Ezra 7
Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ · Tap a verse to see its cross-references.
Ezra ya zo Urushalima
1Bayan waɗannan abubuwa, a zamanin Artazerzes sarkin Farisa, sai Ezra ɗan Serahiya, ɗan Azariya, ɗan Hilkiya, 2ɗan Shallum, ɗan Zadok, ɗan Ahitub, 3ɗan Amariya, ɗan Azariya, ɗan Merahiyot, 4ɗan Zerahiya, ɗan Uzzi, ɗan Bukki, 5ɗan Abishuwa, ɗan Finehas, ɗan Eleyazar, ɗan Haruna babban firist. 6Shi Ezra ɗin ya zo daga Babilon. Shi malami ne ya kuma san Dokar Musa sosai wadda Ubangiji, Allah na Isra’ila ya bayar. Sarki ya ba shi duk abin da ya roƙa, gama Ubangiji Allahnsa yana tare da shi. 7Waɗansu Isra’ilawa, haɗe da firistoci, da Lawiyawa, da mawaƙa, da masu tsaron ƙofofi, da masu aiki a haikali su ma suka zo Urushalima a shekara ta bakwai a zamanin mulkin sarki Artazerzes.
8Ezra ya iso Urushalima a wata na biyar na shekara ta bakwai na kama mulkin sarkin. 9Ya fara tafiyarsa daga Babilon a rana ta farko ga watan farko, ya kuma iso Urushalima a rana ta farko ga watan biyar, gama alherin Allahnsa yana tare da shi. 10Gama Ezra ya miƙa kansa ga bincike da kuma kiyaye Dokar Ubangiji, da kuma koya wa Isra’ilawa dokoki da kuma umarnan Ubangiji.
Wasiƙar sarki Artazerzes zuwa ga Ezra
11Ga wasiƙar da sarki Artazerzes ya ba Ezra wanda yake firist da kuma malami, mutumin da yake cike da sani game da dokoki da kuma umarnan Ubangiji wa Isra’ila.
12Artazerzes, sarkin sarakuna.
Zuwa ga Ezra firist, malamin Dokar Allah na sama.
Gaisuwa.
13Yanzu ina ba da umarni cewa duk wani mutumin Isra’ilan da yake cikin mulkina, haɗe da firistoci, da Lawiyawa, da suke so su tafi tare da kai zuwa Urushalima za su iya tafiya. 14Sarki ne da mashawartansa guda bakwai suka aike ka don ka je ka ga halin da Yahuda da Urushalima suke ciki game da dokokin Allahnka, waɗanda suke a hannunka. 15Za ka kuma tafi da zinariya da azurfa waɗanda sarki da mashawartansa suka ba da kyautar yardar rai ga Allah na Isra’ila, wanda haikalinsa ke a Urushalima, 16haɗe da duk zinariya da azurfan da za ka iya samu a Babilon, da kuma duk bayarwar yardar rai daga mutane da firistoci, domin haikalin Allahnsu da yake a Urushalima. 17Ka tabbata ka yi amfani da kuɗin nan don ka sayi bijimai, da raguna, da ’yan raguna, da hadayu na gari, da na sha, ka kuma miƙa su a kan bagade na haikalin Allahnka a Urushalima.
18Sa’an nan kai da ’yan’uwanka Yahudawa ku yi abin da kuka ga ya fi kyau da sauran zinariya da azurfa ɗin bisa ga nufin Allah. 19Ka kai wa Allah na Urushalima duk kayan da aka ba ka amanarsu don yin sujada a haikalin Allahnka. 20Duk kuma wani abin da ake bukata domin haikalin Allahnka, daga ɗakunan ajiya sarki za ka fitar da kuɗin.
21Yanzu fa ni, Sarki Artazerzes, ina ba da umarni ga kowane ma’aji na Kewayen Kogin Yuferites su tanada duk abin da Ezra firist, wanda kuma yake malamin Dokar Allah na sama zai bukaci, 22har zuwa talenti ɗari na azurfa, da mudu ɗari na alkama, da garwa ɗari na ruwan inabi, da garwa ɗari na man zaitun, da kuma gishiri ba iyaka. 23A yi duk abin da Allah na sama ya ce don haikalin Allah na sama, sai a yi shi da himma. Me zai sa a jawo wa sarki da ’ya’yansa fushin Allah? 24Ku kuma san cewa, ba ku da ikon sa firistoci, da Lawiyawa, da mawaƙa, da masu tsaron ƙofofin haikali, da masu aiki a gidan Allah, ko waɗansu masu aiki a haikali su biya haraji, ko kuɗin shiga.
25Kai kuma Ezra, bisa ga hikimar da Allah ya ba ka, sai ka zaɓi mahukunta da alƙalai waɗanda za su zama masu yanke hukunci ga dukan mutanen Kewayen Kogin Yuferites, duk waɗanda suka san dokokin Allahnka, ka kuma koya wa duk waɗanda ba su san dokokin ba. 26Ba shakka duk wanda bai yi biyayya da dokokin Allahnka ba, da kuma dokokin sarki ba dole a yanke masa hukuncin kisa, ko hukuncin kora, ko hukuncin raba shi da mallakarsa, ko kuma hukuncin kulle shi a kurkuku.
27Yabo ya tabbata ga Ubangiji Allah na kakanninmu, ya taɓa zuciyar sarki don yă kawo ɗaukaka ga haikalin Allah a Urushalima ta wannan hanya. 28Wanda kuma ya sa na sami tagomashi a gaban sarki da mashawartansa, da kuma duk manyan masu muƙami nasa. Gama Ubangiji Allahna yana tare da ni, sai na sami ƙarfin hali na tattara shugabannin mutane daga Isra’ila, don mu tafi tare.

Did you know?
Ezra's Mission and the Decree of Artaxerxes
- Ezra is introduced with a priestly genealogy tracing back to Aaron through Hilkiah, the high priest who discovered the Book of the Law under King Josiah. Described as a skilled scribe, Ezra set his heart to study the Law of the Lord, practice it, and teach its decrees in Israel.Sources: Ezra · Hilkiah · the Bible text itself
- The Persian monarch Artaxerxes is traditionally identified as Artaxerxes I Longimanus, whose seventh year of reign corresponds to 458 BC. His royal decree granted Ezra broad authority to lead returning Israelites, appoint magistrates west of the Euphrates, and draw provisions and funds from the royal treasury.Sources: Artaxerxes · Persia · the Bible text itself
- Ezra and his fellow travelers set out from Babylon on the first day of the first month and arrived in Jerusalem on the first day of the fifth month. The narrative emphasizes that this four-month overland journey succeeded because the gracious hand of God was upon him.Sources: Ezra · the Bible text itself
Notes written with AI assistance from open sources (Theographic Bible Metadata, CC BY-SA 4.0; Easton’s Bible Dictionary, public domain) and reviewed before publishing.
Places in this chapter
- Babylon · 32.543, 44.422 · verse 1
- Jerusalem · 31.777, 35.234 · verses 1, 6, 7, 8, 9, 13, 14, 15, 16, 17, 19, 27, 28
- Persia · 34.806, 48.516 · verse 1
- Babylonia · 32.543, 44.422 · verses 6, 9, 16
- Beyond the River · 31.777, 35.234 · verses 21, 25
Only places identified with high confidence are shown (90% or more according to the scholarly sources compiled by OpenBible). Period map: DARE (Digital Atlas of the Roman Empire), CC BY 4.0; modern map: © OpenStreetMap contributors; places: OpenBible.info (CC BY 4.0).
Credits and license for this translation
Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Hausa: Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ (Bible) of Nigeria copyright © 2009, 2020 Biblica, Inc. Language: Hausa Contributor: Biblica, Inc. An sami wannan aiki a sauƙaƙe a ƙarƙashin lasisin Ƙasa da ƙasa na Lasisin Creative Commons Attribution-ShareAlike 4.0 na Ƙasa da ƙasa (CC BY-SA). Don a ga kwafin wannan lasisi, a ziyarci: http://creativecommons.org/licenses/by-sa/4.0 ko kuma a aika ta wasiƙa zuwa ga Creative Commons, PO Box 1866, Mountain View, CA 94042, USA. “Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista ta hannun Biblica, Inc., kuma yin amfani da tambarin Biblica® na bukata rubutaccen izinin Biblica, Inc. A ƙarƙashin sharaɗin lasisin CC BY-SA, za ka iya kwafa ka kuma sāke raba wannan aikin da ba a gyaggyara ba muddin ba ka taɓa tambarin nan na Biblica® ba. Idan ka gyara wani kwafi ko ka juya wannan aiki, ta wurin kirkiro da aikin da aka samu, dole ne ka ka cire tambarin Biblica®. A aikin da aka samo, dole ne ka nuna canje-canjen da ka yi, ka kuma nuna aikin haka: “Ainihi aikin ta hannun Biblica, Inc. yana nan kyauta a www.biblica.com da buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki.” Dole sharaɗin neman izini ya fita a kan kan magana ko kuma a shafi neman izinin aiki kamar haka: Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. “Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini. “Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission. Dole kuma a samo aikin da ka yi daga ainihin aikin a ƙarƙashin wannan lasisi (CC BY-SA). Idan za ka so ka sanar da Biblica, Inc. dangane da juyinka na wannan aiki, sai ka tuntuɓe mu a https://open.bible/contact-us. This work is made available under the Creative Commons Attribution-ShareAlike 4.0 International License (CC BY-SA). To view a copy of this license, visit http://creativecommons.org/licenses/by-sa/4.0 or send a letter to Creative Commons, PO Box 1866, Mountain View, CA 94042, USA. Biblica® is a trademark registered by Biblica, Inc., and use of the Biblica® trademark requires the written permission of Biblica, Inc. Under the terms of the CC BY-SA license, you may copy and redistribute this unmodified work as long as you keep the Biblica® trademark intact. If you modify a copy or translate this work, thereby creating a derivative work, you must remove the Biblica® trademark. On the derivative work, you must indicate what changes you have made and attribute the work as follows: “The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible.” Notice of copyright must appear on the title or copyright page of the work as follows: Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. “Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini. “Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission. You must also make your derivative work available under the same license (CC BY-SA). If you would like to notify Biblica, Inc. regarding your translation of this work, please contact us at https://open.bible/contact-us. This translation is made available to you under the terms of the Creative Commons Attribution Share-Alike license 4.0. You have permission to share and redistribute this Bible translation in any format and to make reasonable revisions and adaptations of this translation, provided that: You include the above copyright and source information. If you make any changes to the text, you must indicate that you did so in a way that makes it clear that the original licensor is not necessarily endorsing your changes. If you redistribute this text, you must distribute your contributions under the same license as the original. Pictures included with Scriptures and other documents on this site are licensed just for use with those Scriptures and documents. For other uses, please contact the respective copyright owners. Note that in addition to the rules above, revising and adapting God's Word involves a great responsibility to be true to God's Word. See Revelation 22:18-19. 2025-05-03
Source: http://ebible.org/hausa/ · eBible.org