Nations Bible

2 Kings 19

Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ · Tap a verse to see its cross-references.

An yi annabcin ceton Urushalima

1Da sarki Hezekiya ya ji haka, sai ya kyakketa tufafinsa, ya sa tufafin makoki, ya shiga haikalin Ubangiji. 2Ya aiki Eliyakim sarkin fada, Shebna marubuci da shugabannin firistoci, dukansu sanye da tufafin makoki, zuwa wurin annabi Ishaya ɗan Amoz. 3Suka ce masa, “Hezekiya ya ce, yau ranar wahala ce, da ta cin mutunci, da ta shan kunya, ga shi, ’ya’ya suna gab da a haife su, amma ba ƙarfin da za a yi yunƙuri a haife su. 4Mai yiwuwa Ubangiji Allahnka ya ji dukan maganganun sarkin yaƙi, wanda maigidansa, sarkin Assuriya, ya aiko don yă rena Allah mai rai. Bari Ubangiji Allahnka yă tsawata masa saboda maganar da ya ji. Saboda haka ka yi addu’a domin raguwar da har yanzu suke a raye.”

5Da fadawan sarki Hezekiya suka isa wurin Ishaya, 6Ishaya ya ce musu, “Ku faɗa wa maigidanku, in ji Ubangiji, ‘Kada abin da ka ji yă firgita ka, wato, waɗannan kalmomin da karen nan na sarkin Assuriya ya yi saɓo da su. 7Saurara! Zan sa masa wani ruhun da zai sa yă ji wata jita-jitar da za tă sa yă koma ƙasarsa. A can zan sa a kashe shi da takobi a ƙasarsa.’ ”

8Da sarkin yaƙin ya ji cewa sarkin Assuriya ya bar Lakish, sai ya janye, ya kuma iske sarkin yana yaƙi da Libna.

9To, Sennakerib ya sami labari cewa Tirhaka, mutumin Kush sarkin Masar, yana zuwa masa da yaƙi. Saboda haka ya sāke aika manzanni zuwa wurin Hezekiya cewa, 10“Ku faɗa wa Hezekiya sarkin Yahuda, kada ka bar allahn da kake dogara gare shi yă ruɗe ka cewa, ‘Urushalima ba za tă fāɗi a hannun sarkin Assuriya ba.’ 11Ba shakka ka riga ka ji abin da sarkin Assuriya ya yi da dukan ƙasashe, yana hallaka su gaba ɗaya. Kai kuwa kana ji za a cece ka? 12Allolin al’umman da kakannina suka hallaka, sun cece su ne, allolin Gozan, da na Haran, da na Rezef, da kuma na mutane Eden da suke a Tel Assar? 13Ina sarkin Hamat, da sarkin Arfad, da sarkin birnin Sefarfayim, ko na Hena da kuma na Iffa?”

Addu’ar Hezekiya

14Hezekiya ya karɓi wasiƙar daga manzannin ya karanta. Sa’an nan ya tashi ya tafi haikalin Ubangiji ya shimfiɗa wasiƙar a gaban Ubangiji. 15Hezekiya kuwa ya yi addu’a ga Ubangiji ya ce, “Ya Ubangiji, Allah na Isra’ila, wanda yake zaune tsakanin kerubobi, kai kaɗai ne Allah bisa dukan mulkokin duniya. Kai ka yi sama da duniya. 16Ka kasa kunne, ya Ubangiji, ka ji; ka buɗe idanunka ya Ubangiji ka gani; ka saurari kalmomin da Sennakerib ya aiko don yă yi wa Allah mai rai ba’a.

17“Da gaske ne, ya Ubangiji, cewa sarakunan Assuriya sun hallakar da waɗannan al’ummai da ƙasashensu. 18Sun jefar da allolinsu cikin wuta, suka hallaka su, gama ba alloli ba ne, katakai ne da kuma duwatsu, ayyukan hannuwan mutane. 19To, ya Ubangiji Allahnmu, ka cece mu daga hannunsa, don dukan mulkokin duniya su san cewa kai kaɗai, ya Ubangiji ne Allah.”

Ishaya ya yi annabcin fāɗuwar Sennakerib

20Sai Ishaya ɗan Amoz ya aika da saƙo zuwa wurin Hezekiya cewa, “Ga abin da Ubangiji, Allah na Isra’ila ya ce, na ji addu’arka game da Sennakerib sarkin Assuriya. 21Ga abin da Ubangiji yana cewa game da shi,

“ ‘Budurwar Sihiyona

ta rena ka tana kuma yin maka ba’a.

Diyar Urushalima

ta kaɗa kanta yayinda kake gudu.

22Wane ne ka zaga, ka kuma yi masa saɓo?

Wa kake gāba da shi har ka ɗaga muryarka,

har ka tā da idanunka da fahariya?

Kana gāba da Mai Tsarki na Isra’ila!

23Ta wurin manzanninka

ka tara wa Ubangiji zagi.

Ka kuma ce,

“Da yawa kekunan yaƙina

na haye kan ƙwanƙolin duwatsu,

wurin mafi tsawo na Lebanon.

Na sassare itacen al’ul nasa mafi tsawo

mafi daraja na itacen fir nasa.

Na ratsa har can tsakiyar kurmi,

mafi kyau na kurminsa.

24Na tona rijiyoyi a ƙasashen waje

na kuma sha ruwa a can.

Da tafin ƙafafuna

na busar da dukan rafuffukan Masar.”

25“ ‘Ba ka taɓa ji ba?

Tun da daɗewa na ƙaddara haka.

Tuntuni kuwa na shirya shi;

yanzu kuma na sa ya faru,

cewa ka mai da birane masu katanga

tarin duwatsu.

26Ƙarfin mutanensu ya tsiyaye,

suka razana aka kuma kunyata su.

Suna kama da tsirai a gona,

kamar sabon toho

kamar ciyawa mai tohuwa bisa rufin ɗaki

wanda ya bushe saboda zafi, kafin yă yi girma.

27“ ‘Amma na san wurin zamanka

da fitarka da shigarka

da yadda kake fushi da ni.

28Domin kana fushi da ni

reninka ya iso kunnuwata,

zan sa ƙugiyata a hancinka

da linzamina a bakinka,

zan kuma sa ka koma

a ta hanyar da ka zo.’

29“Wannan zai zama alama a gare ka, ya Hezekiya,

“Bana, za ku ci amfanin gonar da ya tsira da kansa,

baɗi kuma amfanin gonar da ya tsiro daga na bara.

Amma a shekara ta uku, za ku yi shuki, ku kuma girbe,

ku dasa gonakin inabi, ku kuma ci ’ya’yansa.

30Sau ɗaya kuma ragowar masarautar Yahuda

za tă yi saiwoyi a ƙasa ta kuma ba da ’ya’ya a bisa.

31Gama daga Urushalima za a sami ragowa,

daga Dutsen Sihiyona kuma za a sami waɗanda suka tsira.

Himmar Ubangiji Maɗaukaki za tă cika wannan.

32“Saboda haka ga abin da Ubangiji ya ce game da sarkin Assuriya,

“Ba zai shiga birnin nan ba

ko yă harba kibiya a nan.

Ba zai kusace ta da garkuwa

ko yă yi mata zoben yaƙi ba.

33Ta hanyar da ya zo ne zai koma;

ba zai shiga birnin nan ba, in ji Ubangiji.

34Zan kāre birnin nan in cece ta,

saboda kaina da kuma bawana Dawuda.”

35A daren nan mala’ikan Ubangiji ya fita ya kashe dakaru dubu ɗari da tamanin da biyu a sansanin Assuriyawa. Da mutane suka farka da safe, sai ga gawawwaki ko’ina. 36Saboda haka Sennakerib sarkin Assuriya ya tā da sansanin ya kuma janye. Ya koma Ninebe ya zauna a can.

37Wata rana yayinda yake sujada a haikalin Nisrok, allahnsa, sai ’ya’yansa maza, Adrammelek da Sharezer suka kashe shi da takobi, suka gudu zuwa ƙasar Ararat. Sai Esar-Haddon ɗansa ya gāje shi.

Artistic illustration — an interpretation, not a historical record.

Did you know?

Jerusalem Delivered from Assyria

  • When Hezekiah received Sennacherib's threatening letter, he entered the temple and spread it out before God, affirming that while the gods of other conquered nations were merely wood and stone, the God of Israel is the maker of heaven and earth.Sources: the Bible text itself · Hezekiah
  • Sennacherib sent his second threatening message to Jerusalem while fighting against Libnah after departing Lachish, prompted by reports that Tirhakah, the king of Cush, was marching out to oppose him.Sources: the Bible text itself · Tirhakah · Libnah · Lachish
  • After the angel of the Lord struck 185,000 soldiers in the Assyrian camp, Sennacherib retreated to Nineveh, where his own sons later assassinated him with swords inside the temple of his god Nisroch.Sources: the Bible text itself · Sennacherib

Notes written with AI assistance from open sources (Theographic Bible Metadata, CC BY-SA 4.0; Easton’s Bible Dictionary, public domain) and reviewed before publishing.

Places in this chapter

  • Assyria · 36.359, 43.153 · verses 4, 6, 8, 10, 11, 17, 20, 32, 35, 36, 37
  • Jerusalem · 31.777, 35.234 · verses 8, 9, 10, 21, 31, 32
  • Lachish · Today: Tell ed Duweir · 31.565, 34.849 · verse 8
  • Cush · Today: Cush 1 · 16.935, 33.751 · verse 9
  • Eden · Today: Beth-eden · 36.701, 38.087 · verse 12
  • Haran · Today: Harran · 36.864, 39.033 · verse 12
  • Hamath · Today: Hama · 35.136, 36.750 · verse 13
  • Zion · Today: Jerusalem · 31.777, 35.234 · verse 21
  • Lebanon · 33.540, 35.584 · verse 23
  • Mount Carmel · 32.672, 35.023 · verse 23
  • Egypt · 30.129, 31.308 · verse 24
  • Mount Zion · 31.772, 35.229 · verse 31
  • Nineveh · 36.359, 43.153 · verse 36
  • Ararat · Today: Urartu · 39.703, 44.300 · verse 37

Only places identified with high confidence are shown (90% or more according to the scholarly sources compiled by OpenBible). Period map: DARE (Digital Atlas of the Roman Empire), CC BY 4.0; modern map: © OpenStreetMap contributors; places: OpenBible.info (CC BY 4.0).

Credits and license for this translation
Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™
Hausa: Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ (Bible) of Nigeria
copyright © 2009, 2020 Biblica, Inc.
Language: Hausa
Contributor: Biblica, Inc.
An sami wannan aiki a sauƙaƙe a ƙarƙashin lasisin Ƙasa da ƙasa na Lasisin Creative Commons Attribution-ShareAlike 4.0 na Ƙasa da ƙasa (CC BY-SA). Don a ga kwafin wannan lasisi, a ziyarci: http://creativecommons.org/licenses/by-sa/4.0 ko kuma a aika ta wasiƙa zuwa ga Creative Commons, PO Box 1866, Mountain View, CA 94042, USA.
“Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista ta hannun Biblica, Inc., kuma yin amfani da tambarin Biblica® na bukata rubutaccen izinin Biblica, Inc. A ƙarƙashin sharaɗin lasisin CC BY-SA, za ka iya kwafa ka kuma sāke raba wannan aikin da ba a gyaggyara ba muddin ba ka taɓa tambarin nan na Biblica® ba. Idan ka gyara wani kwafi ko ka juya wannan aiki, ta wurin kirkiro da aikin da aka samu, dole ne ka ka cire tambarin Biblica®. A aikin da aka samo, dole ne ka nuna canje-canjen da ka yi, ka kuma nuna aikin haka: “Ainihi aikin ta hannun Biblica, Inc. yana nan kyauta a www.biblica.com da buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki.”
Dole sharaɗin neman izini ya fita a kan kan magana ko kuma a shafi neman izinin aiki kamar haka:
Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™
Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc.
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™
Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc.
“Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini.
“Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission.
Dole kuma a samo aikin da ka yi daga ainihin aikin a ƙarƙashin wannan lasisi (CC BY-SA).
Idan za ka so ka sanar da Biblica, Inc. dangane da juyinka na wannan aiki, sai ka tuntuɓe mu a https://open.bible/contact-us.
This work is made available under the Creative Commons Attribution-ShareAlike 4‪.0 International License (CC BY-SA). To view a copy of this license, visit http://creativecommons.org/licenses/by-sa/4‪.0 or send a letter to Creative Commons, PO Box 1866, Mountain View, CA 94042, USA.
Biblica® is a trademark registered by Biblica, Inc., and use of the Biblica® trademark requires the written permission of Biblica, Inc. Under the terms of the CC BY-SA license, you may copy and redistribute this unmodified work as long as you keep the Biblica® trademark intact. If you modify a copy or translate this work, thereby creating a derivative work, you must remove the Biblica® trademark. On the derivative work, you must indicate what changes you have made and attribute the work as follows: “The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible.”
Notice of copyright must appear on the title or copyright page of the work as follows:
Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™
Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc.
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™
Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc.
“Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini.
“Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission.
You must also make your derivative work available under the same license (CC BY-SA).
If you would like to notify Biblica, Inc. regarding your translation of this work, please contact us at https://open.bible/contact-us.
This translation is made available to you under the terms of the
Creative Commons Attribution Share-Alike license 4.0.
You have permission to share and redistribute this Bible translation in any format and to make reasonable revisions and adaptations of this translation, provided that:
You include the above copyright and source information.
If you make any changes to the text, you must indicate that you did so in a way that makes it clear that the original licensor is not necessarily endorsing your changes.
If you redistribute this text, you must distribute your contributions under the same license as the original.
Pictures included with Scriptures and other documents on this site are licensed just for use with those Scriptures and documents.
For other uses, please contact the respective copyright owners.
Note that in addition to the rules above, revising and adapting God's Word involves a great responsibility to be true to God's Word. See Revelation 22:18-19.
2025-05-03

Source: http://ebible.org/hausa/ · eBible.org

Talk to us

Tell us where you read from, how the Bible has helped you, or what we could improve. We read every message.