, Euang Hediza Naohammed, Kiash Dachung Butus, Nadaki M. Philip, Rev. Ayuba Taiba, Rev. Cain Yusuf Daniel, Rev. Dalhatu Dambo Ayuba, Rev. Dr. Tambanya Yahaya, Rev. Dr. Yakubu Hassan, Rev. Hannatu Samuel Ndberhukwu, Rev. Ibrahim Kassim, Rev. M. Dan'Amarya, Rev. Yakuba Ayuba
This translation is made available to you under the terms of the
Creative Commons Attribution Share-Alike license 4.0.
You have permission to share and redistribute this Bible translation in any format and to make reasonable revisions and adaptations of this translation, provided that:
You include the above copyright and source information.
If you make any changes to the text, you must indicate that you did so in a way that makes it clear that the original licensor is not necessarily endorsing your changes.
If you redistribute this text, you must distribute your contributions under the same license as the original.
Pictures included with Scriptures and other documents on this site are licensed just for use with those Scriptures and documents.
For other uses, please contact the respective copyright owners.
Note that in addition to the rules above, revising and adapting God's Word involves a great responsibility to be true to God's Word. See Revelation 22:18-19.
2020-06-19

Source: http://ebible.org/hauulb/ · eBible.org

Talk to us

Tell us where you read from, how the Bible has helped you, or what we could improve. We read every message.