Nations Bible

Jeremiah 17

Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ · Tap a verse to see its cross-references.

1“An rubuta zunubin Yahuda da alƙalamin ƙarfe,

an rubuta da tsinin dutse,

a kan allunan zukatansu

da kuma a kan ƙahonin bagadansu.

2Har ’ya’yansu ma sun tuna

bagadansu da ginshiƙan Asheransu

kusa da itatuwa masu duhuwa

da kuma a kan tuddai masu tsayi.

3Dutsena a ƙasar

da dukiyarku na ƙasar da dukan arzikinku

za a ba da su ganima,

tare da masujadanku na kan tuddai,

saboda zunubi ko’ina a ƙasarku.

4Saboda laifinku za ku rasa

gādon da na ba ku.

Zan bautar da ku ga abokan gābanku

a ƙasar da ba ku sani ba,

domin kun husata ni,

zai kuwa ci har abada.”

5Ga abin da Ubangiji yana cewa,

“La’ananne ne mutumin da yake dogara ga mutum,

wanda ya dogara ga jiki don ƙarfi

wanda kuma zuciyarsa ta juya wa Ubangiji baya.

6Zai zama kamar ɗan kurmi a ƙasar da take kango;

ba za su ga arziki sa’ad da ya zo ba.

Za su zauna a busassun wuraren hamada,

a cikin ƙasar gishiri inda ba kowa.

7“Amma mai albarka ne mutumin da yake dogara ga Ubangiji,

wanda ƙarfin halinsa yana daga Ubangiji.

8Za su zama kamar itacen da aka dasa kusa da ruwa

wanda ya miƙa saiwoyinsa zuwa cikin rafi.

Ba ya jin tsoro sa’ad da zafi ya zo;

ganyayensa kullum kore suke.

Ba shi da damuwa a shekarar fări

ba ya taɓa fasa ba da ’ya’ya.”

9Zuciya ta fi kome ruɗu

ta fi ƙarfin warkewa.

Wa zai iya gane ta?

10“Ni Ubangiji nakan bincike zuciya

in gwada tunani,

don in sāka wa kowane mutum bisa ga halinsa,

bisa ga ayyukansa.”

11Kamar makwarwar da ta kwanta a kan ƙwan da ba ita ta zuba ba

haka yake da mutumin da ya sami arziki a hanyar da ba daidai ba.

A tsakiyar rayuwarsa za su rabu da shi,

a ƙarshe kuma zai zama wawa.

12Kursiyi mai daraja, da aka ɗaukaka tun daga farko,

shi ne wuri mai tsarkinmu.

13Ya Ubangiji, sa zuciyar Isra’ila,

duk waɗanda suka rabu da kai za su sha kunya.

Waɗanda suka juya maka baya za a rubuta su a ƙura

domin sun yashe Ubangiji,

maɓulɓular ruwan rai.

14Ka warkar da ni, ya Ubangiji, zan kuwa warke;

ka cece ni zan kuwa cetu,

gama kai ne nake yabo.

15Sun riƙa ce mini, “Ina maganar Ubangiji take?

Bari tă cika yanzu!”

16Ban gudu zaman mai yin maka kiwo ba;

ka sani ban marmarin ranan nan ta masifa ba.

Abin da ya fito daga leɓunana kuwa, a bayyane suke gare ka.

17Kada ka zama mini abin razana;

kai ne mafakata a ranar masifa.

18Bari masu tsananta mini su sha kunya,

amma ka kiyaye ni daga shan kunya;

bari su tsorata,

amma ka kiyaye ni da razana.

Ka kawo musu ranar masifa;

ka hallaka su da hallaka riɓi biyu.

Kiyaye Asabbaci da tsarki

19Ga abin da Ubangiji ya ce mini, “Ka je ka tsaya a ƙofar mutane, inda sarakunan Yahuda sukan shiga su fita; ka tsaya kuma a dukan sauran ƙofofin Urushalima. 20Ka ce musu, ‘Ku ji maganar Ubangiji, ku sarakunan Yahuda, da dukan mutanen Yahuda da dukan mazaunan Urushalima waɗanda suke bi ta waɗannan ƙofofi. 21Ga abin da Ubangiji yana cewa, ku yi hankali kada ku ɗauki kaya a ranar Asabbaci ko ku shigar da shi ta ƙofofin Urushalima. 22Kada ku fitar da kayan gidajenku ko ku yi wani aiki a ranar Asabbaci mai tsarki, yadda na umarci kakanni-kakanninku. 23Duk da haka ba su saurara ba, ba su kuwa mai da hankali ba; suka taurare ba su kuwa saurara ko su karɓi horo ba. 24Amma in kuka yi hankali kuka yi mini biyayya, in ji Ubangiji, ba ku kuwa shigar da kaya ta ƙofofi a ranar Asabbaci ba, amma kuka kiyaye ranar Asabbaci da tsarki ba tare da yin wani aiki a cikinta ba, 25sa’an nan sarakuna da suke zama a kursiyin Dawuda za su shiga ta ƙofofin wannan birni tare da fadawansu. Su da fadawansu za su shiga a kan kekunan yaƙi da kuma a kan dawakai, mutanen Yahuda suna musu rakiya tare da waɗanda suke zaune a Urushalima, wannan birni kuwa za tă kasance da mazauna har abada. 26Mutane za su zo daga garuruwan Yahuda da ƙauyukan kewaye da Urushalima, daga iyakar Benyamin da gindin tuddan yamma, daga ƙasar tudu da kuma Negeb, suna kawo hadayun ƙonawa da hadayun gari, sadakokin turare da na godiya zuwa gidan Ubangiji. 27Amma in ba ku yi mini biyayya ba, ba ku kiyaye ranar Asabbaci da tsarki ba, kuka ɗauki wani kaya yayinda kuke shiga ƙofofin Urushalima a ranar Asabbaci, to, sai in cinna wa ƙofofin Urushalima wutar da ba a iya kashewa, tă cinye kagaranta.’ ”

Artistic illustration — an interpretation, not a historical record.

Did you know?

Trust, the Heart, and the Sabbath

  • The iron stylus and diamond point were ancient tools used to carve deep, permanent inscriptions into hard stone or metal surfaces. Jeremiah invokes this image to emphasize that the idolatry of Judah was not a superficial slip, but deeply etched into their hearts and upon the horns of their altars.Sources: the Bible text itself
  • Jeremiah contrasts a solitary shrub in the parched, salty desert with a flourishing tree planted by a stream. A tree with roots reaching into water stays green and continues bearing fruit even in years of drought, serving as an image of enduring life for those who trust in God rather than human strength.Sources: the Bible text itself
  • Jeremiah was instructed to proclaim God's word at the gates of Jerusalem, specifically forbidding the carrying of commercial loads on the Sabbath. Keeping the Sabbath holy promised the continuation of kings on the throne of David and the arrival of worshippers from the territory of Benjamin, Judah, and the arid Negev.Sources: the Bible text itself · David · Benjamin (patriarch) · Jerusalem

Notes written with AI assistance from open sources (Theographic Bible Metadata, CC BY-SA 4.0; Easton’s Bible Dictionary, public domain) and reviewed before publishing.

Places in this chapter

  • Arabah · 30.417, 35.151 · verse 6
  • Jerusalem · 31.777, 35.234 · verses 19, 20, 21, 25, 26, 27
  • People’s Gate · Today: in Jerusalem · 31.777, 35.234 · verse 19
  • Negeb · 31.245, 34.841 · verse 26
  • Shephelah · 31.692, 34.875 · verse 26

Only places identified with high confidence are shown (90% or more according to the scholarly sources compiled by OpenBible). Period map: DARE (Digital Atlas of the Roman Empire), CC BY 4.0; modern map: © OpenStreetMap contributors; places: OpenBible.info (CC BY 4.0).

Credits and license for this translation
Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™
Hausa: Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ (Bible) of Nigeria
copyright © 2009, 2020 Biblica, Inc.
Language: Hausa
Contributor: Biblica, Inc.
An sami wannan aiki a sauƙaƙe a ƙarƙashin lasisin Ƙasa da ƙasa na Lasisin Creative Commons Attribution-ShareAlike 4.0 na Ƙasa da ƙasa (CC BY-SA). Don a ga kwafin wannan lasisi, a ziyarci: http://creativecommons.org/licenses/by-sa/4.0 ko kuma a aika ta wasiƙa zuwa ga Creative Commons, PO Box 1866, Mountain View, CA 94042, USA.
“Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista ta hannun Biblica, Inc., kuma yin amfani da tambarin Biblica® na bukata rubutaccen izinin Biblica, Inc. A ƙarƙashin sharaɗin lasisin CC BY-SA, za ka iya kwafa ka kuma sāke raba wannan aikin da ba a gyaggyara ba muddin ba ka taɓa tambarin nan na Biblica® ba. Idan ka gyara wani kwafi ko ka juya wannan aiki, ta wurin kirkiro da aikin da aka samu, dole ne ka ka cire tambarin Biblica®. A aikin da aka samo, dole ne ka nuna canje-canjen da ka yi, ka kuma nuna aikin haka: “Ainihi aikin ta hannun Biblica, Inc. yana nan kyauta a www.biblica.com da buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki.”
Dole sharaɗin neman izini ya fita a kan kan magana ko kuma a shafi neman izinin aiki kamar haka:
Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™
Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc.
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™
Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc.
“Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini.
“Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission.
Dole kuma a samo aikin da ka yi daga ainihin aikin a ƙarƙashin wannan lasisi (CC BY-SA).
Idan za ka so ka sanar da Biblica, Inc. dangane da juyinka na wannan aiki, sai ka tuntuɓe mu a https://open.bible/contact-us.
This work is made available under the Creative Commons Attribution-ShareAlike 4‪.0 International License (CC BY-SA). To view a copy of this license, visit http://creativecommons.org/licenses/by-sa/4‪.0 or send a letter to Creative Commons, PO Box 1866, Mountain View, CA 94042, USA.
Biblica® is a trademark registered by Biblica, Inc., and use of the Biblica® trademark requires the written permission of Biblica, Inc. Under the terms of the CC BY-SA license, you may copy and redistribute this unmodified work as long as you keep the Biblica® trademark intact. If you modify a copy or translate this work, thereby creating a derivative work, you must remove the Biblica® trademark. On the derivative work, you must indicate what changes you have made and attribute the work as follows: “The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible.”
Notice of copyright must appear on the title or copyright page of the work as follows:
Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™
Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc.
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™
Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc.
“Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini.
“Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission.
You must also make your derivative work available under the same license (CC BY-SA).
If you would like to notify Biblica, Inc. regarding your translation of this work, please contact us at https://open.bible/contact-us.
This translation is made available to you under the terms of the
Creative Commons Attribution Share-Alike license 4.0.
You have permission to share and redistribute this Bible translation in any format and to make reasonable revisions and adaptations of this translation, provided that:
You include the above copyright and source information.
If you make any changes to the text, you must indicate that you did so in a way that makes it clear that the original licensor is not necessarily endorsing your changes.
If you redistribute this text, you must distribute your contributions under the same license as the original.
Pictures included with Scriptures and other documents on this site are licensed just for use with those Scriptures and documents.
For other uses, please contact the respective copyright owners.
Note that in addition to the rules above, revising and adapting God's Word involves a great responsibility to be true to God's Word. See Revelation 22:18-19.
2025-05-03

Source: http://ebible.org/hausa/ · eBible.org

Talk to us

Tell us where you read from, how the Bible has helped you, or what we could improve. We read every message.