Nations Bible

Isaiah 22

Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ · Tap a verse to see its cross-references.

Annabci a kan Urushalima

1Abin da Allah ya faɗa game da Kwarin Wahayi.

Mene ne ya dame ku a yanzu,

da dukanku kuka hau kan rufin gidaje.

2Ya kai gari cike da hayaniya,

Ya ke birnin tashin hankali da alkarya mai murna?

Mutanenki ba su mutu ta wurin takobi ba,

ba kuwa za su mutu a yaƙi ba.

3Dukan shugabanninki sun gudu gaba ɗaya;

an kama su ba tare da an yi amfani da baka ba.

Dukanku da aka kama an kwashe ku ɗaurarru gaba ɗaya,

kun gudu tun abokin gāba yana da nisa.

4Saboda haka na ce, “Ƙyale ni kurum;

bari in yi kuka mai zafi.

Kada ka yi ƙoƙarin ta’azantar da ni

a kan hallakar mutanena.”

5Ubangiji, Ubangiji Maɗaukaki, yana da ranar

giggicewa da tattakewa da banrazana

a cikin Kwarin Wahayi,

ranar ragargazawar katanga

da ta yin kuka ga duwatsu.

6Elam ya ɗauki kwari da baka,

tare da mahayan kekunan yaƙinta da dawakai;

Kir ta buɗe garkuwoyi.

7Kwarurukanku mafi kyau sun cika da kekunan yaƙi,

an kuma tsai da mahayan dawakai a ƙofofin birni.

8An rurrushe kāriyar Yahuda,

a ranan nan kuwa kun yi la’akari

da makamai a cikin Fadan Kurmi;

9kuka ga cewa Birnin Dawuda

tana da wuraren kāriya masu yawa da suka tsattsage;

kuka tattara ruwa

a Tafkin Ƙasa.

10Kuka ƙirga gine-gine a Urushalima

kuka kuma rurrushe gidaje don ku ƙarfafa katanga.

11Kuka gina matarar ruwa tsakanin katanga biyu

saboda ruwan Tsohon Tafki,

amma ba ku yi la’akari da Wannan da ya yi su ba,

ko ku kula da Wannan da ya shirya shi tuntuni.

12Ubangiji, Ubangiji Maɗaukaki

ya kira ku a wannan rana

don ku yi kuka ku yi ihu,

don ku aske gashinku ku kuma sa tsummoki.

13Amma duba, sai ga shi kuna farin ciki kuna kuma murna,

kuna yankan shanu kuna kashe tumaki,

kuna cin nama kuna kuma shan ruwan inabi!

Kuna cewa, “Bari mu ci mu kuma sha,

gama gobe za mu mutu!”

14Ubangiji Maɗaukaki ya bayyana wannan a kunnena cewa, “Har ranar mutuwarka ba za a yi kafarar wannan zunubi ba,” in ji mai girma Ubangiji Maɗaukaki.

15Ga abin da Ubangiji, Ubangiji Maɗaukaki, ya faɗa,

“Je, ka faɗa wa wannan mai hidima,

Shebna, sarkin fada.

16Mene ne kake yi a nan kuma wa ya ba ka izini

ka haƙa kabari wa kanka a nan,

kana fafe kabarinka a bisa

kana sassaƙa wurin hutunka a dutse?

17“Ka yi hankali, Ubangiji yana shirin ya kama ka da ƙarfi

ya kuma ɗauke ka, ya kai mai ƙarfi.

18Zai dunƙule ka kamar ƙwallo

ya jefa ka a cikin ƙasa mai girma.

A can za ka mutu

a can kuma kekunan yaƙinka masu daraja za su kasance,

abin kunya kake ga gidan maigidanka!

19Zan tumɓuke ka daga makaminka,

za a kuma kore ka daga matsayinka.

20“A wannan rana zan kira bawana, Eliyakim ɗan Hilkiya. 21Zan rufe shi da rigarka in kuma yi masa ɗamara in miƙa masa ikonka. Zai zama mahaifi ga waɗanda suke zama a Urushalima da kuma gidan Yahuda. 22Zan sa mabuɗin gidan Dawuda a kafaɗarsa; abin da ya buɗe ba mai rufewa, kuma abin da ya rufe ba mai buɗewa. 23Zan kafa shi kamar turke a tsayayyen wuri; zai zama mazaunin daraja domin gidan mahaifinsa. 24Dukan ɗaukakar iyalinsa za tă rataya a kansa daga ’ya’yansa da zuriyarsa har zuwa dukan ƙananan kayan aikinsa, wato, daga kwanoni har zuwa tuluna.

25“A ranan nan, in ji Ubangiji Maɗaukaki, turken da aka kafa a tsayayyen wuri zai sumɓule; za a sare shi ya fāɗi, za a kuma datse nauyin da yake rataya a kansa.” Ni Ubangiji na faɗa.

Artistic illustration — an interpretation, not a historical record.

Did you know?

The Valley of Vision and the Palace Stewards

  • Facing impending siege, the people of Jerusalem inspected armaments in the House of the Forest, channeled water from the lower pool into reservoirs, and tore down residential houses to reinforce breaches in the walls of the City of David.Sources: the Bible text itself · Jerusalem
  • Shebna, the steward over the royal palace, was rebuked for carving an elaborate tomb for himself in the rock. God declared that Shebna would be ousted and replaced by Eliakim son of Hilkiah, who would receive the robe of office and the key to the house of David.Sources: the Bible text itself · Shebna · Eliakim
  • The invading army arrayed against the Valley of Vision included archers from Elam, a highland territory east of Babylonia, alongside warriors from Kir bearing shields.Sources: the Bible text itself · Elam · Kir

Notes written with AI assistance from open sources (Theographic Bible Metadata, CC BY-SA 4.0; Easton’s Bible Dictionary, public domain) and reviewed before publishing.

Places in this chapter

  • Jerusalem · 31.777, 35.234 · verses 1, 5, 10, 21
  • Elam · 32.189, 48.258 · verse 6
  • House of the Forest of Lebanon · Today: in Jerusalem · 31.777, 35.234 · verse 8
  • City of David · 31.774, 35.236 · verse 9
  • Lower Pool · Today: in Jerusalem · 31.777, 35.234 · verse 9
  • Old Pool · Today: in Jerusalem · 31.777, 35.234 · verse 11

Only places identified with high confidence are shown (90% or more according to the scholarly sources compiled by OpenBible). Period map: DARE (Digital Atlas of the Roman Empire), CC BY 4.0; modern map: © OpenStreetMap contributors; places: OpenBible.info (CC BY 4.0).

Credits and license for this translation
Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™
Hausa: Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ (Bible) of Nigeria
copyright © 2009, 2020 Biblica, Inc.
Language: Hausa
Contributor: Biblica, Inc.
An sami wannan aiki a sauƙaƙe a ƙarƙashin lasisin Ƙasa da ƙasa na Lasisin Creative Commons Attribution-ShareAlike 4.0 na Ƙasa da ƙasa (CC BY-SA). Don a ga kwafin wannan lasisi, a ziyarci: http://creativecommons.org/licenses/by-sa/4.0 ko kuma a aika ta wasiƙa zuwa ga Creative Commons, PO Box 1866, Mountain View, CA 94042, USA.
“Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista ta hannun Biblica, Inc., kuma yin amfani da tambarin Biblica® na bukata rubutaccen izinin Biblica, Inc. A ƙarƙashin sharaɗin lasisin CC BY-SA, za ka iya kwafa ka kuma sāke raba wannan aikin da ba a gyaggyara ba muddin ba ka taɓa tambarin nan na Biblica® ba. Idan ka gyara wani kwafi ko ka juya wannan aiki, ta wurin kirkiro da aikin da aka samu, dole ne ka ka cire tambarin Biblica®. A aikin da aka samo, dole ne ka nuna canje-canjen da ka yi, ka kuma nuna aikin haka: “Ainihi aikin ta hannun Biblica, Inc. yana nan kyauta a www.biblica.com da buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki.”
Dole sharaɗin neman izini ya fita a kan kan magana ko kuma a shafi neman izinin aiki kamar haka:
Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™
Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc.
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™
Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc.
“Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini.
“Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission.
Dole kuma a samo aikin da ka yi daga ainihin aikin a ƙarƙashin wannan lasisi (CC BY-SA).
Idan za ka so ka sanar da Biblica, Inc. dangane da juyinka na wannan aiki, sai ka tuntuɓe mu a https://open.bible/contact-us.
This work is made available under the Creative Commons Attribution-ShareAlike 4‪.0 International License (CC BY-SA). To view a copy of this license, visit http://creativecommons.org/licenses/by-sa/4‪.0 or send a letter to Creative Commons, PO Box 1866, Mountain View, CA 94042, USA.
Biblica® is a trademark registered by Biblica, Inc., and use of the Biblica® trademark requires the written permission of Biblica, Inc. Under the terms of the CC BY-SA license, you may copy and redistribute this unmodified work as long as you keep the Biblica® trademark intact. If you modify a copy or translate this work, thereby creating a derivative work, you must remove the Biblica® trademark. On the derivative work, you must indicate what changes you have made and attribute the work as follows: “The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible.”
Notice of copyright must appear on the title or copyright page of the work as follows:
Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™
Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc.
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™
Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc.
“Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini.
“Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission.
You must also make your derivative work available under the same license (CC BY-SA).
If you would like to notify Biblica, Inc. regarding your translation of this work, please contact us at https://open.bible/contact-us.
This translation is made available to you under the terms of the
Creative Commons Attribution Share-Alike license 4.0.
You have permission to share and redistribute this Bible translation in any format and to make reasonable revisions and adaptations of this translation, provided that:
You include the above copyright and source information.
If you make any changes to the text, you must indicate that you did so in a way that makes it clear that the original licensor is not necessarily endorsing your changes.
If you redistribute this text, you must distribute your contributions under the same license as the original.
Pictures included with Scriptures and other documents on this site are licensed just for use with those Scriptures and documents.
For other uses, please contact the respective copyright owners.
Note that in addition to the rules above, revising and adapting God's Word involves a great responsibility to be true to God's Word. See Revelation 22:18-19.
2025-05-03

Source: http://ebible.org/hausa/ · eBible.org

Talk to us

Tell us where you read from, how the Bible has helped you, or what we could improve. We read every message.