Nations Bible

Joshua 18

Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ · Tap a verse to see its cross-references.

An raba sauran ƙasar

1Isra’ilawa duka suka taru a Shilo suka kafa tenti inda za su dinga taruwa. Yanzu ƙasar tana ƙarƙashin mulkinsu, 2amma akwai sauran kabilu bakwai na Isra’ila waɗanda ba su samu rabon gādonsu ba tukuna.

3Saboda haka Yoshuwa ya ce wa Isra’ilawa, “Har yaushe za ku yi jinkirin shiga, ku mallaki ƙasar da Ubangiji Allah na iyayenku ya ba ku? 4Ku ba da mutum uku daga kowace kabila, ni kuwa in aike su, su zagaya dukan ƙasar su rubuta bayani game da ita, bisa ga yadda za a raba ta gādo ga kowace kabila, sa’an nan su dawo wurina. 5Za ku raba ƙasar kashi bakwai. Mutanen Yahuda za su ci gaba da kasancewa a wurin da suke a kudu, sai kuma mutanen Yusuf a wurin da suke a arewa. 6Bayan kun auna ƙasar, ku raba ta kashi bakwai, sai ku kawo mini taswirar ƙasar. Ni kuma in yi muku ƙuri’a a gaban Ubangiji Allahnmu. 7Lawiyawa ba su da rabo a cikinku, domin aikin firistocin da suke yi wa Ubangiji shi ne gādonsu. Gad, Ruben da rabin kabilar Manasse kuwa sun riga sun samu gādonsu a gabashin gefen Urdun, Musa bawan Ubangiji ya ba su.”

8Da mutanen za su kama hanya su je su zāna yadda ƙasar take, Yoshuwa ya umarce su cewa, “Ku je ku ga yadda ƙasar take. Sa’an nan ku dawo wurina, zan yi muku ƙuri’a a nan Shilo a gaban Ubangiji.” 9Mutanen kuwa suka tafi suka bi ta cikin ƙasar, suka bayyana yadda take a rubuce, gari-gari, kashi bakwai, suka koma wurin Yoshuwa a Shilo.

10Sai Yoshuwa ya yi musu ƙuri’a a gaban Ubangiji, a nan ne ya raba wa Isra’ilawa ƙasar bisa ga yadda aka raba su kabila-kabila.

Rabon da kabilar Benyamin ta samu

11Ƙuri’ar kabilar Benyamin bisa ga iyalansu. Rabonsu ya kama daga ƙasar da take tsakanin kabilar Yahuda da ta Yusuf.

12Daga gefen arewa, iyakarsu ta kama ne daga Urdun, ta wuce arewa a gangaren Yeriko, ta nufi yamma cikin ƙasar kan tudu, ta fito a jejin Bet-Awen. 13Daga can ta ƙetare zuwa gangaren Luz a kudu (wato, Betel), ta wuce zuwa Atarot Adda a tudun arewa na kwarin Bet-Horon.

14Daga tudun da yake fuskantar Bet-Horon a kudu, iyakar ta juya kudu ta gefen yamma ta ɓullo a Kiriyat Ba’al (wato, Kiriyat Yeyarim), birnin Yahuda. Wannan ita ce iyakar a wajen yamma.

15A gefen kudu kuwa, iyakar ta fara daga ƙauyukan Kiriyat Yeyarim wajen yamma sai ta miƙe zuwa maɓuɓɓugar ruwan Neftowa. 16Iyakar ta gangara zuwa gefen dutsen da yake fuskantar Kwarin Ben Hinnom, wanda yake arewa da Kwarin Refayim. Ta ci gaba ta gangara ta Kwarin Hinnom ta yi kudu kusa da birnin Yebusiyawa har zuwa En Rogel. 17Sai ta nausa ta yi wajen arewa, zuwa En Shemesh, ta ci gaba zuwa Gelilot, wanda yake fuskantar hawan Adummim. Daga can ta gangara zuwa Dutsen Bohan, ɗan Ruben. 18Sai ta wuce ta yi arewancin gangaren Bet-Araba, ta wuce har zuwa cikin Araba. 19Sa’an nan ta wuce zuwa arewancin gangaren Bet-Hogla ta kuma ɓulla a arewancin gaɓar Tekun Gishiri, a bakin Urdun a kudu. Wannan ita ce iyakar a wajen kudu.

20Urdun shi ne iyaka a wajen gabas.

21Waɗannan su ne garuruwan da kabilar Benyamin suke da su na gādo.

Yeriko, Bet-Hogla, Emek Keziz, 22Bet-Araba, Zemarayim, Betel, 23Awwim, Fara, Ofra, 24Kefar Ammoni, Ofni da Geba, garuruwa goma sha biyu ke nan da ƙauyukansu.

25Akwai kuma Gibeyon, Rama, Beyerot, 26Mizfa Kefira, Moza, 27Rekem, Irfeyel, Tarala, 28Zela, Hayelef, birnin Yebusiyawa (wato, Urushalima), Gibeya da Kiriyat, garuruwa goma sha huɗu ke nan da ƙauyukansu.

Artistic illustration — an interpretation, not a historical record.

Did you know?

Assembly at Shiloh and Benjamin's Allotment

  • The assembly of Israel established the Tent of Meeting at Shiloh, a city in Ephraim north of Bethel. This made Shiloh the central place of worship and the staging ground for distributing the remaining land to the tribes.Sources: the Bible text itself · Shiloh
  • To divide the territory among the seven remaining tribes, Joshua sent three men from each tribe to walk the land and record a detailed description of seven portions. Joshua then cast lots in the presence of the LORD at Shiloh to assign each allotment.Sources: the Bible text itself
  • The first lot among the seven tribes fell to Benjamin, situated between the territories of Judah to the south and the house of Joseph to the north. This compact allotment included prominent cities such as Jericho, Bethel, and Jebus (Jerusalem).Sources: the Bible text itself · Benjamin (patriarch)

Notes written with AI assistance from open sources (Theographic Bible Metadata, CC BY-SA 4.0; Easton’s Bible Dictionary, public domain) and reviewed before publishing.

Places in this chapter

  • Shiloh · Today: Khirbet Seilun · 32.056, 35.290 · verses 1, 8, 9, 10
  • Jordan · Today: Jordan River · 31.761, 35.558 · verses 7, 12, 19, 20
  • Jericho · Today: Tell es Sultan · 31.872, 35.445 · verses 12, 21
  • Lower Beth-horon · Today: Beit Ur al Tahta · 31.895, 35.084 · verse 13
  • Luz · Today: Beitin · 31.923, 35.241 · verse 13
  • Beth-horon · Today: Beit Ur al Tahta · 31.895, 35.084 · verse 14
  • Kiriath-jearim · Today: Deir el Azar · 31.809, 35.104 · verses 14, 15, 28
  • Valley of Hinnom · Today: Hinnom Valley · 31.769, 35.228 · verse 16
  • Valley of Rephaim · 31.763, 35.219 · verse 16
  • Adummim · 31.817, 35.362 · verse 17
  • Arabah · 30.417, 35.151 · verse 18
  • Salt Sea · Today: Dead Sea · 31.500, 35.500 · verse 19
  • Gibeon · Today: El Jib · 31.847, 35.183 · verse 25
  • Mizpeh · Today: Tell en Nasbeh · 31.885, 35.216 · verse 26
  • Jerusalem · 31.777, 35.234 · verse 28

Only places identified with high confidence are shown (90% or more according to the scholarly sources compiled by OpenBible). Period map: DARE (Digital Atlas of the Roman Empire), CC BY 4.0; modern map: © OpenStreetMap contributors; places: OpenBible.info (CC BY 4.0).

Credits and license for this translation
Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™
Hausa: Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ (Bible) of Nigeria
copyright © 2009, 2020 Biblica, Inc.
Language: Hausa
Contributor: Biblica, Inc.
An sami wannan aiki a sauƙaƙe a ƙarƙashin lasisin Ƙasa da ƙasa na Lasisin Creative Commons Attribution-ShareAlike 4.0 na Ƙasa da ƙasa (CC BY-SA). Don a ga kwafin wannan lasisi, a ziyarci: http://creativecommons.org/licenses/by-sa/4.0 ko kuma a aika ta wasiƙa zuwa ga Creative Commons, PO Box 1866, Mountain View, CA 94042, USA.
“Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista ta hannun Biblica, Inc., kuma yin amfani da tambarin Biblica® na bukata rubutaccen izinin Biblica, Inc. A ƙarƙashin sharaɗin lasisin CC BY-SA, za ka iya kwafa ka kuma sāke raba wannan aikin da ba a gyaggyara ba muddin ba ka taɓa tambarin nan na Biblica® ba. Idan ka gyara wani kwafi ko ka juya wannan aiki, ta wurin kirkiro da aikin da aka samu, dole ne ka ka cire tambarin Biblica®. A aikin da aka samo, dole ne ka nuna canje-canjen da ka yi, ka kuma nuna aikin haka: “Ainihi aikin ta hannun Biblica, Inc. yana nan kyauta a www.biblica.com da buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki.”
Dole sharaɗin neman izini ya fita a kan kan magana ko kuma a shafi neman izinin aiki kamar haka:
Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™
Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc.
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™
Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc.
“Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini.
“Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission.
Dole kuma a samo aikin da ka yi daga ainihin aikin a ƙarƙashin wannan lasisi (CC BY-SA).
Idan za ka so ka sanar da Biblica, Inc. dangane da juyinka na wannan aiki, sai ka tuntuɓe mu a https://open.bible/contact-us.
This work is made available under the Creative Commons Attribution-ShareAlike 4‪.0 International License (CC BY-SA). To view a copy of this license, visit http://creativecommons.org/licenses/by-sa/4‪.0 or send a letter to Creative Commons, PO Box 1866, Mountain View, CA 94042, USA.
Biblica® is a trademark registered by Biblica, Inc., and use of the Biblica® trademark requires the written permission of Biblica, Inc. Under the terms of the CC BY-SA license, you may copy and redistribute this unmodified work as long as you keep the Biblica® trademark intact. If you modify a copy or translate this work, thereby creating a derivative work, you must remove the Biblica® trademark. On the derivative work, you must indicate what changes you have made and attribute the work as follows: “The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible.”
Notice of copyright must appear on the title or copyright page of the work as follows:
Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™
Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc.
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™
Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc.
“Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini.
“Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission.
You must also make your derivative work available under the same license (CC BY-SA).
If you would like to notify Biblica, Inc. regarding your translation of this work, please contact us at https://open.bible/contact-us.
This translation is made available to you under the terms of the
Creative Commons Attribution Share-Alike license 4.0.
You have permission to share and redistribute this Bible translation in any format and to make reasonable revisions and adaptations of this translation, provided that:
You include the above copyright and source information.
If you make any changes to the text, you must indicate that you did so in a way that makes it clear that the original licensor is not necessarily endorsing your changes.
If you redistribute this text, you must distribute your contributions under the same license as the original.
Pictures included with Scriptures and other documents on this site are licensed just for use with those Scriptures and documents.
For other uses, please contact the respective copyright owners.
Note that in addition to the rules above, revising and adapting God's Word involves a great responsibility to be true to God's Word. See Revelation 22:18-19.
2025-05-03

Source: http://ebible.org/hausa/ · eBible.org

Talk to us

Tell us where you read from, how the Bible has helped you, or what we could improve. We read every message.