Ezekiel 27
Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ · Tap a verse to see its cross-references.
Makoki domin Taya
1Maganar Ubangiji ta zo mini cewa, 2“Ɗan mutum, ka yi makoki domin Taya. 3Ka ce wa Taya, wadda take zaune a hanyar shiga zuwa teku, kasuwar masu yawa mutane a bakin teku, ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa,
“ ‘Kin ce, ya Taya,
“Ni kyakkyawa ce cikakkiya.”
4Manyan tekuna ne wurin zamanki;
maginanki sun sa kyanki ya zama cikakke.
5Sun yi dukan katakanki
daga itatuwan fir daga Senir;
sun kwaso itatuwan al’ul daga Lebanon
don su yi miki jigon jirgin ruwa.
6Da oak daga Bashan
suka yi sandunan tuƙan jirgin ruwa
da itatuwan kasharina daga bakin tekun Saifurus
suka yi daɓe jirgin ruwanki, suka kuma manne masa hauren giwa.
7Lilin mai kyau mai ado daga Masar ne filafilan jirgin ruwanki
suka kuma zama tutarki;
an yi tutarki da shuɗi da shunayya
daga bakin tekun Elisha.
8Mutanen Sidon da Arfad su ne matuƙan jirgin ruwanki;
gwanayenki, ya Taya, suna ciki a matsayi matuƙan jiragen ruwa.
9Masu hikima na Gebal suna ciki
a matsayin masu tattoshe mahaɗan katakon jirginki.
Dukan jiragen ruwa da matuƙansu
sukan zo wurinki don kasuwanci.
10“ ‘Mutanen Farisa, Lidiya da Fut
su ne suka zama sojoji a cikin mayaƙanki.
Sun rataye garkuwoyinsu da hulunan kwano a katangarki,
suna kawo miki daraja.
11Mutanen Arfad da Helek
sun yi tsaron katangar a kowace gefe;
mutanen Gammad
su ne a hasumiyoyinki.
Sun rataye garkuwoyinsu kewaye da katangarki;
sun sa kyanki ya zama cikakke.
12“ ‘Tarshish ta yi ciniki da ke saboda yawan wadatar kayayyakinki; sun sayi kayan cinikinki da azurfa, ƙarfe, kuza da dalma.
13“ ‘Girka, Tubal da Meshek sun yi kasuwanci da ke; sun sayi kayanki suka biya da bayi da kuma abubuwan da aka yi da tagulla.
14“ ‘Mutanen Bet Togarma sun sayi kayan cinikinki da dawakai, dawakan yaƙi da alfadarai.
15“ ‘Mutanen Dedan sun yi kasuwanci da ke, bakin teku masu yawa abokan cinikinki ne; sun biya ki da hauren giwa da katakon kanya.
16“ ‘Mutanen Aram sun yi ciniki da ke saboda yawan kayanki; suka sayi kayan cinikinki da zumurrudu, da shunayya, da kayan ado, da lilin mai taushi, da murjani, da yakutu.
17“ ‘Yahuda da Isra’ila sun yi kasuwanci da ke; sun sayi kayanki da alkama da Minnit da alawa, da zuma, da mai, da ganyaye masu ƙanshi.
18“ ‘Mutanen Damaskus sun ga abin da za ki iya bayarwa sai suka yi ciniki da ke, ta sayi kayanki da ruwan inabi daga Helbon, da ulu daga Zahar. 19Wedan da Yaban kusa da Uzal, suka sayi kayanki; wato gyararren ƙarfe da kayan yaji.
20“ ‘Mutanen Dedan sun sayi kayanki da sirdin zama a kan dawakai.
21“ ‘Mutanen Arabiya da dukan sarakunan Kedar abokan cinikinki ne; sun yi ciniki da ke suka sayi kayanki da ’yan raguna, da raguna, da awaki.
22“ ‘’Yan kasuwan Sheba da Ra’ama sun yi ciniki da ke; suka sayi kayanki da kayan yaji mafi kyau iri-iri, da duwatsu masu daraja iri-iri, da zinariya.
23“ ‘Haran, Kanne da Eden da kuma ’yan kasuwan Sheba, Assuriya da Kilmad sun yi ciniki da ke. 24A kasuwarki sun yi ciniki da ke suka sayar miki tufafi masu tsada, da na shuɗi, da masu ado, da dardumai masu ƙyalƙyali da kirtani, da igiyoyi waɗanda aka tuƙa da kyau.
25“ ‘Jiragen ruwan Tarshish sun zama
masu jigilar kayanki.
Kin cika da kaya masu nauyi
a tsakiyar teku.
26Matuƙan jiragenki sun kai ki
can cikin manyan tekuna.
Amma iskar gabas za tă farfasa ki kucu-kucu
a tsakiyar teku.
27Dukiyarki, cinikinki da kayan kasuwarki,
ma’aikatanki na jirgi, matuƙan jiragenki da masu tattoshe mahaɗan katakan jiragenki,
’yan kasuwarki da dukan sojojinki,
da kuma kowa da yake cikin jirgi
zai nutsa a tsakiyar teku
a ranar da jirginki zai nutse.
28Ƙasashen bakin teku za su girgiza
sa’ad da matuƙan jirginki suka yi kuka.
29Dukan waɗanda suke riƙe da matuƙi
za su ƙyale jiragensu;
ma’aikatan jirage da dukan matuƙan jirage
za su tsaya a bakin teku.
30Za su tā da muryarsu
su yi kuka mai zafi a kanki;
za su yayyafa ƙura a kawunansu,
su yi ta birgima a cikin toka.
31Za su aske kawunansu saboda ke
za su kuma sa tufafin makoki.
Za su yi kuka dominki su yi ɓacin rai
da kuma kuka mai zafi.
32Yayinda suke kuka a kanki kuwa,
za su yi makoki dominki suna cewa,
“Wa ya taɓa yin shiru kamar Taya,
kewaye da teku?”
33Sa’ad da kayan cinikinki suka tafi ƙasashen hayi,
kin gamsar da al’ummai masu yawa;
da dukiyarki masu yawa da kuma kayan cinikinki
kin azurtar da sarakunan duniya.
34Yanzu teku ta farfashe ki
cikin zurfafan ruwaye;
kayan cinikinki da dukan kamfaninki
sun nutse tare da ke.
35Dukan mazaunan bakin teku
sun giggice saboda masifarki;
sarakunansu sun tsorata ƙwarai
fuskokinsu kuwa sun yamutse don tsoro.
36’Yan kasuwa a cikin al’ummai suna yin miki tsaki;
kin zo ga mummunar ƙarshe
ba za ki ƙara kasancewa ba har abada.’ ”

Did you know?
The Lament and Commerce of Tyre
- In this lament, the prophet depicts the Phoenician maritime city of Tyre as a magnificent trading ship. Its structure is described as built with timbers of Lebanon cedar, cypress, and Bashan oak, outfitted with sails of Egyptian linen, and manned by mariners and craftsmen from coastal cities like Sidon, Arvad, and Gebal.Sources: the Bible text itself · Tyre · Lebanon · Arvad
- The chapter offers a detailed catalog of ancient Mediterranean and Near Eastern commerce. Tyre’s trade connections spanned from Tarshish in the west for metals like silver and tin, to Javan (Greece), the nomadic tribes of Kedar for livestock, and the merchants of Sheba in southern Arabia for gold, gems, and fine spices.Sources: the Bible text itself · Tarshish · Javan · Sheba
Notes written with AI assistance from open sources (Theographic Bible Metadata, CC BY-SA 4.0; Easton’s Bible Dictionary, public domain) and reviewed before publishing.
Places in this chapter
- Tyre · 33.271, 35.196 · verses 2, 3, 8, 32
- Lebanon · 33.540, 35.584 · verse 5
- Senir · Today: Mount Hermon · 33.400, 35.850 · verse 5
- Bashan · 32.781, 35.935 · verse 6
- Cyprus · 35.000, 33.000 · verse 6
- Egypt · 30.129, 31.308 · verse 7
- Sidon · Today: Sandikli archaeological site in Sidon · 33.561, 35.372 · verse 8
- Gebal · Today: Byblos · 34.119, 35.646 · verse 9
- Lud · Today: Lydia · 38.488, 28.040 · verse 10
- Persia · 34.806, 48.516 · verse 10
- Javan · Today: Ionia · 38.200, 27.500 · verse 13
- Meshech · Today: about 200 km around Gordion · 39.655, 31.994 · verse 13
- Tubal · Today: Tabal · 37.296, 36.254 · verse 13
- Syria · Today: Aram · 33.511, 36.306 · verse 16
- Damascus · 33.511, 36.306 · verse 18
- Dan · Today: Tel Dan · 33.249, 35.652 · verse 19
- Arabia · Today: Arabian Peninsula · 23.000, 46.000 · verse 21
- Kedar · 29.811, 39.868 · verse 21
- Sheba · 15.348, 44.206 · verses 22, 23
- Asshur · Today: Assur · 35.457, 43.263 · verse 23
- Eden · Today: Beth-eden · 36.701, 38.087 · verse 23
- Haran · Today: Harran · 36.864, 39.033 · verse 23
Only places identified with high confidence are shown (90% or more according to the scholarly sources compiled by OpenBible). Period map: DARE (Digital Atlas of the Roman Empire), CC BY 4.0; modern map: © OpenStreetMap contributors; places: OpenBible.info (CC BY 4.0).
Credits and license for this translation
Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Hausa: Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ (Bible) of Nigeria copyright © 2009, 2020 Biblica, Inc. Language: Hausa Contributor: Biblica, Inc. An sami wannan aiki a sauƙaƙe a ƙarƙashin lasisin Ƙasa da ƙasa na Lasisin Creative Commons Attribution-ShareAlike 4.0 na Ƙasa da ƙasa (CC BY-SA). Don a ga kwafin wannan lasisi, a ziyarci: http://creativecommons.org/licenses/by-sa/4.0 ko kuma a aika ta wasiƙa zuwa ga Creative Commons, PO Box 1866, Mountain View, CA 94042, USA. “Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista ta hannun Biblica, Inc., kuma yin amfani da tambarin Biblica® na bukata rubutaccen izinin Biblica, Inc. A ƙarƙashin sharaɗin lasisin CC BY-SA, za ka iya kwafa ka kuma sāke raba wannan aikin da ba a gyaggyara ba muddin ba ka taɓa tambarin nan na Biblica® ba. Idan ka gyara wani kwafi ko ka juya wannan aiki, ta wurin kirkiro da aikin da aka samu, dole ne ka ka cire tambarin Biblica®. A aikin da aka samo, dole ne ka nuna canje-canjen da ka yi, ka kuma nuna aikin haka: “Ainihi aikin ta hannun Biblica, Inc. yana nan kyauta a www.biblica.com da buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki.” Dole sharaɗin neman izini ya fita a kan kan magana ko kuma a shafi neman izinin aiki kamar haka: Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. “Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini. “Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission. Dole kuma a samo aikin da ka yi daga ainihin aikin a ƙarƙashin wannan lasisi (CC BY-SA). Idan za ka so ka sanar da Biblica, Inc. dangane da juyinka na wannan aiki, sai ka tuntuɓe mu a https://open.bible/contact-us. This work is made available under the Creative Commons Attribution-ShareAlike 4.0 International License (CC BY-SA). To view a copy of this license, visit http://creativecommons.org/licenses/by-sa/4.0 or send a letter to Creative Commons, PO Box 1866, Mountain View, CA 94042, USA. Biblica® is a trademark registered by Biblica, Inc., and use of the Biblica® trademark requires the written permission of Biblica, Inc. Under the terms of the CC BY-SA license, you may copy and redistribute this unmodified work as long as you keep the Biblica® trademark intact. If you modify a copy or translate this work, thereby creating a derivative work, you must remove the Biblica® trademark. On the derivative work, you must indicate what changes you have made and attribute the work as follows: “The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible.” Notice of copyright must appear on the title or copyright page of the work as follows: Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. “Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini. “Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission. You must also make your derivative work available under the same license (CC BY-SA). If you would like to notify Biblica, Inc. regarding your translation of this work, please contact us at https://open.bible/contact-us. This translation is made available to you under the terms of the Creative Commons Attribution Share-Alike license 4.0. You have permission to share and redistribute this Bible translation in any format and to make reasonable revisions and adaptations of this translation, provided that: You include the above copyright and source information. If you make any changes to the text, you must indicate that you did so in a way that makes it clear that the original licensor is not necessarily endorsing your changes. If you redistribute this text, you must distribute your contributions under the same license as the original. Pictures included with Scriptures and other documents on this site are licensed just for use with those Scriptures and documents. For other uses, please contact the respective copyright owners. Note that in addition to the rules above, revising and adapting God's Word involves a great responsibility to be true to God's Word. See Revelation 22:18-19. 2025-05-03
Source: http://ebible.org/hausa/ · eBible.org