Nations Bible

2 Kings 3

Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ · Tap a verse to see its cross-references.

Mowab ta yi tawaye

1Yoram, ɗan Ahab ya zama sarki Isra’ila, a Samariya, a shekara ta goma sha takwas ta mulkin Yehoshafat, sarkin Yahuda, ya kuma yi mulki shekara goma sha biyu. 2Yoram ya aikata mugunta a gaban Ubangiji, amma ba kamar yadda mahaifinsa da mahaifiyarsa suka yi ba. Ya kawar da dutsen tsarkin Ba’al wanda mahaifinsa ya yi. 3Duk da haka ya manne wa zunuban Yerobowam ɗan Nebat, wanda ya sa Isra’ila ta aikata, bai rabu da su ba.

4Mesha, sarkin Mowab yana kiwon tumaki, ya kuma zama tilas yă biya haraji ga sarkin Isra’ila. Saboda haka yakan ba da ’yan tumaki dubu ɗari, da kuma gashin raguna dubu ɗari. 5Amma bayan mutuwar Ahab, sai sarkin Mowab ya yi wa sarkin Isra’ila tawaye. 6To, a lokacin, Sarki Yoram ya tashi daga Samariya, ya tattara sojoji daga dukan Isra’ila. 7Ya kuma aika da wannan saƙo ga Yehoshafat sarkin Yahuda cewa, “Sarkin Mowab ya yi mini tawaye. Za ka tafi tare da ni mu yaƙi Mowab?”

Sai sarkin Yahuda ya ce, “I, ina shirye mu tafi. Ai, sojojina sojojinka ne, dawakaina kuma dawakanka ne.”

8Ya ƙara da cewa, “Wace hanya za mu bi?”

Sai Yoram ya amsa ya ce, “Ta hanyar jejin Edom.”

9Saboda haka sarkin Isra’ila ya fita tare da sarkin Yahuda, da kuma sarkin Edom. Da suka yi kwana bakwai suna ta zagawa, sai sojoji da dabbobi suka rasa ruwan sha.

10Sai sarkin Isra’ila ya ce, “Mene! Ubangiji ya kira mu sarakunan nan uku don kawai yă ba da mu ga Mowab ne?”

11Amma Yehoshafat ya yi tambaya ya ce, “Babu wani annabin Ubangiji a nan da za mu nemi nufin Ubangiji ta wurinsa?”

Wani hafsan sarkin Isra’ila ya amsa ya ce, “Ai, akwai Elisha ɗan Shafat, wanda dā ya yi wa Iliya hidima.”

12Yehoshafat ya ce, “Maganar Ubangiji tana tare da shi.” Saboda haka sarkin Isra’ila da Yehoshafat da kuma sarkin Edom suka tafi wurin Elisha.

13Elisha ya ce wa sarkin Isra’ila, “Ina ruwana da kai? Tafi wurin annabawan mahaifinka da annabawa mahaifiyarka.”

Sai sarkin Isra’ila ya ce, “A’a, ai Ubangiji ne ya kira mu, mu sarakunan nan uku don yă bashe mu ga Mowab.”

14Sai Elisha ya ce, “Muddin Ubangiji Maɗaukaki yana a raye, wanda nake bauta, da ba don ina ganin girman Yehoshafat Sarkin Yahuda ba, da ko kallonka ba zan yi ba. 15Amma yanzu, a kawo mini makaɗin garaya.”

Yayinda makaɗin garayan yake kiɗa, ikon Ubangiji ya sauko a kan Elisha 16ya kuma ce, “Ga abin da Ubangiji ya ce, zan cika kwarin nan da tafkunan ruwa. 17Gama ga abin da Ubangiji ya ce, ko da yake babu iska, ko ruwan sama, duk da haka kwarin nan zai cika da ruwa, har ku da dabbobinku da kuma sauran dabbobi ku sha. 18Wannan abu mai sauƙi ne a wurin Ubangiji; zai kuma ba da Mowab a gare ku. 19Za ku ci kowane birni mai katanga, da kowane babban gari. Za ku sare kowane itace mai kyau, ku kuma tattoshe maɓuɓɓugan ruwa. Za ku kuma yi amfani da duwatsu ku lalatar da kowace gona mai kyau.”

20Kashegari, daidai lokacin hadaya, sai ga ruwa yana gangarowa daga gefen Edom! Ƙasar kuwa ta cika da ruwa.

21To, dukan Mowabawa suka ji cewa sarakuna suna tafe don su yaƙe su; saboda haka aka kira kowane namiji, babba da yaro, wanda ya isa ɗaukan makami, aka jera su a bakin iyaka. 22Da suka tashi da sassafe, rana tana haska ruwa. Sai ruwan ya yi ja kamar jini a idanun Mowabawan da suke a ƙetare. 23Sai suka ce, “Jini ne! Ba shakka sarakunan nan sun yaƙe juna, suka karkashe juna. Ya Mowabawa, mu tafi mu kwashi ganima!”

24Amma da Mowabawa suka isa sansanin Isra’ila, sai Isra’ilawa suka taso suka auka musu har sai da suka gudu. Isra’ilawa kuwa suka kai musu hari, suka karkashe Mowabawa. 25Suka ragargaza garuruwa, kowane mutum kuwa ya jefa dutse a kowane gona mai kyau har sai da aka rufe gonakin gaba ɗaya. Suka tattoshe duk maɓulɓulan ruwa, suka kuma sare duk itace mai kyau. Kir Hareset ne kaɗai aka bari tare da duwatsunsa yadda suke, amma mutanen da suke da majajjawa suka yi wa birnin zobe, suka kai masa hari shi ma.

26Da sarkin Mowab ya ga yaƙi ya rinjaye shi, sai ya ɗauki mutane masu takobi ɗari bakwai, ya ratsa zuwa wajen sarkin Edom, amma ba su yi nasara ba. 27Sa’an nan ya ɗauki ɗansa na fari, wanda zai gāje shi, ya yi hadaya da shi a bisa katangan birnin. Isra’ilawa suka firgita ƙwarai; sai suka janye suka koma ƙasarsu.

Did you know?

War with Moab and Elisha's Prophecy

  • Mesha, the king of Moab, was a sheep breeder who rendered an annual tribute of 100,000 lambs and the wool of 100,000 rams to the king of Israel. Following the death of King Ahab, Mesha revolted, leading Ahab's son Joram to mobilize his army and form an alliance with King Jehoshaphat of Judah and the king of Edom.Sources: the Bible text itself · Joram · Kir-hareseth
  • After a seven-day march through the Desert of Edom left the allied armies and their animals without water, they sought counsel from the prophet Elisha. At Elisha's request, a harpist played, and the prophet announced that dry trenches in the valley would fill with water without wind or rain.Sources: the Bible text itself · Elisha · Edom
  • The morning sun reflecting off the newly pooled water made it appear as red as blood to the Moabites, leading them to assume the allied kings had slaughtered one another. The resulting Moabite charge ended in disaster, culminating in the siege of the fortress of Kir-hareseth, where Mesha sacrificed his firstborn son on the city wall.Sources: the Bible text itself · Kir-hareseth · Moab

Notes written with AI assistance from open sources (Theographic Bible Metadata, CC BY-SA 4.0; Easton’s Bible Dictionary, public domain) and reviewed before publishing.

Places in this chapter

  • Samaria · 32.276, 35.195 · verses 1, 6
  • Moab · Today: Moab 1 · 31.181, 35.701 · verses 4, 5, 7, 10, 13, 18, 21, 22, 23, 24, 26, 27
  • Edom · 30.746, 35.604 · verses 8, 9, 12, 20, 26

Only places identified with high confidence are shown (90% or more according to the scholarly sources compiled by OpenBible). Period map: DARE (Digital Atlas of the Roman Empire), CC BY 4.0; modern map: © OpenStreetMap contributors; places: OpenBible.info (CC BY 4.0).

Credits and license for this translation
Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™
Hausa: Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ (Bible) of Nigeria
copyright © 2009, 2020 Biblica, Inc.
Language: Hausa
Contributor: Biblica, Inc.
An sami wannan aiki a sauƙaƙe a ƙarƙashin lasisin Ƙasa da ƙasa na Lasisin Creative Commons Attribution-ShareAlike 4.0 na Ƙasa da ƙasa (CC BY-SA). Don a ga kwafin wannan lasisi, a ziyarci: http://creativecommons.org/licenses/by-sa/4.0 ko kuma a aika ta wasiƙa zuwa ga Creative Commons, PO Box 1866, Mountain View, CA 94042, USA.
“Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista ta hannun Biblica, Inc., kuma yin amfani da tambarin Biblica® na bukata rubutaccen izinin Biblica, Inc. A ƙarƙashin sharaɗin lasisin CC BY-SA, za ka iya kwafa ka kuma sāke raba wannan aikin da ba a gyaggyara ba muddin ba ka taɓa tambarin nan na Biblica® ba. Idan ka gyara wani kwafi ko ka juya wannan aiki, ta wurin kirkiro da aikin da aka samu, dole ne ka ka cire tambarin Biblica®. A aikin da aka samo, dole ne ka nuna canje-canjen da ka yi, ka kuma nuna aikin haka: “Ainihi aikin ta hannun Biblica, Inc. yana nan kyauta a www.biblica.com da buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki.”
Dole sharaɗin neman izini ya fita a kan kan magana ko kuma a shafi neman izinin aiki kamar haka:
Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™
Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc.
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™
Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc.
“Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini.
“Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission.
Dole kuma a samo aikin da ka yi daga ainihin aikin a ƙarƙashin wannan lasisi (CC BY-SA).
Idan za ka so ka sanar da Biblica, Inc. dangane da juyinka na wannan aiki, sai ka tuntuɓe mu a https://open.bible/contact-us.
This work is made available under the Creative Commons Attribution-ShareAlike 4‪.0 International License (CC BY-SA). To view a copy of this license, visit http://creativecommons.org/licenses/by-sa/4‪.0 or send a letter to Creative Commons, PO Box 1866, Mountain View, CA 94042, USA.
Biblica® is a trademark registered by Biblica, Inc., and use of the Biblica® trademark requires the written permission of Biblica, Inc. Under the terms of the CC BY-SA license, you may copy and redistribute this unmodified work as long as you keep the Biblica® trademark intact. If you modify a copy or translate this work, thereby creating a derivative work, you must remove the Biblica® trademark. On the derivative work, you must indicate what changes you have made and attribute the work as follows: “The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible.”
Notice of copyright must appear on the title or copyright page of the work as follows:
Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™
Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc.
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™
Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc.
“Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini.
“Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission.
You must also make your derivative work available under the same license (CC BY-SA).
If you would like to notify Biblica, Inc. regarding your translation of this work, please contact us at https://open.bible/contact-us.
This translation is made available to you under the terms of the
Creative Commons Attribution Share-Alike license 4.0.
You have permission to share and redistribute this Bible translation in any format and to make reasonable revisions and adaptations of this translation, provided that:
You include the above copyright and source information.
If you make any changes to the text, you must indicate that you did so in a way that makes it clear that the original licensor is not necessarily endorsing your changes.
If you redistribute this text, you must distribute your contributions under the same license as the original.
Pictures included with Scriptures and other documents on this site are licensed just for use with those Scriptures and documents.
For other uses, please contact the respective copyright owners.
Note that in addition to the rules above, revising and adapting God's Word involves a great responsibility to be true to God's Word. See Revelation 22:18-19.
2025-05-03

Source: http://ebible.org/hausa/ · eBible.org

Talk to us

Tell us where you read from, how the Bible has helped you, or what we could improve. We read every message.