Nations Bible

Jeremiah 31

Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ · Tap a verse to see its cross-references.

1“A lokacin nan, zan zama Allah na dukan kabilan Isra’ila, za su kuma zama mutanena,” in ji Ubangiji.

2Ga abin da Ubangiji yana cewa,

“Mutanen da suka tsere wa takobi

za su sami tagomashi a hamada;

zan zo don in ba da hutu ga Isra’ila.”

3Ubangiji ya bayyana mana a dā, yana cewa,

“Na ƙaunace ku da madawwamiyar ƙauna;

na janye ku da ƙauna marar iyaka.

4Zan sāke gina ki

za ki kuwa sāke ginuwa, ya Budurwar Isra’ila.

Za ki kuma ɗauki ganganki

ki fita don ki yi rawa da masu farin ciki.

5Za ki sāke dasa gonakin inabi

a kan tussan Samariya;

manoma za su yi shuka a kansu

su kuma ji daɗin amfaninsu.

6Za a yi ranar da matsara za su tā da murya

a kan tuddan Efraim su ce,

‘Ku zo, bari mu haura Sihiyona,

zuwa wurin Ubangiji Allahnmu.’ ”

7Ga abin da Ubangiji yana cewa,

“Ku rera don farin ciki wa Yaƙub;

ku yi sowa don al’ummai da suke nesa.

Ka sa a ji yabanku, ku kuma ce,

‘Ya Ubangiji ka ceci mutanenka,

raguwar Isra’ila.’

8Ga shi, zan kawo su daga ƙasar arewa

in tattara su daga iyakar duniya.

A cikinsu makafi da guragu za su kasance,

mata masu ciki da matan da suke naƙuda;

jama’a mai yawan gaske za su komo.

9Za su zo da kuka;

za su yi addu’a yayinda nake komo da su.

Zan bishe su kusa da rafuffukan ruwa

a miƙaƙƙiyar hanya inda ba za su yi tuntuɓe ba,

domin ni ne mahaifin Isra’ila,

Efraim kuma ɗan farina ne.

10“Ku ji maganar Ubangiji, ya al’ummai;

ku yi shelarta a gaban teku masu nesa cewa,

‘Shi wanda ya watsar da Isra’ila zai tattara su

zai kuma lura da garkensa kamar makiyayi.’

11Gama Ubangiji zai fanshi Yaƙub

zai cece su daga hannun waɗanda suka fi su ƙarfi.

12Za su zo su yi sowa don farin ciki a ƙwanƙolin Sihiyona;

za su yi farin ciki cikin yalwar Ubangiji

hatsi, sabon ruwan inabi da mai,

’ya’yan garken tumaki da na shanu.

Za su zama kamar gonar da aka yi wa banruwa,

ba za su ƙara yin baƙin ciki ba.

13’Yan mata za su yi rawa su kuma yi murna,

haka ma samari da tsofaffi.

Zan mai da makokinsu farin ciki;

zan ta’azantar da su in kuma sa su yi farin ciki a maimakon baƙin ciki.

14Zan ƙosar da firistoci da yalwa,

mutanena kuma za su cika da yalwa,”

in ji Ubangiji.

15Ga abin da Ubangiji yana cewa,

“An ji murya daga Rama,

makoki da kuka mai zafi,

Rahila tana kuka domin ’ya’yanta

ta kuma ƙi a ta’azantar da ita

domin ’ya’yanta ba su.”

16Ga abin da Ubangiji yana cewa,

“Hana muryarki kuka

da kuma idanunki hawaye,

gama za a sāka wa aikinki,”

in ji Ubangiji.

“Za su komo daga ƙasar abokin gāba.

17Saboda haka akwai sa zuciya domin nan gaba,”

in ji Ubangiji.

“’Ya’yanki za su komo ƙasarsu.

18“Tabbatacce na ji gurnanin Efraim yana cewa,

‘Ka hore ni kamar ɗan maraƙi mai ƙin ji,

na kuwa horu.

Ka mayar da ni, zan kuwa dawo,

domin kai ne Ubangiji Allahna.

19Bayan na kauce,

sai na tuba;

bayan na gane,

sai na sunkuyar da kaina.

Na ji kunya da ƙasƙanci

domin ina ɗauke da kunyar ƙuruciyata.’

20Efraim ba ƙaunataccen ɗana ba ne,

ɗan da nake jin daɗinsa?

Ko da yake sau da dama ina maganar gāba a kansa,

duk da haka nakan tuna da shi.

Saboda haka zuciyata tana marmarinsa;

ina da jinƙai mai girma dominsa,”

in ji Ubangiji.

21“Ki kafa alamun hanya;

ki sa shaidun bishewa.

Ki lura da babbar hanya da kyau,

hanyar da kika bi.

Ki komo, ya Budurwar Isra’ila,

ki komo zuwa garuruwanki.

22Har yaushe za ki yi ta yawo,

Ya ’ya marar aminci?

Ubangiji zai ƙirƙiro sabon abu a duniya

mace za tă kewaye namiji.”

23Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki, Allah na Isra’ila yana cewa, “Sa’ad da na komo da su daga bauta mutane a ƙasar Yahuda da cikin garuruwanta za su sāke yi amfani da waɗannan kalmomi. ‘ Ubangiji ya albarkace ka, ya mazauni mai adalci, ya tsarkakan dutse.’ 24Mutane za su zauna tare a Yahuda da dukan garuruwansa, manoma da waɗanda suke yawo da garkunansu. 25Zan wartsake waɗanda suka gaji in kuma ƙosar da waɗanda ransu ya yi yaushi.”

26A kan wannan na farka na duba kewaye. Barcina ya yi mini daɗi.

27“Kwanaki suna zuwa,” in ji Ubangiji, “sa’ad da zan kafa gidan Isra’ila da gidan Yahuda da ’ya’yan mutane da na dabbobi. 28Kamar yadda na lura da su don su tumɓuke su kuma rusar, su lalatar, su hallaka su kuma kawo masifa, haka zan lura da su don su gina su kuma dasa,” in ji Ubangiji. 29“A waɗannan kwanaki mutane ba za su ƙara ce,

“ ‘Ubanni suka ci ’ya’yan inabi masu tsami,

haƙoran ’ya’ya suka mutu ba.’

30A maimako, kowa zai mutu saboda zunubinsa; duk wanda ya ci ’ya’yan inabi masu tsami, haƙoransa ne za su mutu.

31“Lokaci yana zuwa,” in ji Ubangiji,

“sa’ad da zan yi sabon alkawari

da gidan Isra’ila

da kuma gidan Yahuda.

32Ba zai zama kamar alkawarin

da na yi da kakanni kakanninsu ba

sa’ad da na kama su da hannu

na bishe su daga Masar,

domin sun take alkawarina,

ko da yake na zama miji a gare su,”

in ji Ubangiji.

33“Ga alkawarin da zan yi da gidan Isra’ila

bayan wannan lokaci,” in ji Ubangiji.

“Zan sa dokata a tunaninsu

in kuma rubuta ta a zukatansu.

Zan zama Allahnsu,

za su kuma zama mutanena.

34Mutum ba zai ƙara koya wa maƙwabci ba,

ko ya koya wa ɗan’uwansa cewa, ‘Ka san Ubangiji,’

domin duk za su san ni,

daga ƙaraminsu har zuwa babba,”

in ji Ubangiji.

“Gama zan gafarta muguntarsu

ba zan kuwa ƙara tuna da zunubansu ba.”

35Ga abin da Ubangiji yana cewa,

shi da ya kafa rana

don tă yi haske a yini

shi da ya sa wata da taurari

su yi haske da dare,

shi da yake dama teku

don raƙuman ruwansa su yi ruri

Ubangiji Maɗaukaki ne sunansa.

36“In dai wannan kafaffiyar ƙa’ida ta daina aiki a gabana,”

in ji Ubangiji,

“to, sai zuriyar Isra’ila ta daina

zama al’umma a gabana.”

37Ga abin da Ubangiji yana cewa,

“In a iya auna sammai

a kuma bincike tushen duniya a ƙarƙas

to, sai in ƙi dukan zuriyar Isra’ila ke nan

saboda dukan abin da suka yi,”

in ji Ubangiji.

38“Kwanaki suna zuwa,” in ji Ubangiji, “sa’ad da za a sāke gina wannan birni domina daga Hasumiyar Hananel zuwa Ƙofar Kusurwa. 39Ma’auni zai miƙe daga can ya nausa kai tsaye zuwa tudun Gareb sa’an nan ya juya zuwa Gowa. 40Dukan kwarin da ake zubar da toka da kuma gawawwaki, da dukan lambatun da suke can har zuwa Kwarin Kidron a gabas zuwa kusurwar Ƙofar Doki, za su zama mai tsarki ga Ubangiji. Ba za a ƙara tumɓuke birnin ko a rushe shi ba.”

Did you know?

Restoration and the New Covenant

  • In Jeremiah 31:15, Rachel, the ancestral mother of Joseph and Benjamin whose tomb is near Bethlehem, is portrayed as weeping in Ramah for her lost children. Ramah was a city in Benjamin where captives of Jerusalem, including Jeremiah himself, were later assembled following the Babylonian conquest.Sources: the Bible text itself · Rachel · Ramah
  • Although Ephraim was Joseph's younger son, he received the preeminent right-hand blessing from his grandfather Jacob. In this chapter, God tenderly refers to Ephraim as his firstborn and a delightful child, promising mercy and return to the scattered people.Sources: the Bible text itself · Ephraim · Jacob (Israel)
  • This chapter introduces the promise of a new covenant, contrasting it with the covenant made when God led their ancestors out of Egypt. Instead of outward instruction alone, this covenant describes God placing his law directly into their minds and inscribing it upon their hearts.Sources: the Bible text itself · Egypt

Notes written with AI assistance from open sources (Theographic Bible Metadata, CC BY-SA 4.0; Easton’s Bible Dictionary, public domain) and reviewed before publishing.

Places in this chapter

  • Samaria · 32.276, 35.195 · verse 5
  • Mount Ephraim · 31.923, 35.241 · verse 6
  • Zion · Today: Jerusalem · 31.777, 35.234 · verses 6, 12
  • Jerusalem · 31.777, 35.234 · verses 23, 38
  • Egypt · 30.129, 31.308 · verse 32
  • Corner Gate · Today: in Jerusalem · 31.777, 35.234 · verse 38
  • Tower of Hananel · Today: Antonia Fortress · 31.780, 35.234 · verse 38
  • Gareb · Today: in Jerusalem · 31.777, 35.234 · verse 39
  • Goah · Today: within 8 km of Jerusalem · 31.777, 35.234 · verse 39
  • Horse Gate · Today: in Jerusalem · 31.777, 35.234 · verse 40
  • Kidron · Today: Kidron River · 31.780, 35.240 · verse 40

Only places identified with high confidence are shown (90% or more according to the scholarly sources compiled by OpenBible). Period map: DARE (Digital Atlas of the Roman Empire), CC BY 4.0; modern map: © OpenStreetMap contributors; places: OpenBible.info (CC BY 4.0).

Credits and license for this translation
Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™
Hausa: Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ (Bible) of Nigeria
copyright © 2009, 2020 Biblica, Inc.
Language: Hausa
Contributor: Biblica, Inc.
An sami wannan aiki a sauƙaƙe a ƙarƙashin lasisin Ƙasa da ƙasa na Lasisin Creative Commons Attribution-ShareAlike 4.0 na Ƙasa da ƙasa (CC BY-SA). Don a ga kwafin wannan lasisi, a ziyarci: http://creativecommons.org/licenses/by-sa/4.0 ko kuma a aika ta wasiƙa zuwa ga Creative Commons, PO Box 1866, Mountain View, CA 94042, USA.
“Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista ta hannun Biblica, Inc., kuma yin amfani da tambarin Biblica® na bukata rubutaccen izinin Biblica, Inc. A ƙarƙashin sharaɗin lasisin CC BY-SA, za ka iya kwafa ka kuma sāke raba wannan aikin da ba a gyaggyara ba muddin ba ka taɓa tambarin nan na Biblica® ba. Idan ka gyara wani kwafi ko ka juya wannan aiki, ta wurin kirkiro da aikin da aka samu, dole ne ka ka cire tambarin Biblica®. A aikin da aka samo, dole ne ka nuna canje-canjen da ka yi, ka kuma nuna aikin haka: “Ainihi aikin ta hannun Biblica, Inc. yana nan kyauta a www.biblica.com da buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki.”
Dole sharaɗin neman izini ya fita a kan kan magana ko kuma a shafi neman izinin aiki kamar haka:
Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™
Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc.
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™
Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc.
“Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini.
“Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission.
Dole kuma a samo aikin da ka yi daga ainihin aikin a ƙarƙashin wannan lasisi (CC BY-SA).
Idan za ka so ka sanar da Biblica, Inc. dangane da juyinka na wannan aiki, sai ka tuntuɓe mu a https://open.bible/contact-us.
This work is made available under the Creative Commons Attribution-ShareAlike 4‪.0 International License (CC BY-SA). To view a copy of this license, visit http://creativecommons.org/licenses/by-sa/4‪.0 or send a letter to Creative Commons, PO Box 1866, Mountain View, CA 94042, USA.
Biblica® is a trademark registered by Biblica, Inc., and use of the Biblica® trademark requires the written permission of Biblica, Inc. Under the terms of the CC BY-SA license, you may copy and redistribute this unmodified work as long as you keep the Biblica® trademark intact. If you modify a copy or translate this work, thereby creating a derivative work, you must remove the Biblica® trademark. On the derivative work, you must indicate what changes you have made and attribute the work as follows: “The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible.”
Notice of copyright must appear on the title or copyright page of the work as follows:
Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™
Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc.
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™
Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc.
“Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini.
“Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission.
You must also make your derivative work available under the same license (CC BY-SA).
If you would like to notify Biblica, Inc. regarding your translation of this work, please contact us at https://open.bible/contact-us.
This translation is made available to you under the terms of the
Creative Commons Attribution Share-Alike license 4.0.
You have permission to share and redistribute this Bible translation in any format and to make reasonable revisions and adaptations of this translation, provided that:
You include the above copyright and source information.
If you make any changes to the text, you must indicate that you did so in a way that makes it clear that the original licensor is not necessarily endorsing your changes.
If you redistribute this text, you must distribute your contributions under the same license as the original.
Pictures included with Scriptures and other documents on this site are licensed just for use with those Scriptures and documents.
For other uses, please contact the respective copyright owners.
Note that in addition to the rules above, revising and adapting God's Word involves a great responsibility to be true to God's Word. See Revelation 22:18-19.
2025-05-03

Source: http://ebible.org/hausa/ · eBible.org

Talk to us

Tell us where you read from, how the Bible has helped you, or what we could improve. We read every message.