Jeremiah 3
Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ · Tap a verse to see its cross-references.
1“In mutum ya saki matarsa
ta kuwa bar shi ta auri wani mutum,
zai iya komo da ita kuma?
Ƙasar ba za tă ƙazantu gaba ɗaya ba?
Amma kun yi rayuwa kamar karuwa da masoya masu yawa
yanzu za ki komo wurina?”
In ji Ubangiji.
2“Ta da idanu ki duba tsaunuka ki gani.
Akwai wani wurin da ba a kwana da ke ba?
A gefen hanya kin zauna kina jiran masoyanki,
kin zauna kamar makiyayi a hamada.
Kin ƙazantar da ƙasar
da karuwancinki da muguntarki.
3Saboda haka an hana yayyafi,
kuma babu ruwan bazara da ya sauka.
Duk da haka kina da irin kallon da karuwa takan yi;
kin ƙi ki ji kunya.
4Yanzu ba kin kira ni,
‘Mahaifina, abokina daga ƙuruciyata ba,
5kullum za ka riƙa fushi?
Hasalarka za tă ci gaba har abada ne?’
Haka kike magana,
amma kina aikata dukan muguntar da kika iya yi.”
Isra’ila marar aminci
6A zamanin Sarki Yosiya, Ubangiji ya ce mini, “Ka ga abin da marar amincin nan, Isra’ila ta yi? Ta haura kan kowane tudu mai tsayi da kowane gindin itace mai duhuwa ta yi zina a can. 7Na yi zaton bayan ta yi wannan duka, za tă komo wurina amma ba tă yi haka ba, ’yar’uwarta marar aminci nan Yahuda ta gani. 8Na ba wa Isra’ila marar bangaskiya takardar saki na kuwa kore ta saboda duk zinanta. Duk da haka na ga cewa ’yar’uwarta marar amincin nan Yahuda ba ta da tsoro; ita ma ta fita ta yi zina. 9Domin fasikancin Isra’ila bai yi tasiri gare ta ba, sai ta ƙazantar da ƙasar ta kuma yi zina da dutse da kuma itace. 10Duk da wannan duka, Yahuda ’yar’uwarta rashin amincin ba tă komo gare ni da dukan zuciyarta ba, sai a munafunce,” in ji Ubangiji.
11Ubangiji ya ce mini, “Isra’ila marar bangaskiya ta fi Yahuda marar aminci. 12Ka tafi, ka yi shelar saƙon nan wajen arewa cewa,
“ ‘Ki komo, Isra’ila marar bangaskiya,’ in ji Ubangiji,
‘Ba zan ƙara yin fushi da ke ba,
gama ni mai jinƙai ne,’ in ji Ubangiji,
‘Ba zan yi fushi da ke har abada ba.
13Ki dai yarda da laifinki
kin yi wa Ubangiji Allahnki tawaye,
kin watsar da alheranki ga baƙin alloli
a ƙarƙashin kowane itace mai duhuwa,
ba ki kuwa yi mini biyayya ba,’ ”
in ji Ubangiji.
14“Ku komo, ku mutane marasa bangaskiya,” in ji Ubangiji, “gama ni ne mijinku. Zan ɗauke ku, ɗaya daga garuruwanku da kuma biyu daga zuriyarku in kawo ku a Sihiyona. 15Sa’an nan zan ba ku makiyaya da suke yin abin da zuciyata take so, waɗanda za su bishe ku da sani da kuma fahimi. 16A kwanakin, sa’ad da kuka ƙaru sosai a ƙasar,” in ji Ubangiji, “mutane ba za su ƙara yin magana a kan, ‘Akwatin alkawarin Ubangiji ba.’ Ba zai ƙara shiga zuciyarsu ko su tuna ba; ko su bukace shi, ko kuwa su yi wani irinsa ba. 17A lokacin za su ce da Urushalima Kursiyin Ubangiji, kuma dukan al’ummai za su taru a Urushalima don su girmama sunan Ubangiji. Ba za su ƙara bin taurinkai zuciyarsu mai mugunta ba. 18A kwanakin gidan Yahuda zai haɗu da gidan Isra’ila, tare kuma za su zo daga ƙasar da take wajen arewa zuwa ƙasar da na ba kakanninsu gādo.
19“Ni kaina na faɗa,
“ ‘Da farin ciki zan ɗauke ki kamar ’ya’yana maza
in ba ki ƙasa mai daɗi,
gādo mafi kyau da wata al’umma.’
Na zaci za ki kira ni ‘Mahaifi’
ba za ki ƙara rabuwa da bina ba.
20Amma kamar mace marar aminci ga mijinta,
haka kika kasance marar aminci gare ni, ya gidan Isra’ila,”
in ji Ubangiji.
21An ji kuka a filayen tuddai,
kuka da roƙon mutanen Isra’ila,
domin sun lalace hanyoyinsu
sun kuma manta da Ubangiji Allahnsu.
22“Ku komo, mutane marasa bangaskiya;
zan warkar da ku daga ja da bayanku.”
“I, za mu zo wurinka,
gama kai ne Ubangiji Allahnmu.
23Tabbatacce hayaniyar bin gumaka a kan tuddai
da duwatsu banza ne;
tabbatacce a wurin Ubangiji Allahnmu ne
akwai ceton Isra’ila.
24Daga ƙuruciyarmu allolin kunya sun cinye mu
amfanin wahalar kakanninmu
garkunan tumakinsu da na awakinsu,
yaransu maza da mata.
25Bari mu kwanta mu sha kunya,
bari kuma kunyarmu ta rufe mu.
Mun yi wa Ubangiji Allahnmu zunubi,
da mu da kakanninmu;
daga ƙuruciyarmu har yă zuwa yau
ba mu yi wa Ubangiji Allahnmu biyayya ba.”

Did you know?
A Call to Faithless Sisters to Return
- During the reign of King Josiah of Judah, Jeremiah received prophecies comparing the northern kingdom of Israel and the southern kingdom of Judah to two sisters. Although the northern kingdom had already been sent away for its idolatry, Judah failed to learn from her sister's fate and turned back only in pretense.Sources: the Bible text itself · Josiah
- The prophet foretells a future restoration where the scattered people are brought back to Zion, the historic hill of Jerusalem. In that day, Jerusalem itself would be recognized as the Throne of the LORD, and the ark of the covenant would no longer be remembered or rebuilt.Sources: the Bible text itself · Zion · Jerusalem
- Drawing upon ancient marriage and divorce concepts, the text describes worshiping foreign gods on hills and under green trees as marital unfaithfulness. Despite this betrayal, the LORD repeatedly calls upon His faithless children to acknowledge their guilt and return to Him.Sources: the Bible text itself
Notes written with AI assistance from open sources (Theographic Bible Metadata, CC BY-SA 4.0; Easton’s Bible Dictionary, public domain) and reviewed before publishing.
Places in this chapter
Only places identified with high confidence are shown (90% or more according to the scholarly sources compiled by OpenBible). Period map: DARE (Digital Atlas of the Roman Empire), CC BY 4.0; modern map: © OpenStreetMap contributors; places: OpenBible.info (CC BY 4.0).
Credits and license for this translation
Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Hausa: Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ (Bible) of Nigeria copyright © 2009, 2020 Biblica, Inc. Language: Hausa Contributor: Biblica, Inc. An sami wannan aiki a sauƙaƙe a ƙarƙashin lasisin Ƙasa da ƙasa na Lasisin Creative Commons Attribution-ShareAlike 4.0 na Ƙasa da ƙasa (CC BY-SA). Don a ga kwafin wannan lasisi, a ziyarci: http://creativecommons.org/licenses/by-sa/4.0 ko kuma a aika ta wasiƙa zuwa ga Creative Commons, PO Box 1866, Mountain View, CA 94042, USA. “Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista ta hannun Biblica, Inc., kuma yin amfani da tambarin Biblica® na bukata rubutaccen izinin Biblica, Inc. A ƙarƙashin sharaɗin lasisin CC BY-SA, za ka iya kwafa ka kuma sāke raba wannan aikin da ba a gyaggyara ba muddin ba ka taɓa tambarin nan na Biblica® ba. Idan ka gyara wani kwafi ko ka juya wannan aiki, ta wurin kirkiro da aikin da aka samu, dole ne ka ka cire tambarin Biblica®. A aikin da aka samo, dole ne ka nuna canje-canjen da ka yi, ka kuma nuna aikin haka: “Ainihi aikin ta hannun Biblica, Inc. yana nan kyauta a www.biblica.com da buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki.” Dole sharaɗin neman izini ya fita a kan kan magana ko kuma a shafi neman izinin aiki kamar haka: Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. “Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini. “Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission. Dole kuma a samo aikin da ka yi daga ainihin aikin a ƙarƙashin wannan lasisi (CC BY-SA). Idan za ka so ka sanar da Biblica, Inc. dangane da juyinka na wannan aiki, sai ka tuntuɓe mu a https://open.bible/contact-us. This work is made available under the Creative Commons Attribution-ShareAlike 4.0 International License (CC BY-SA). To view a copy of this license, visit http://creativecommons.org/licenses/by-sa/4.0 or send a letter to Creative Commons, PO Box 1866, Mountain View, CA 94042, USA. Biblica® is a trademark registered by Biblica, Inc., and use of the Biblica® trademark requires the written permission of Biblica, Inc. Under the terms of the CC BY-SA license, you may copy and redistribute this unmodified work as long as you keep the Biblica® trademark intact. If you modify a copy or translate this work, thereby creating a derivative work, you must remove the Biblica® trademark. On the derivative work, you must indicate what changes you have made and attribute the work as follows: “The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible.” Notice of copyright must appear on the title or copyright page of the work as follows: Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. “Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini. “Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission. You must also make your derivative work available under the same license (CC BY-SA). If you would like to notify Biblica, Inc. regarding your translation of this work, please contact us at https://open.bible/contact-us. This translation is made available to you under the terms of the Creative Commons Attribution Share-Alike license 4.0. You have permission to share and redistribute this Bible translation in any format and to make reasonable revisions and adaptations of this translation, provided that: You include the above copyright and source information. If you make any changes to the text, you must indicate that you did so in a way that makes it clear that the original licensor is not necessarily endorsing your changes. If you redistribute this text, you must distribute your contributions under the same license as the original. Pictures included with Scriptures and other documents on this site are licensed just for use with those Scriptures and documents. For other uses, please contact the respective copyright owners. Note that in addition to the rules above, revising and adapting God's Word involves a great responsibility to be true to God's Word. See Revelation 22:18-19. 2025-05-03
Source: http://ebible.org/hausa/ · eBible.org