Jeremiah 20
Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ · Tap a verse to see its cross-references.
Irmiya da Fashhur
1Da firist nan Fashhur ɗan Immer, babban ma’aikaci a cikin haikalin Ubangiji, ya ji Irmiya yana annabcin waɗannan abubuwa, 2sai ya sa aka yi wa Irmiya dūka aka kuma sa shi a turu a Ƙofar Bisa na Benyamin a haikalin Ubangiji. 3Kashegari, sa’ad da Fashhur ya fitar da shi daga turu, sai Irmiya ya ce masa, “ Ubangiji ba zai kira ka Fashhur ba, amma ya ba ka suna Magor-Missabib. 4Gama ga abin da Ubangiji yana cewa, ‘Zan maishe ka abin razana ga kanka da kuma ga dukan abokanka; da idanunka za ka gan takobin abokan gāba yana kashe su. Zan miƙa Yahuda duka ga sarkin Babilon, wanda zai kwashe su zuwa Babilon ya kuma kashe su da takobi. 5Zan ba wa abokan gābansu dukan dukiyar wannan birni dukan amfaninsa, dukan abubuwa masu daraja na sarakunan Yahuda. Za su kwashe su ganima su kai su Babilon. 6Kai kuma Fashhur, da dukan waɗanda suke a gidanka za ku tafi zaman bauta a Babilon. A can za ku mutu a kuma binne ku, da kai da dukan abokanka waɗanda ka yi musu annabce-annabcen ƙarya.’ ”
Damuwar Irmiya
7Ya Ubangiji, ka ruɗe ni, na kuwa ruɗu;
ka fi ni ƙarfi, ka kuwa yi nasara.
Na zama abin dariya dukan yini;
kowa yana yi mini ba’a.
8Duk sa’ad da na yi magana, nakan tā da murya
ina furta hargitsi da hallaka.
Haka maganar Ubangiji ta kawo mini
zagi da reni dukan yini.
9Amma in na ce, “Ba zan ambace shi ba
ba zan ƙara yin magana da sunansa ba,”
sai in ji maganarsa a cikina kamar wuta,
wutar da aka kulle a ƙasusuwana.
Na gaji da danne ta a cikina;
tabbatacce ba zan iya ba.
10Na ji mutane da yawa suna raɗa cewa,
“Razana ta kowace fuska!
Mu kai kararsa! Bari mu kai kararsa!”
Dukan abokaina
suna jira in yi tuntuɓe, suna cewa,
“Mai yiwuwa a ruɗe shi;
sai mu yi nasara a kansa
mu ɗau fansa a kansa.”
11Amma Ubangiji yana tare da ni kamar babban jarumi;
saboda haka masu tsananta mini za su yi tuntuɓe ba kuwa za su yi nasara ba.
Za su fāɗi su kuma sha mummunar kunya;
ba za a taɓa manta da rashin bangirmansu ba.
12Ya Ubangiji Maɗaukaki, kai da kake gwada adali
kana bincika zuciya duk da tunani,
bari in ga sakayyarka a kansu,
gama a gare ka na miƙa damuwata.
13Ku rera ga Ubangiji!
Ku yabi Ubangiji!
Ya kuɓutar da ran mabukaci
daga hannuwan mugaye.
14La’ananniya ce ranar da aka haife ni!
Kada ranar da mahaifiyata ta haife ni ta zama mai albarka!
15La’ananne ne mutumin da ya kawo wa mahaifina labari,
wanda ya sa shi ya yi murna cewa, “An haifa maka yaro, ɗa namiji!”
16Bari mutumin ya zama kamar garuruwan
da Ubangiji ya tumɓuke ba tausayi.
Bari yă ji kuka da safe
kururuwan yaƙi kuma da tsakar rana.
17Gama bai kashe ni a cikin ciki ba,
da ma ya sa cikin mahaifiyata ya zama kabarina,
cikinta ya fadada har abada.
18Me ya sa na ma fito daga cikin ciki
in ga wahala da baƙin ciki
in kuma ƙare kwanakina da kunya?

Did you know?
Jeremiah's Persecution and Inner Turmoil
- Pashhur, the priest who arrested and beat Jeremiah, was the son of Immer—the ancestral head of the sixteenth priestly division—and served as chief official in the house of the LORD. His high administrative post gave him the authority to punish Jeremiah and confine him in wooden stocks at the Upper Gate of Benjamin near the temple.Sources: Immer · Gate of Benjamin · the Bible text itself
- Upon being released, Jeremiah announced that God gave Pashhur the symbolic name 'Magor-missabib' ('terror on every side'). Jeremiah prophesied that Pashhur, his household, and his friends would be carried away captive into Babylon to die, alongside the plunder of Judah's wealth.Sources: Babylon · the Bible text itself
- The chapter reveals Jeremiah's intense emotional struggle between public derision and prophetic compulsion. Although mocked and betrayed by close friends, he confessed that holding back God's message felt like a fire burning in his heart and shut up within his bones.Sources: Jeremiah · the Bible text itself
Notes written with AI assistance from open sources (Theographic Bible Metadata, CC BY-SA 4.0; Easton’s Bible Dictionary, public domain) and reviewed before publishing.
Places in this chapter
- Benjamin Gate · Today: in Jerusalem · 31.777, 35.234 · verse 2
- Babylon · 32.543, 44.422 · verses 4, 5, 6
- Jerusalem · 31.777, 35.234 · verse 5
Only places identified with high confidence are shown (90% or more according to the scholarly sources compiled by OpenBible). Period map: DARE (Digital Atlas of the Roman Empire), CC BY 4.0; modern map: © OpenStreetMap contributors; places: OpenBible.info (CC BY 4.0).
Credits and license for this translation
Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Hausa: Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ (Bible) of Nigeria copyright © 2009, 2020 Biblica, Inc. Language: Hausa Contributor: Biblica, Inc. An sami wannan aiki a sauƙaƙe a ƙarƙashin lasisin Ƙasa da ƙasa na Lasisin Creative Commons Attribution-ShareAlike 4.0 na Ƙasa da ƙasa (CC BY-SA). Don a ga kwafin wannan lasisi, a ziyarci: http://creativecommons.org/licenses/by-sa/4.0 ko kuma a aika ta wasiƙa zuwa ga Creative Commons, PO Box 1866, Mountain View, CA 94042, USA. “Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista ta hannun Biblica, Inc., kuma yin amfani da tambarin Biblica® na bukata rubutaccen izinin Biblica, Inc. A ƙarƙashin sharaɗin lasisin CC BY-SA, za ka iya kwafa ka kuma sāke raba wannan aikin da ba a gyaggyara ba muddin ba ka taɓa tambarin nan na Biblica® ba. Idan ka gyara wani kwafi ko ka juya wannan aiki, ta wurin kirkiro da aikin da aka samu, dole ne ka ka cire tambarin Biblica®. A aikin da aka samo, dole ne ka nuna canje-canjen da ka yi, ka kuma nuna aikin haka: “Ainihi aikin ta hannun Biblica, Inc. yana nan kyauta a www.biblica.com da buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki.” Dole sharaɗin neman izini ya fita a kan kan magana ko kuma a shafi neman izinin aiki kamar haka: Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. “Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini. “Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission. Dole kuma a samo aikin da ka yi daga ainihin aikin a ƙarƙashin wannan lasisi (CC BY-SA). Idan za ka so ka sanar da Biblica, Inc. dangane da juyinka na wannan aiki, sai ka tuntuɓe mu a https://open.bible/contact-us. This work is made available under the Creative Commons Attribution-ShareAlike 4.0 International License (CC BY-SA). To view a copy of this license, visit http://creativecommons.org/licenses/by-sa/4.0 or send a letter to Creative Commons, PO Box 1866, Mountain View, CA 94042, USA. Biblica® is a trademark registered by Biblica, Inc., and use of the Biblica® trademark requires the written permission of Biblica, Inc. Under the terms of the CC BY-SA license, you may copy and redistribute this unmodified work as long as you keep the Biblica® trademark intact. If you modify a copy or translate this work, thereby creating a derivative work, you must remove the Biblica® trademark. On the derivative work, you must indicate what changes you have made and attribute the work as follows: “The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible.” Notice of copyright must appear on the title or copyright page of the work as follows: Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. “Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini. “Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission. You must also make your derivative work available under the same license (CC BY-SA). If you would like to notify Biblica, Inc. regarding your translation of this work, please contact us at https://open.bible/contact-us. This translation is made available to you under the terms of the Creative Commons Attribution Share-Alike license 4.0. You have permission to share and redistribute this Bible translation in any format and to make reasonable revisions and adaptations of this translation, provided that: You include the above copyright and source information. If you make any changes to the text, you must indicate that you did so in a way that makes it clear that the original licensor is not necessarily endorsing your changes. If you redistribute this text, you must distribute your contributions under the same license as the original. Pictures included with Scriptures and other documents on this site are licensed just for use with those Scriptures and documents. For other uses, please contact the respective copyright owners. Note that in addition to the rules above, revising and adapting God's Word involves a great responsibility to be true to God's Word. See Revelation 22:18-19. 2025-05-03
Source: http://ebible.org/hausa/ · eBible.org