Nations Bible

Nehemiah 12

Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ · Tap a verse to see its cross-references.

Firistoci da Lawiyawa

1Waɗannan su ne firistoci da Lawiyawa waɗanda suka komo tare da Zerubbabel ɗan Sheyaltiyel da kuma Yeshuwa.

Serahiya, Irmiya, Ezra,

2Amariya, Malluk, Hattush

3Shekaniya, Rehum, Meremot,

4Iddo, Ginneton, Abiya,

5Miyamin, Mowadiya, Bilga,

6Shemahiya, Yohiyarib, Yedahiya,

7Sallu, Amok, Hilkiya da Yedahiya.

8Lawiyawan su ne Yeshuwa, Binnuyi, Kadmiyel, Sherebiya, Yahuda, da kuma Mattaniya, wanda tare da ’yan’uwansa yake lura da waƙoƙin godiya. 9Bakbukiya da Unni, ’yan’uwansu sun tsaya ɗaura da su a hidimomi.

10Yeshuwa ne mahaifin Yohiyakim,

Yohiyakim shi ne mahaifin Eliyashib,

Eliyashib shi ne mahaifin Yohiyada,

11Yohiyada shi ne mahaifin Yonatan,

Yonatan kuma mahaifin Yadduwa.

12A kwanakin Yohiyakim, waɗannan su ne shugabannin iyalan firistoci,

na iyalin Serahiya, Merahiya;

na iyalin Irmiya, Hananiya;

13na iyalin Ezra, Meshullam;

na iyalin Amariya, Yehohanan;

14na iyalin Malluk, Yonatan;

na iyalin Shebaniya, Yusuf;

15na iyalin Harim, Adna;

na iyalin Merahiyot, Helkai;

16na iyalin Iddo, Zakariya;

na iyalin Ginneton, Meshullam;

17na iyalin Abiya, Zikri;

na iyalin Miniyamin da na Mowadiya, Filtai;

18na iyalin Bilga, Shammuwa;

na iyalin Shemahiya, Yehonatan;

19na iyalin Yohiyarib, Mattenai;

na iyalin Yedahiya, Uzzi;

20na iyalin Sallu, Kallai;

na iyalin Amok, Eber;

21na iyalin Hilkiya, Hashabiya;

na iyalin Yedahiya, Netanel.

22Shugabannin iyalin Lawiyawa a kwanakin Eliyashib, Yohiyada, Yohanan da Yadduwa, da kuma na firistoci, an rubuta su a zamanin mulkin Dariyus mutumin Farisa. 23Shugabannin iyali cikin zuriyar Lawi har zuwa lokacin Yohanan ɗan Eliyashib, an rubuta su a cikin littafin tarihi. 24Shugabannin Lawiyawa kuwa su ne Hashabiya, Sherebiya, Yeshuwa ɗan Kadmiyel, da ’yan’uwansu, waɗanda suka tsaya ɗaura da su don su yi yabo da kuma godiya, sashe ɗaya kan ba da amsa ga ɗaya sashen, kamar yadda Dawuda mutumin Allah ya umarta.

25Mattaniya, Bakbukiya, Obadiya, Meshullam, Talmon da Akkub su ne matsaran ƙofofi waɗanda suka yi tsaron ɗaukan ajiya a ƙofofi. 26Sun yi hidima a kwanakin Yohiyakim ɗan Yeshuwa, ɗan Yozadak, kuma a kwanakin Nehemiya gwamna da kuma na Ezra firist da kuma marubuci.

Keɓewar katangar Urushalima

27A keɓewar katangar Urushalima, an nemi Lawiyawa daga inda suke zama aka kawo su Urushalima don su yi bikin miƙawa da farin ciki da waƙoƙin godiya da kuma kiɗin kuge, garaya da molo. 28Aka kuma tattara mawaƙa su ma daga yankin kewayen Urushalima, daga ƙauyukan Netofawa, 29daga Bet-Gilgal, da kuma daga wuraren Geba da Azmawet, gama mawaƙan sun gina wa kansu ƙauyuka kewaye da Urushalima.

30Sa’ad da firistoci da Lawiyawa suka tsarkake kansu da tsarki, sai suka tsarkake mutane, ƙofofi da kuma katanga.

31Sai na sa shugabannin Yahuda suka haura zuwa bisan katangar. Na kuma sa manyan ƙungiyoyi biyu na mawaƙa su miƙa godiya. Ɗaya ya haura zuwa bisan katangar zuwa dama, wajen Ƙofar Juji. 32Hoshahiya da rabin shugabannin Yahuda kuwa suka bi su, 33tare da Azariya, Ezra, Meshullam, 34Yahuda, Benyamin, Shemahiya, Irmiya, 35da waɗansu firistoci kuma da ƙahoni, da kuma Zakariya ɗan Yonatan, ɗan Shemahiya, ɗan Mattaniya, ɗan Mikahiya, ɗan Zakkur, ɗan Asaf, 36da ’yan’uwansa, Shemahiya, Azarel, Milalai, Gilalai, Ma’ai, Netanel, Yahuda da Hanani, tare da kayan kiɗi da Dawuda mutumin Allah ya umarta. Ezra malamin Doka ya jagoranci jerin gwanon. 37A Ƙofar Maɓuɓɓuga suka ci gaba kai tsaye suka haura matakalan Birnin Dawuda a kan hawa zuwa katangar suka wuce a bisa gidan Dawuda zuwa Ƙofar Ruwa wajen gabas.

38Ƙungiyar mawaƙa ta biyu suka yi jerin gwano a ɗaya gefen. Na bi su a bisan katangar, tare da rabin mutanen, muka wuce Hasumiya Tanderu zuwa Katanga Mai Faɗi, 39bisa Ƙofar Efraim, Ƙofar Yeshana, Ƙofar Kifi, Hasumiyar Hananel da kuma Hasumiya ɗari, har zuwa Ƙofar Tumaki. A Ƙofar Matsara suka tsaya.

40Ƙungiyoyin mawaƙa biyu da suka yi godiya suka ɗauki wurarensu a gidan Allah, haka ma ni, tare da rabin shugabanni, 41da kuma firistoci, Eliyakim, Ma’asehiya, Miniyamin, Mikahiya, Eliyohenai, Zakariya da Hananiya tare da ƙahoninsu, 42haka ma Ma’asehiya, Shemahiya, Eleyazar, Uzzi, Yehohanan, Malkiya, Elam da Ezer. Mawaƙan suka rera waƙoƙi a ƙarƙashin kulawar Yezrahiya. 43A rana ta uku kuma suka miƙa manyan hadayu, suna farin ciki domin Allah ya ba su farin ciki mai girma. Mata da yara suka yi farin ciki su ma. An ji ƙarar farin ciki da ake yi a Urushalima daga nesa.

44A lokacin an naɗa mutane su lura da ɗakunan ajiya don sadakoki, nunan fari da kuma zakka. Daga gonakin garuruwan da suke kewaye za su kawo sassan da Dokar ta umarta zuwa ɗakunan ajiya domin firistoci da Lawiyawa, gama Yahuda ya ji daɗin aikin firistoci da Lawiyawa. 45Sun yi hidimar Allahnsu da kuma hidimar tsarkakewa, kamar yadda mawaƙa da matsaran ƙofofi suka yi, bisa ga umarnin Dawuda da ɗansa Solomon. 46Gama tun dā, a kwanakin Dawuda da Asaf, akwai masu bi da mawaƙa da kuma na waƙoƙin yabo da na godiya ga Allah. 47Saboda haka a kwanakin Zerubbabel da Nehemiya, dukan Isra’ila suka ba da sashe na kowace rana domin mawaƙa da matsaran ƙofofi. Suka kuma keɓe sashe don sauran Lawiyawa, Lawiyawan kuma suka keɓe sashe don zuriyar Haruna.

Artistic illustration — an interpretation, not a historical record.

Did you know?

Dedication of the Wall and Priestly Registers

  • For the dedication of Jerusalem's rebuilt wall, Levites and singers were brought from surrounding settlements where they had built villages, including Beth-gilgal and the fields of Geba and Azmaveth. Musical worship was organized in alternating groups using instruments patterned after the instructions of King David.Sources: the Bible text itself · Beth-gilgal · Geba · Azmaveth
  • The dedication ceremony featured two large thanksgiving choirs marching directly along the top of the newly repaired city walls in opposite directions. One procession was led by Ezra the scribe toward the Dung Gate, while Nehemiah followed the second group, until both choirs met at the house of God.Sources: the Bible text itself · Dung Gate · Gate of the Fountain
  • The chapter preserves ancestral records of priests and Levites spanning from the first return under Zerubbabel and the high priest Jeshua through several generations into the Persian period. These records documented the lineage of high priests and family heads responsible for temple services and gatekeeping.Sources: the Bible text itself · Zerubbabel · Joshua · Eliashib

Notes written with AI assistance from open sources (Theographic Bible Metadata, CC BY-SA 4.0; Easton’s Bible Dictionary, public domain) and reviewed before publishing.

Places in this chapter

  • Jerusalem · 31.777, 35.234 · verses 27, 28, 29, 43
  • Dung Gate · Today: in Jerusalem · 31.777, 35.234 · verse 31
  • City of David · 31.774, 35.236 · verse 37
  • Fountain Gate · Today: in Jerusalem · 31.777, 35.234 · verse 37
  • Water Gate · Today: in Jerusalem · 31.777, 35.234 · verse 37
  • Broad Wall · 31.776, 35.232 · verse 38
  • Tower of the Ovens · Today: in Jerusalem · 31.777, 35.234 · verse 38
  • Ephraim Gate · Today: in Jerusalem · 31.777, 35.234 · verse 39
  • Fish Gate · Today: in Jerusalem · 31.777, 35.234 · verse 39
  • Gate of the Guard · Today: in Jerusalem · 31.777, 35.234 · verse 39
  • Gate of Yeshanah · Today: in Jerusalem · 31.777, 35.234 · verse 39
  • Sheep Gate · Today: in Jerusalem · 31.777, 35.234 · verse 39
  • Tower of Hananel · Today: Antonia Fortress · 31.780, 35.234 · verse 39
  • Tower of the Hundred · Today: within 500 m of the Antonia Fortress · 31.780, 35.234 · verse 39

Only places identified with high confidence are shown (90% or more according to the scholarly sources compiled by OpenBible). Period map: DARE (Digital Atlas of the Roman Empire), CC BY 4.0; modern map: © OpenStreetMap contributors; places: OpenBible.info (CC BY 4.0).

Credits and license for this translation
Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™
Hausa: Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ (Bible) of Nigeria
copyright © 2009, 2020 Biblica, Inc.
Language: Hausa
Contributor: Biblica, Inc.
An sami wannan aiki a sauƙaƙe a ƙarƙashin lasisin Ƙasa da ƙasa na Lasisin Creative Commons Attribution-ShareAlike 4.0 na Ƙasa da ƙasa (CC BY-SA). Don a ga kwafin wannan lasisi, a ziyarci: http://creativecommons.org/licenses/by-sa/4.0 ko kuma a aika ta wasiƙa zuwa ga Creative Commons, PO Box 1866, Mountain View, CA 94042, USA.
“Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista ta hannun Biblica, Inc., kuma yin amfani da tambarin Biblica® na bukata rubutaccen izinin Biblica, Inc. A ƙarƙashin sharaɗin lasisin CC BY-SA, za ka iya kwafa ka kuma sāke raba wannan aikin da ba a gyaggyara ba muddin ba ka taɓa tambarin nan na Biblica® ba. Idan ka gyara wani kwafi ko ka juya wannan aiki, ta wurin kirkiro da aikin da aka samu, dole ne ka ka cire tambarin Biblica®. A aikin da aka samo, dole ne ka nuna canje-canjen da ka yi, ka kuma nuna aikin haka: “Ainihi aikin ta hannun Biblica, Inc. yana nan kyauta a www.biblica.com da buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki.”
Dole sharaɗin neman izini ya fita a kan kan magana ko kuma a shafi neman izinin aiki kamar haka:
Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™
Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc.
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™
Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc.
“Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini.
“Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission.
Dole kuma a samo aikin da ka yi daga ainihin aikin a ƙarƙashin wannan lasisi (CC BY-SA).
Idan za ka so ka sanar da Biblica, Inc. dangane da juyinka na wannan aiki, sai ka tuntuɓe mu a https://open.bible/contact-us.
This work is made available under the Creative Commons Attribution-ShareAlike 4‪.0 International License (CC BY-SA). To view a copy of this license, visit http://creativecommons.org/licenses/by-sa/4‪.0 or send a letter to Creative Commons, PO Box 1866, Mountain View, CA 94042, USA.
Biblica® is a trademark registered by Biblica, Inc., and use of the Biblica® trademark requires the written permission of Biblica, Inc. Under the terms of the CC BY-SA license, you may copy and redistribute this unmodified work as long as you keep the Biblica® trademark intact. If you modify a copy or translate this work, thereby creating a derivative work, you must remove the Biblica® trademark. On the derivative work, you must indicate what changes you have made and attribute the work as follows: “The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible.”
Notice of copyright must appear on the title or copyright page of the work as follows:
Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™
Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc.
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™
Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc.
“Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini.
“Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission.
You must also make your derivative work available under the same license (CC BY-SA).
If you would like to notify Biblica, Inc. regarding your translation of this work, please contact us at https://open.bible/contact-us.
This translation is made available to you under the terms of the
Creative Commons Attribution Share-Alike license 4.0.
You have permission to share and redistribute this Bible translation in any format and to make reasonable revisions and adaptations of this translation, provided that:
You include the above copyright and source information.
If you make any changes to the text, you must indicate that you did so in a way that makes it clear that the original licensor is not necessarily endorsing your changes.
If you redistribute this text, you must distribute your contributions under the same license as the original.
Pictures included with Scriptures and other documents on this site are licensed just for use with those Scriptures and documents.
For other uses, please contact the respective copyright owners.
Note that in addition to the rules above, revising and adapting God's Word involves a great responsibility to be true to God's Word. See Revelation 22:18-19.
2025-05-03

Source: http://ebible.org/hausa/ · eBible.org

Talk to us

Tell us where you read from, how the Bible has helped you, or what we could improve. We read every message.