Nations Bible

Deuteronomy 5

Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ · Tap a verse to see its cross-references.

Dokoki goma

1Musa ya tattara dukan Isra’ila ya ce,

Ku ji, ya Isra’ila, ƙa’idodi da dokokin da na furta a kunnuwanku a yau. Ku koye su, ku kuma tabbata kun bi su. 2Ubangiji Allahnmu ya yi alkawari da mu a Horeb. 3Ba da kakanninmu ba ne Ubangiji ya yi wannan alkawari, amma da mu ne, da dukanmu waɗanda muke da rai a yau. 4Ubangiji ya yi magana fuska da fuska da ku daga wuta a kan dutse. 5(A wannan lokaci na tsaya tsakanin Ubangiji da ku, don in furta muku maganar Ubangiji, domin kun ji tsoron wutar, ba ku kuwa hau dutsen ba.)

Ya ce,

6“Ni ne Ubangiji Allahnka, wanda ya fitar da ku daga Masar, daga ƙasar bauta.

7“Ba za ka kasance da waɗansu alloli a gabana ba.

8Ba za ka yi wa kanka gunki, ko wata siffar abin da take a sama a bisa, ko siffar abin da yake a duniya a ƙasa, ko siffar abin da yake a cikin ruwa a ƙarƙashin ƙasa ba. 9Ba za ka rusuna musu, ko ka yi musu sujada ba. Gama Ni, Ubangiji Allahnka, Allah ne mai kishi, nakan hukunta ’ya’ya saboda zunuban iyaye har tsara ta uku da ta huɗu na waɗanda suka ƙi ni. 10Amma nakan nuna ƙauna ga dubban tsararraki na waɗanda suke ƙaunata, suke kuma kiyaye dokokina.

11Ba za ka yi amfani da sunan Ubangiji Allahnka a banza ba, gama Ubangiji zai ba wa duk mai yin amfani da sunansa a banza laifi.

12Ka kiyaye ranar Asabbaci ta wurin kiyaye ta da tsarki, yadda Ubangiji Allahnka ya umarce ka. 13Kwanaki shida za ka yi aiki, ka kuma yi dukan aikinka, 14amma rana ta bakwai, Asabbaci ne ga Ubangiji Allahnka. A kanta ba za ka yi wani aiki ba, ko kai, ko ɗanka, ko ’yarka, ko bawanka, ko baiwarka, ko saniyarka, ko jakinka, ko wani daga dabbobinka, ko baƙo a ƙofofinka, don bayinka maza da mata su ma su huta, kamar ka. 15Ka tuna fa, dā kai bawa ne a ƙasar Masar amma Ubangiji Allahnka ya fitar da kai daga can da iko da kuma ƙarfi. Saboda haka Ubangiji Allahnka ya umarce ka ka kiyaye ranar Asabbaci.

16Ka ba da girma ga mahaifinka da mahaifiyarka, yadda Ubangiji Allahnka ya umarce ka, don ka yi tsawon rai, ka kuma sami zaman lafiya a ƙasar da Ubangiji Allahnka yake ba ka.

17Kada ka yi kisankai.

18Kada ka yi zina.

19Kada ka yi sata.

20Kada ka ba da shaidar ƙarya a kan maƙwabcinka.

21Kada ka yi ƙyashin matar maƙwabcinka. Kada kuma ka yi sha’awar gidan maƙwabcinka, ko gonarsa, ko bayinsa maza da mata, ko saniyarka, ko jakinsa, ko dai wani abin da yake na maƙwabtanka.”

22Waɗannan su ne dokokin da Ubangiji ya furta da babbar murya ga taronku gaba ɗaya, a can dutse ta tsakiyar wuta, girgije da kuma baƙin duhu; bai kuma ƙara kome ba. Sa’an nan ya rubuta su a kan alluna biyu na dutse, ya kuma ba ni su.

23Sa’ad da kuka ji muryar daga duhu, yayinda dutsen yana cin wuta, dukan manyan kabilanku da dattawanku suka zo wurina. 24Kuka kuma ce, “ Ubangiji Allahnmu ya nuna mana ɗaukakarsa da zatinsa, mun kuma ji muryarsa a tsakiyar wutar. A yau mun ga cewa mutum zai iya rayu idan ma Allah ya yi magana da shi. 25Amma yanzu, don me za mu mutu? Wannan wuta mai girma za tă cinye mu, za mu kuwa mutu in muka ci gaba da jin muryar Ubangiji Allahnmu. 26Gama wanda ɗan adam ne ya taɓa jin muryar Allah mai rai yana magana daga wuta, kamar yadda muka ji, ya kuma tsira? 27Kai, ka matsa kusa, ka saurara ga dukan abin da Ubangiji Allahnmu ya faɗa. Sa’an nan ka faɗa mana dukan abin da Ubangiji Allahnmu ya faɗa maka. Za mu saurara, mu kuma yi biyayya.”

28Ubangiji ya ji ku, sa’ad da kuka yi magana da ni, sai Ubangiji ya ce mini, “Na ji abin da wannan mutane suka faɗa maka. Abin da suka faɗa daidai ne. 29Kash, da a ce zukatansu za su zama masu tsorona, su kuma kiyaye dukan dokokina kullum mana, saboda kome yă zama da lafiya gare su, da kuma ’ya’yansu har abada!

30“Je, ka faɗa musu su koma tentunansu. 31Kai kuwa ka tsaya a nan tare da ni saboda in ba ka umarnai, ƙa’idodi da kuma dokoki duka, da za ka koya musu don su bi a ƙasar da nake ba su, su mallaka.”

32Sai ku yi hankali don ku yi abin da Ubangiji Allahnku ya umarce ku; kada ku juya dama ko hagu. 33Ku yi tafiya cikin dukan hanyar da Ubangiji Allahnku ya umarce ku, saboda ku zauna, ku yi nasara, ku kuma yi tsawon rai a ƙasar da za ku mallaka.

Artistic illustration — an interpretation, not a historical record.

Did you know?

The Covenant and the Ten Commandments

  • In Deuteronomy, the mountain where the covenant and commandments were given is called Horeb. Horeb refers to the broader mountain range of which Sinai was a peak, situated beside a spacious plain where the Israelites could camp.Sources: Horeb · the Bible text itself
  • In Deuteronomy's account of the Sabbath commandment, the requirement of rest is explicitly tied to Israel's history of slavery in Egypt. Because the Israelites had been liberated from forced labor, their servants, foreigners, and working animals were also granted complete rest on the seventh day.Sources: the Bible text itself
  • Moses served as an intermediary between God and the people because the tribal heads and elders feared they would die if they continued hearing the divine voice from the fire and deep darkness. They asked Moses to go near, receive the remaining statutes, and report them to the assembly.Sources: the Bible text itself

Notes written with AI assistance from open sources (Theographic Bible Metadata, CC BY-SA 4.0; Easton’s Bible Dictionary, public domain) and reviewed before publishing.

Places in this chapter

  • Mount Horeb · Today: Jebel Musa · 28.540, 33.973 · verse 2
  • Egypt · 30.129, 31.308 · verses 6, 15

Only places identified with high confidence are shown (90% or more according to the scholarly sources compiled by OpenBible). Period map: DARE (Digital Atlas of the Roman Empire), CC BY 4.0; modern map: © OpenStreetMap contributors; places: OpenBible.info (CC BY 4.0).

Credits and license for this translation
Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™
Hausa: Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ (Bible) of Nigeria
copyright © 2009, 2020 Biblica, Inc.
Language: Hausa
Contributor: Biblica, Inc.
An sami wannan aiki a sauƙaƙe a ƙarƙashin lasisin Ƙasa da ƙasa na Lasisin Creative Commons Attribution-ShareAlike 4.0 na Ƙasa da ƙasa (CC BY-SA). Don a ga kwafin wannan lasisi, a ziyarci: http://creativecommons.org/licenses/by-sa/4.0 ko kuma a aika ta wasiƙa zuwa ga Creative Commons, PO Box 1866, Mountain View, CA 94042, USA.
“Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista ta hannun Biblica, Inc., kuma yin amfani da tambarin Biblica® na bukata rubutaccen izinin Biblica, Inc. A ƙarƙashin sharaɗin lasisin CC BY-SA, za ka iya kwafa ka kuma sāke raba wannan aikin da ba a gyaggyara ba muddin ba ka taɓa tambarin nan na Biblica® ba. Idan ka gyara wani kwafi ko ka juya wannan aiki, ta wurin kirkiro da aikin da aka samu, dole ne ka ka cire tambarin Biblica®. A aikin da aka samo, dole ne ka nuna canje-canjen da ka yi, ka kuma nuna aikin haka: “Ainihi aikin ta hannun Biblica, Inc. yana nan kyauta a www.biblica.com da buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki.”
Dole sharaɗin neman izini ya fita a kan kan magana ko kuma a shafi neman izinin aiki kamar haka:
Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™
Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc.
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™
Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc.
“Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini.
“Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission.
Dole kuma a samo aikin da ka yi daga ainihin aikin a ƙarƙashin wannan lasisi (CC BY-SA).
Idan za ka so ka sanar da Biblica, Inc. dangane da juyinka na wannan aiki, sai ka tuntuɓe mu a https://open.bible/contact-us.
This work is made available under the Creative Commons Attribution-ShareAlike 4‪.0 International License (CC BY-SA). To view a copy of this license, visit http://creativecommons.org/licenses/by-sa/4‪.0 or send a letter to Creative Commons, PO Box 1866, Mountain View, CA 94042, USA.
Biblica® is a trademark registered by Biblica, Inc., and use of the Biblica® trademark requires the written permission of Biblica, Inc. Under the terms of the CC BY-SA license, you may copy and redistribute this unmodified work as long as you keep the Biblica® trademark intact. If you modify a copy or translate this work, thereby creating a derivative work, you must remove the Biblica® trademark. On the derivative work, you must indicate what changes you have made and attribute the work as follows: “The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible.”
Notice of copyright must appear on the title or copyright page of the work as follows:
Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™
Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc.
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™
Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc.
“Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini.
“Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission.
You must also make your derivative work available under the same license (CC BY-SA).
If you would like to notify Biblica, Inc. regarding your translation of this work, please contact us at https://open.bible/contact-us.
This translation is made available to you under the terms of the
Creative Commons Attribution Share-Alike license 4.0.
You have permission to share and redistribute this Bible translation in any format and to make reasonable revisions and adaptations of this translation, provided that:
You include the above copyright and source information.
If you make any changes to the text, you must indicate that you did so in a way that makes it clear that the original licensor is not necessarily endorsing your changes.
If you redistribute this text, you must distribute your contributions under the same license as the original.
Pictures included with Scriptures and other documents on this site are licensed just for use with those Scriptures and documents.
For other uses, please contact the respective copyright owners.
Note that in addition to the rules above, revising and adapting God's Word involves a great responsibility to be true to God's Word. See Revelation 22:18-19.
2025-05-03

Source: http://ebible.org/hausa/ · eBible.org

Talk to us

Tell us where you read from, how the Bible has helped you, or what we could improve. We read every message.