Nations Bible

Numbers 23

Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ · Tap a verse to see its cross-references.

Maganar Bala’am ta farko na abin da Allah ya faɗa

1Bala’am ya ce, “Ka gina mini bagadai bakwai a nan, ka shirya mini bijimai bakwai da raguna bakwai.” 2Balak ya yi yadda Bala’am ya faɗa, sai su biyu suka miƙa bijimi da rago a kan kowane bagade.

3Sa’an nan Bala’am ya ce wa Balak, “Tsaya nan kusa da hadayarka, ni kuwa in koma wani wurin da yake a kaɗaice. Wataƙila Ubangiji zai sadu da ni. Duk abin da ya bayyana mini, zan faɗa maka.” Sai ya haura kan wani wurin da yake a kaɗaice a tudun.

4Allah kuwa ya sadu da Bala’am. Bala’am ya ce, “Na shirya bagadai bakwai, na kuma miƙa bijimi guda da rago guda, a kan kowane bagade.”

5Ubangiji ya ba wa Bala’am saƙo ya ce, “Ka koma wurin Balak, ka faɗa masa wannan saƙo.”

6Saboda haka, sai Bala’am ya koma wurin Balak ya same shi tsaye a kusa da hadayarsa, tare da dukan dattawan Mowab. 7Sai Bala’am ya furta abin da Allah ya faɗa masa ya ce,

“Balak ya kawo ni daga Aram,

sarkin Mowab ya kawo ni daga gabashin duwatsu.

Ya ce, ‘Zo, ka la’anta mini Yaƙub;

zo, ka tsine Isra’ila.’

8Yaya zan iya la’anta

waɗanda Allah bai la’anta ba?

Yaya zan tsine

waɗanda Ubangiji bai tsine ba?

9Daga kan duwatsu na gan su,

daga bisa kan tuddai na hange su.

Na ga mutane da suke zaune su kaɗai

ba sa ɗauki kansu ɗaya da al’ummai ba.

10Wa zai iya ƙidaya ƙurar Yaƙub

ko yă ƙidaya kashi ɗaya bisa huɗu na Isra’ila?

Bari in mutu, mutuwar adali

ƙarshena kuma yă zama kamar nasu!”

11Balak ya ce wa Bala’am, “Me ke nan ka yi mini? Na kawo ka, ka la’anta abokan gābana, sai ga shi albarka kake sa musu!”

12Bala’am ya ce, “Ba dole in faɗa abin da Ubangiji ya sa a bakina ba?”

Maganar Bala’am ta biyu na abin da Ubangiji ya faɗa

13Sa’an nan Balak ya ce masa, “Zo, mu tafi wani wuri inda za ka gan su; a nan kana ganin sashe ne kawai, ba dukansu ba. Daga can kuwa, ka la’anta mini su.” 14Saboda haka ya ɗauke shi zuwa filin Zofim a ƙwanƙolin Fisga, a can ya gina bagadai bakwai, ya kuma miƙa bijimi da rago a kan kowane bagade.

15Bala’am ya ce wa Balak, “Tsaya nan kusa da hadayarka, ni kuwa in je in sadu da Ubangiji a can.”

16Ubangiji ya sadu da Bala’am, ya kuma ba shi saƙo ya ce, “Koma wurin Balak ka ba shi wannan saƙo.”

17Saboda haka ya tafi ya same Balak tsaye a kusa da hadayarsa, tare da dattawan Mowab. Balak ya tambaye Bala’am ya ce, “Mene ne Ubangiji ya ce?”

18Sai Bala’am ya furta saƙon da aka ba shi ya ce,

“Tashi, Balak, ka saurara;

ka kasa kunne gare ni, ɗan Ziffor.

19Allah ba mutum ba ne, da zai yi ƙarya,

shi ba ɗan mutum ba ne, da zai canja tunaninsa.

Yana maganar abin da ba zai iya aikata ba ne?

Yakan kuma yi alkawarin da ba zai iya cikawa ba?

20Na karɓi umarni in sa albarka;

na kuwa sa albarka, ba zan iya janye ta ba.

21“Bai ga mugunta a cikin Yaƙub ba,

bai kuma ga wahala a Isra’ila ba.

Ubangiji Allahnsu yana tare da su;

sowar Sarki yana cikinsu.

22Allah ya fitar da su daga Masar;

suna da ƙarfi iri na kutunkun ɓauna.

23Ba wata maitar da za tă ci Yaƙub,

ba sihiri da zai cuci Isra’ila.

Yanzu za a ce game da Yaƙub

da Isra’ila, ‘Duba abin da Allah ya yi!’

24Mutane sun tashi kamar ƙaƙƙarfar zakanya;

sun tā da kansu kamar zaki

wanda ba ya hutawa

sai ya cinye naman abin da ya kama

ya kuma sha jinin abin da ya kama.”

25Sai Balak ya ce wa Bala’am, “Kada ka la’anta su, kada kuma ka sa musu albarka!”

26Bala’am amsa ya ce, “Ban faɗa maka zan yi kaɗai abin da Ubangiji ya ce ba?”

Maganar Bala’am ta uku na abin da Ubangiji ya faɗa

27Sai Balak ya ce wa Bala’am, “Zo in kai ka wani wuri. Wataƙila zai gamshi Allah, yă bari ka la’anta mini su daga can.” 28Balak kuwa ya ɗauki Bala’am zuwa ƙwanƙolin Feyor, wanda yake fuskantar hamada.

29Bala’am ya ce, “Ka gina mini bagadai bakwai a nan, ka kuma shirya mini bijimai bakwai da raguna bakwai.” 30Balak ya yi yadda Bala’am ya ce, ya kuwa miƙa bijimi da rago a kan kowane bagade.

Did you know?

Balaam's Oracles of Blessing

  • In his first oracle, Balaam mentions that Balak brought him from Aram in the eastern mountains. According to biblical tradition, Balaam was from Mesopotamia and held a widespread reputation for invoking powerful blessings and curses.Sources: the Bible text itself · Balaam · Aram
  • Seeking a favorable outcome, King Balak led Balaam to different vantage points across Moab, including the Field of Zophim on the summit of Pisgah and the peak of Peor overlooking the wilderness, hoping a different view would allow him to curse Israel.Sources: the Bible text itself · Zophim · Pisgah · Peor
  • At each new location, Balaam instructed Balak to construct seven altars and sacrifice seven bulls and seven rams—one bull and one ram on each altar—before stepping aside to receive an oracle from the Lord.Sources: the Bible text itself

Notes written with AI assistance from open sources (Theographic Bible Metadata, CC BY-SA 4.0; Easton’s Bible Dictionary, public domain) and reviewed before publishing.

Places in this chapter

  • Moab · Today: Moab 1 · 31.181, 35.701 · verses 6, 7, 17
  • Aram · 33.511, 36.306 · verse 7
  • East · Today: region around Amman · 31.955, 35.934 · verse 7
  • Egypt · 30.129, 31.308 · verse 22
  • Jeshimon · 31.470, 35.223 · verse 28
  • Peor · Today: within 1 km of Khirbet Ayun Musa · 31.777, 35.738 · verse 28

Only places identified with high confidence are shown (90% or more according to the scholarly sources compiled by OpenBible). Period map: DARE (Digital Atlas of the Roman Empire), CC BY 4.0; modern map: © OpenStreetMap contributors; places: OpenBible.info (CC BY 4.0).

Credits and license for this translation
Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™
Hausa: Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ (Bible) of Nigeria
copyright © 2009, 2020 Biblica, Inc.
Language: Hausa
Contributor: Biblica, Inc.
An sami wannan aiki a sauƙaƙe a ƙarƙashin lasisin Ƙasa da ƙasa na Lasisin Creative Commons Attribution-ShareAlike 4.0 na Ƙasa da ƙasa (CC BY-SA). Don a ga kwafin wannan lasisi, a ziyarci: http://creativecommons.org/licenses/by-sa/4.0 ko kuma a aika ta wasiƙa zuwa ga Creative Commons, PO Box 1866, Mountain View, CA 94042, USA.
“Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista ta hannun Biblica, Inc., kuma yin amfani da tambarin Biblica® na bukata rubutaccen izinin Biblica, Inc. A ƙarƙashin sharaɗin lasisin CC BY-SA, za ka iya kwafa ka kuma sāke raba wannan aikin da ba a gyaggyara ba muddin ba ka taɓa tambarin nan na Biblica® ba. Idan ka gyara wani kwafi ko ka juya wannan aiki, ta wurin kirkiro da aikin da aka samu, dole ne ka ka cire tambarin Biblica®. A aikin da aka samo, dole ne ka nuna canje-canjen da ka yi, ka kuma nuna aikin haka: “Ainihi aikin ta hannun Biblica, Inc. yana nan kyauta a www.biblica.com da buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki.”
Dole sharaɗin neman izini ya fita a kan kan magana ko kuma a shafi neman izinin aiki kamar haka:
Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™
Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc.
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™
Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc.
“Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini.
“Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission.
Dole kuma a samo aikin da ka yi daga ainihin aikin a ƙarƙashin wannan lasisi (CC BY-SA).
Idan za ka so ka sanar da Biblica, Inc. dangane da juyinka na wannan aiki, sai ka tuntuɓe mu a https://open.bible/contact-us.
This work is made available under the Creative Commons Attribution-ShareAlike 4‪.0 International License (CC BY-SA). To view a copy of this license, visit http://creativecommons.org/licenses/by-sa/4‪.0 or send a letter to Creative Commons, PO Box 1866, Mountain View, CA 94042, USA.
Biblica® is a trademark registered by Biblica, Inc., and use of the Biblica® trademark requires the written permission of Biblica, Inc. Under the terms of the CC BY-SA license, you may copy and redistribute this unmodified work as long as you keep the Biblica® trademark intact. If you modify a copy or translate this work, thereby creating a derivative work, you must remove the Biblica® trademark. On the derivative work, you must indicate what changes you have made and attribute the work as follows: “The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible.”
Notice of copyright must appear on the title or copyright page of the work as follows:
Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™
Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc.
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™
Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc.
“Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini.
“Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission.
You must also make your derivative work available under the same license (CC BY-SA).
If you would like to notify Biblica, Inc. regarding your translation of this work, please contact us at https://open.bible/contact-us.
This translation is made available to you under the terms of the
Creative Commons Attribution Share-Alike license 4.0.
You have permission to share and redistribute this Bible translation in any format and to make reasonable revisions and adaptations of this translation, provided that:
You include the above copyright and source information.
If you make any changes to the text, you must indicate that you did so in a way that makes it clear that the original licensor is not necessarily endorsing your changes.
If you redistribute this text, you must distribute your contributions under the same license as the original.
Pictures included with Scriptures and other documents on this site are licensed just for use with those Scriptures and documents.
For other uses, please contact the respective copyright owners.
Note that in addition to the rules above, revising and adapting God's Word involves a great responsibility to be true to God's Word. See Revelation 22:18-19.
2025-05-03

Source: http://ebible.org/hausa/ · eBible.org

Talk to us

Tell us where you read from, how the Bible has helped you, or what we could improve. We read every message.