Ezekiel 25
Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ · Tap a verse to see its cross-references.
Annabci a kan Ammon
1Maganar Ubangiji ta zo mini cewa, 2“Ɗan mutum, ka fuskanci wajen Ammonawa ka kuma yi annabci a kansu. 3Ka ce musu, ‘Ku ji maganar Ubangiji Mai Iko Duka. Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa domin kun ce “Yauwa” a kan wuri mai tsarkina sa’ad da aka ƙazantar da shi da kuma a kan ƙasar Isra’ila sa’ad da aka mai da ita kufai da lokacin da aka kai mutanen Yahuda bautar talala, 4saboda haka zan ba da ku ga mutanen Gabas abin mallaka. Za su kafa sansanoninsu su yi tentunansu a cikinku; za su ci ’ya’yan itatuwanku su kuma sha madararku. 5Zan mai da Rabba wurin kiwo don raƙuma, Ammon kuma wurin hutu don tumaki. Sa’an nan za ku san cewa ni ne Ubangiji. 6Gama ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa domin kun tafa hannuwanku kuka kuma buga ƙafafunku, kuna farin ciki don nuna dukan ƙiyayyarku a kan ƙasar Isra’ila, 7saboda haka zan miƙa hannuna gāba da ku in kuma ba da ku ganima ga al’ummai. Zan datse ku daga al’ummai in kuma kore ku daga ƙasashe. Zan hallaka ku, za ku kuwa san cewa ni ne Ubangiji.’ ”
Annabci a kan Mowab
8“Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa, ‘Domin Mowab da Seyir sun ce, “Duba, gidan Yahuda ta zama sauran al’ummai,” 9saboda haka zan buɗe ƙofar shiga Mowab, farawa daga garuruwan da suke kan iyaka, Bet-Yeshimot, Ba’al-Meyon da Kiriyatayim, darajar ƙasar. 10Zan ba da Mowabawa tare da Ammonawa ga mutanen Gabas abin mallaka, don kada a ƙara tuna da Ammonawa a cikin al’ummai; 11zan hukunta Mowabawa. Ta haka za su san cewa ni ne Ubangiji.’ ”
Annabci a kan Edom
12“Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa, ‘Domin Edom ya ɗauki wa kanta fansa a kan gida Yahuda, ta yi babban laifi ta wurin yin haka, 13saboda haka ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa zan miƙa hannuna a kan Edom in kashe mutanenta da dabbobinsu. Zan sa ta zama kufai, kuma tun daga Teman har zuwa Dedan za a kashe su da takobi. 14Zan ɗau fansa a kan Edom ta hannun mutanena Isra’ila, za su kuwa hukunta Edom bisa ga fushina da hasalata; za su san sakayyata, in ji Ubangiji Mai Iko Duka.’ ”
Annabci a kan Filistiya
15“Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa, ‘Domin Filistiyawa sun yi sakayya, suka ɗauki fansa da mugunta a zukatansu, da kuma daɗaɗɗen ƙiyayya sun nemi su hallaka Yahuda, 16saboda haka ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa ina gab da miƙa hannuna a kan Filistiyawa, zan kuwa datse Keretawa in kuma hallaka waɗanda suka rage a bakin teku. 17Zan yi musu babbar sakayya da hukunci mai tsanani cikin hasalata. Sa’an nan za su san cewa ni ne Ubangiji, sa’ad da na ɗauki fansa a kansu.’ ”

Did you know?
Judgments on Surrounding Nations
- Ammon lay east of the Jordan River with Rabbah as its chief city. Ezekiel prophesied that because Ammon gloated over the fall of Jerusalem and the profanation of the sanctuary, its territory and capital would be handed over to nomadic tribes from the East as pastures for camels and sheep.Sources: the Bible text itself · Ammon · Rabbah · East
- The neighboring regions of Moab and Mount Seir—the rugged hill country inhabited by the descendants of Esau—were rebuked for claiming Judah was just like all the other nations. Ezekiel warned that their frontier cities would be left exposed and given as a possession to peoples from the East.Sources: the Bible text itself · Moab · Seir · Esau (Edom)
- The chapter concludes with divine judgments against Edom and the Philistines, condemning both peoples for acting out of ancient hostility and taking malicious vengeance against Judah during its time of calamity.Sources: the Bible text itself · Edom
Notes written with AI assistance from open sources (Theographic Bible Metadata, CC BY-SA 4.0; Easton’s Bible Dictionary, public domain) and reviewed before publishing.
Places in this chapter
- Ammon · 31.955, 35.934 · verses 2, 3, 5, 10
- East · Today: region around Amman · 31.955, 35.934 · verses 4, 10
- Rabbah · Today: Amman · 31.955, 35.934 · verse 5
- Moab · Today: Moab 1 · 31.181, 35.701 · verses 8, 9, 10, 11
- Edom · 30.746, 35.604 · verses 12, 13, 14
- Philistia · 31.664, 34.546 · verse 15
Only places identified with high confidence are shown (90% or more according to the scholarly sources compiled by OpenBible). Period map: DARE (Digital Atlas of the Roman Empire), CC BY 4.0; modern map: © OpenStreetMap contributors; places: OpenBible.info (CC BY 4.0).
Credits and license for this translation
Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Hausa: Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ (Bible) of Nigeria copyright © 2009, 2020 Biblica, Inc. Language: Hausa Contributor: Biblica, Inc. An sami wannan aiki a sauƙaƙe a ƙarƙashin lasisin Ƙasa da ƙasa na Lasisin Creative Commons Attribution-ShareAlike 4.0 na Ƙasa da ƙasa (CC BY-SA). Don a ga kwafin wannan lasisi, a ziyarci: http://creativecommons.org/licenses/by-sa/4.0 ko kuma a aika ta wasiƙa zuwa ga Creative Commons, PO Box 1866, Mountain View, CA 94042, USA. “Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista ta hannun Biblica, Inc., kuma yin amfani da tambarin Biblica® na bukata rubutaccen izinin Biblica, Inc. A ƙarƙashin sharaɗin lasisin CC BY-SA, za ka iya kwafa ka kuma sāke raba wannan aikin da ba a gyaggyara ba muddin ba ka taɓa tambarin nan na Biblica® ba. Idan ka gyara wani kwafi ko ka juya wannan aiki, ta wurin kirkiro da aikin da aka samu, dole ne ka ka cire tambarin Biblica®. A aikin da aka samo, dole ne ka nuna canje-canjen da ka yi, ka kuma nuna aikin haka: “Ainihi aikin ta hannun Biblica, Inc. yana nan kyauta a www.biblica.com da buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki.” Dole sharaɗin neman izini ya fita a kan kan magana ko kuma a shafi neman izinin aiki kamar haka: Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. “Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini. “Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission. Dole kuma a samo aikin da ka yi daga ainihin aikin a ƙarƙashin wannan lasisi (CC BY-SA). Idan za ka so ka sanar da Biblica, Inc. dangane da juyinka na wannan aiki, sai ka tuntuɓe mu a https://open.bible/contact-us. This work is made available under the Creative Commons Attribution-ShareAlike 4.0 International License (CC BY-SA). To view a copy of this license, visit http://creativecommons.org/licenses/by-sa/4.0 or send a letter to Creative Commons, PO Box 1866, Mountain View, CA 94042, USA. Biblica® is a trademark registered by Biblica, Inc., and use of the Biblica® trademark requires the written permission of Biblica, Inc. Under the terms of the CC BY-SA license, you may copy and redistribute this unmodified work as long as you keep the Biblica® trademark intact. If you modify a copy or translate this work, thereby creating a derivative work, you must remove the Biblica® trademark. On the derivative work, you must indicate what changes you have made and attribute the work as follows: “The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible.” Notice of copyright must appear on the title or copyright page of the work as follows: Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. “Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini. “Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission. You must also make your derivative work available under the same license (CC BY-SA). If you would like to notify Biblica, Inc. regarding your translation of this work, please contact us at https://open.bible/contact-us. This translation is made available to you under the terms of the Creative Commons Attribution Share-Alike license 4.0. You have permission to share and redistribute this Bible translation in any format and to make reasonable revisions and adaptations of this translation, provided that: You include the above copyright and source information. If you make any changes to the text, you must indicate that you did so in a way that makes it clear that the original licensor is not necessarily endorsing your changes. If you redistribute this text, you must distribute your contributions under the same license as the original. Pictures included with Scriptures and other documents on this site are licensed just for use with those Scriptures and documents. For other uses, please contact the respective copyright owners. Note that in addition to the rules above, revising and adapting God's Word involves a great responsibility to be true to God's Word. See Revelation 22:18-19. 2025-05-03
Source: http://ebible.org/hausa/ · eBible.org