Judges 20
Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ · Tap a verse to see its cross-references.
Isra’ila sun yaƙi mutanen Benyamin
1Sa’an nan dukan Isra’ilawa daga Dan zuwa Beyersheba kuma daga ƙasar Gileyad mutane kamar mutum guda suka fito suka taru a gaban Ubangiji a Mizfa. 2Shugabanni dukan kabilan mutane na kabilan Isra’ila suka zazzauna a wurarensu a taron jama’ar Allah, mayaƙa dubu ɗari huɗu masu ɗamara da takuba. 3(Mutanen Benyamin suka ji cewa Isra’ilawa sun haura zuwa Mizfa.) Sa’an nan Isra’ilawa suka ce, “Gaya mana yadda wannan mugun abu ya faru.”
4Sai Balawen, mijin matar da aka kashe ya ce, “Ni da ƙwarƙwarata mun zo Gibeya a Benyamin don mu kwana. 5Da dad dare mutanen Gibeya suka bi ni suka kewaye gidan da niyya su kashe ni. Suka yi wa ƙwarƙwarata fyaɗe, har ta mutu. 6Na ɗauki ƙwarƙwarata na yayyanka gunduwa-gunduwa na aika da shi ga kowane yankin gādon Isra’ila, domin sun aikata mugu abu da abin kunya a Isra’ila. 7To, dukanku Isra’ilawa, sai ku yi magana ku kuma yanke hukuncinku.”
8Dukan mutane suka tashi kamar mutum ɗaya, suna cewa “Ba waninmu da zai tafi gida. Sam, babu ko ɗayanmu da zai koma gidansa. 9Amma yanzu ga abin da za mu yi wa Gibeya. Za mu haura mu fāɗa yadda ƙuri’a ta nunar. 10Za mu ɗauko mutum goma a kowane mutum ɗari daga dukan kabilan Isra’ila, da ɗari a dubu, da kuma dubu a dubu goma, domin a tanada wa mayaƙan. Sa’an nan, sa’ad da mayaƙan suka iso Geba a Benyamin, za su yi da su daidai bisa ga muguntar da suka yi a Isra’ila.” 11Saboda haka dukan mutane Isra’ilawa suka taru suka kuma haɗu kamar mutum guda don su fāɗa wa birnin da yaƙi.
12Kabilan Isra’ila suka aika jakadu a ko’ina a cikin kabilar Benyamin cewa, “Wace irin mugunta ce wannan da kuka aikata? 13Yanzu fa sai ku fitar da waɗannan ’yan iskan da suka aikata wannan abu na Gibeya don mu kashe su mu kawar da mugunta daga Isra’ila!”
Amma mutanen Benyamin ba su saurari ’yan’uwansu Isra’ilawa ba. 14Daga biranensu suka tattaru a Gibeya don su yaƙi Isra’ilawa. 15Nan da nan mutanen Benyamin suka tattara mayaƙa dubu ashirin da shida masu takuba daga biranensu, ban da mayaƙa ɗari bakwai da aka zaɓa daga mazauna a Gibeya. 16Cikin dukan mayaƙan nan akwai zaɓaɓɓu mutane ɗari bakwai waɗanda su bahagwai ne, kowanne yana iya harbin gashin guda na kai da majajjawa ba kuskure.
17Isra’ila kuwa, ban da Benyamin, sun tara mayaƙa masu takobi dubu ɗari huɗu, dukansu gwanayen yaƙi ne.
18Sai Isra’ilawa suka haura zuwa Betel suka nemi nufin Allah, suka ce, “Wane ne a cikinmu zai fara fāɗa wa mutanen Benyamin?”
Ubangiji ya ce, “Yahuda ce za tă fara.”
19Kashegari sai Isra’ilawa suka tashi suka kafa sansani kusa da Gibeya. 20Mutanen Isra’ila suka fita yaƙi da mutane Benyamin suka kuma ja dāgār yaƙi a Gibeya. 21Mutanen Benyamin suka fito daga Gibeya suka kashe mutum dubu ashirin da biyu na Isra’ilawa a dāgār yaƙi a ranar. 22Amma mutanen Isra’ila suka ƙarfafa juna, suka sāke koma inda suka ja dāgā a rana ta farko. 23Isra’ilawa suka haura suka yi kuka a gaban Ubangiji, har yamma, suka nemi nufin Ubangiji. Suka ce, “Mu sāke koma yaƙi da mutanen Benyamin, ’yan’uwanmu?”
Ubangiji ya ce, “Ku haura ku fāɗa musu.”
24Sai Isra’ilawa suka matsa kusa da Benyamin a rana ta biyu. 25A wannan lokaci, da mutanen Benyamin suka fito daga Gibeya don su yaƙe su, sai suka sāke kashe Isra’ilawa dubu goma sha takwas, dukansu ɗauke da takuba.
26Sa’an nan Isra’ilawa, dukan mutane, suka haura zuwa Betel, a can suka zauna suna kuka a gaban Ubangiji. Suka yi azumi a wannan rana har yamma suka miƙa hadayun ƙonawa da hadayun salama ga Ubangiji. 27Isra’ilawa suka nemi nufin Ubangiji (A kwanakin nan akwatin alkawarin Allah yana can, 28Finehas ɗan Eleyazar, ɗan Haruna, kuwa yana hidima a gabansa.) Suka ce, “Mu sāke haura mu yi yaƙi da mutanen Benyamin ’yan’uwanmu, ko a’a?”
Ubangiji ya ce, “Ku je, gama gobe zan ba da su a hannuwanku.”
29Sa’an nan Isra’ila ta yi kwanto kewaya da Gibeya. 30Suka haura su kara da mutanen Benyamin a rana ta uku suka ja dāgā a Gibeya kamar dā. 31Mutanen Benyamin suka fito su same su aka kuma jawo su nesa da birnin. Suka fara karkashe Isra’ilawa kamar dā, har aka kashe wajen mutum talatin a filaye da kuma a hanyoyi, wadda take zuwa Betel da kuma wadda take zuwa Gibeya. 32Yayinda mutanen Benyamin suna cewa, “Muna cin nasara a kansu kamar dā,” Isra’ilawa kuwa suna cewa, “Mu yi ta jan da baya mu janye su daga birni zuwa kan hanyoyi.”
33Dukan mutanen Isra’ila suka taso daga wurarensu suka ja dāgā a Ba’al-Tamar, Isra’ilawan da suka yi kwanto a yammancin Geba kuwa suka fito. 34Sa’an nan jarumai Isra’ila dubu goma suka yi gaba suka kai wa Gibeya hari. Yaƙi kuwa ya yi zafi har mutane Benyamin ba su san masifa tana dab da su ba. 35Ubangiji kuwa ya fatattake mutanen Benyamin a gaban Isra’ila; a ranar kuwa Isra’ilawa sun kashe mutum 25,100 na mutanen Benyamin, dukansu ɗauke da takuba. 36Sa’an nan Benyamin suka ga an ci su.
To, mutanen Isra’ila sun yi ta ja da baya daga mutanen Benyamin domin suna dogara ga waɗanda sa su yi kwanto kusa da Gibeya ne. 37Mutanen da suke kwanto suka yi wuf suka ruga cikin Gibeya, suka bazu suka kuma karkashe dukan waɗanda suke a birnin. 38Mutanen Isra’ila sun riga sun shirya da ’yan kwanton cewa su murtuke hayaƙi daga birnin, 39a sa’an nan ne mutanen Isra’ila za su juya su fāɗa wa mutane Benyamin da yaƙi.
Mutanen Benyamin sun fara karkashe mutum talatin na Isra’ila, sai suka ce, “Muna cin nasara a kansu kamar dā.” 40Amma da alamar hayaƙi ya fara murtukewa daga birnin, sai mutanen Benyamin suka juya suka ga hayaƙi yana murtukewa ko’ina a cikin birnin zuwa sararin sama. 41Sa’an nan mutanen Isra’ila suka juyo musu, mutanen Benyamin kuwa suka tsorata domin sun gane masifa ta zo musu. 42Saboda haka suka tsere a gaban Isra’ila zuwa wajen hamada, amma ba su iya tsere wa yaƙin ba. Mutanen Isra’ila da suka fito daga cikin birnin suka karkashe su a can. 43Suka kewaye mutanen Benyamin, suka kore su, suka fatattake su a wajajen Gibeya a gabashi. 44Mutum dubu goma sha takwas na mutanen Benyamin suka mutu dukansu kuwa jarumai ne. 45Da suka juya suka juya suka tsere zuwa wajajen hamada zuwa dutsen Rimmon, Isra’ilawa suka kashe mutum dubu biyar a kan hanyoyi. Suka yi ta matsa wa mutanen Benyamin har zuwa Gidom suka kashe mutum dubu biyu kuma.
46A ranar kuwa mutanen Benyamin dubu ashirin da biyar ne aka kashe, dukansu jarumai. 47Amma mutane ɗari shida suka juya suka tsere wajajen hamada zuwa dutsen Rimmon, inda suka zauna wata huɗu. 48Mutanen Isra’ila suka koma wurin mutanen Benyamin suka kashe dukan waɗanda suke a birnin, tare da dabbobi da kome da suka samu. Dukan garuruwan da suka samu sun ƙone su ƙaf.

Did you know?
The War Against Benjamin
- The phrase 'from Dan to Beersheba' describes the full extent of the Promised Land from north to south, a distance of roughly 144 miles (230 km). The assembly gathered at Mizpah, a hilltop town located a few miles northwest of Jerusalem that regularly served as a meeting place during major national crises.Sources: Beersheba · Mizpah · the Bible text itself
- The text notes that Phinehas, son of Eleazar and grandson of Aaron, ministered before the Ark of the Covenant at Bethel when Israel inquired of God. This detail indicates that the civil war at Gibeah took place relatively early in the period of the judges, within two generations of the Exodus.Sources: Phinehas (Levite) · Eleazar · Aaron · Bethel (of Palestine)
- After devastating losses that nearly wiped out the tribe of Benjamin, only 600 surviving warriors managed to escape. They fled to the Rock of Rimmon, a steep hilltop site on the edge of the hill country, where they held out for four months.Sources: Rimmon · Gibeah · the Bible text itself
Notes written with AI assistance from open sources (Theographic Bible Metadata, CC BY-SA 4.0; Easton’s Bible Dictionary, public domain) and reviewed before publishing.
Places in this chapter
- Dan · Today: Tel Dan · 33.249, 35.652 · verse 1
- Gilead · Today: Gilead 1 · 32.187, 35.692 · verse 1
- Jordan · Today: Jordan River · 31.761, 35.558 · verse 1
- Maareh-geba · Today: within 2 km of Tel el Ful · 31.823, 35.231 · verse 33
Only places identified with high confidence are shown (90% or more according to the scholarly sources compiled by OpenBible). Period map: DARE (Digital Atlas of the Roman Empire), CC BY 4.0; modern map: © OpenStreetMap contributors; places: OpenBible.info (CC BY 4.0).
Credits and license for this translation
Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Hausa: Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ (Bible) of Nigeria copyright © 2009, 2020 Biblica, Inc. Language: Hausa Contributor: Biblica, Inc. An sami wannan aiki a sauƙaƙe a ƙarƙashin lasisin Ƙasa da ƙasa na Lasisin Creative Commons Attribution-ShareAlike 4.0 na Ƙasa da ƙasa (CC BY-SA). Don a ga kwafin wannan lasisi, a ziyarci: http://creativecommons.org/licenses/by-sa/4.0 ko kuma a aika ta wasiƙa zuwa ga Creative Commons, PO Box 1866, Mountain View, CA 94042, USA. “Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista ta hannun Biblica, Inc., kuma yin amfani da tambarin Biblica® na bukata rubutaccen izinin Biblica, Inc. A ƙarƙashin sharaɗin lasisin CC BY-SA, za ka iya kwafa ka kuma sāke raba wannan aikin da ba a gyaggyara ba muddin ba ka taɓa tambarin nan na Biblica® ba. Idan ka gyara wani kwafi ko ka juya wannan aiki, ta wurin kirkiro da aikin da aka samu, dole ne ka ka cire tambarin Biblica®. A aikin da aka samo, dole ne ka nuna canje-canjen da ka yi, ka kuma nuna aikin haka: “Ainihi aikin ta hannun Biblica, Inc. yana nan kyauta a www.biblica.com da buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki.” Dole sharaɗin neman izini ya fita a kan kan magana ko kuma a shafi neman izinin aiki kamar haka: Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. “Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini. “Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission. Dole kuma a samo aikin da ka yi daga ainihin aikin a ƙarƙashin wannan lasisi (CC BY-SA). Idan za ka so ka sanar da Biblica, Inc. dangane da juyinka na wannan aiki, sai ka tuntuɓe mu a https://open.bible/contact-us. This work is made available under the Creative Commons Attribution-ShareAlike 4.0 International License (CC BY-SA). To view a copy of this license, visit http://creativecommons.org/licenses/by-sa/4.0 or send a letter to Creative Commons, PO Box 1866, Mountain View, CA 94042, USA. Biblica® is a trademark registered by Biblica, Inc., and use of the Biblica® trademark requires the written permission of Biblica, Inc. Under the terms of the CC BY-SA license, you may copy and redistribute this unmodified work as long as you keep the Biblica® trademark intact. If you modify a copy or translate this work, thereby creating a derivative work, you must remove the Biblica® trademark. On the derivative work, you must indicate what changes you have made and attribute the work as follows: “The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible.” Notice of copyright must appear on the title or copyright page of the work as follows: Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. “Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini. “Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission. You must also make your derivative work available under the same license (CC BY-SA). If you would like to notify Biblica, Inc. regarding your translation of this work, please contact us at https://open.bible/contact-us. This translation is made available to you under the terms of the Creative Commons Attribution Share-Alike license 4.0. You have permission to share and redistribute this Bible translation in any format and to make reasonable revisions and adaptations of this translation, provided that: You include the above copyright and source information. If you make any changes to the text, you must indicate that you did so in a way that makes it clear that the original licensor is not necessarily endorsing your changes. If you redistribute this text, you must distribute your contributions under the same license as the original. Pictures included with Scriptures and other documents on this site are licensed just for use with those Scriptures and documents. For other uses, please contact the respective copyright owners. Note that in addition to the rules above, revising and adapting God's Word involves a great responsibility to be true to God's Word. See Revelation 22:18-19. 2025-05-03
Source: http://ebible.org/hausa/ · eBible.org