1 Samuel 19
Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ · Tap a verse to see its cross-references.
Shawulu ya yi ƙoƙari yă kashe Dawuda
1Shawulu ya gaya wa ɗansa Yonatan da ma’aikatansa su kashe Dawuda. Amma Yonatan yana son Dawuda sosai. 2Sai ya gargaɗe shi ya ce, “Mahaifina Shawulu yana neman hanyar da zai kashe ka. Ka kula da kanka gobe da safe, ka tafi wani wuri ka ɓuya. 3Zan je in tsaya da mahaifina a fili inda kake, zan yi masa magana game da kai. Zan kuma gaya maka abin da na ji.”
4Yonatan ya yi magana mai kyau a kan Dawuda a wajen mahaifinsa ya ce, “Kada sarki yă yi wani mummunan abu wa bawansa Dawuda, gama bai yi maka wani abu marar kyau ba. Abin da ya yi ya amfane ka ƙwarai da gaske. 5Ya yi kasai da ransa sa’ad da ya kashe Bafilistin nan. Ubangiji ya ba wa dukan Isra’ila babban nasara, ka gani, ka kuma yi farin ciki. Don me za ka ci mutuncin amintaccen mutum kamar Dawuda ta wurin kashe shi ba tare da wani dalili ba?”
6Shawulu ya saurari Yonatan sai ya rantse ya ce, “Muddin Ubangiji yana a raye, ba za a kashe Dawuda ba.”
7Ta haka Yonatan ya kira Dawuda ya gaya masa dukan maganarsu. Ya kawo shi wurin Shawulu, Dawuda kuwa ya zauna tare da Shawulu kamar dā.
8Wani yaƙi ya sāke tashi, Dawuda kuwa ya fita ya yaƙi Filistiyawa, ya kai musu hari mai tsanani, sai da suka gudu a gabansa.
9Amma mugun ruhu daga Ubangiji ya sauko wa Shawulu yayinda yana zaune a cikin gidansa da māshi a hannunsa. Yayinda Dawuda yake bugan molo, 10Shawulu ya yi ƙoƙari yă kafe shi da bango da māshinsa, amma Dawuda ya goce sa’ad da Shawulu jefa māshin a bango. A daren nan Dawuda ya nemi hanya ya gudu.
11Shawulu ya aiki mutane zuwa gidan Dawuda su yi gadin gidan, su kuma kashe Dawuda. Amma Mikal matar Dawuda ta gargaɗe Dawuda, ta ce, “In ba ka gudu a daren nan ba, kashegari za a kashe ka.” 12Haka kuwa Mikal ta sauko da Dawuda ta taga ya gudu, ya tsere. 13Sai Mikal ta ɗauki gunki ta kwantar da shi a gādo, ta sa masa gashin akuya a kansa, sai ta rufe da mayafi.
14Da Shawulu ya aiki mutane su kama Dawuda. Mikal ta ce, “Ba shi da lafiya.”
15Sai Shawulu ya sāke aiki mutanen su ga Dawuda, ya ce musu, “Ku kawo shi a gādonsa domin in kashe shi.” 16Amma da mutanen suka shiga sai suka ga gunkin a gadon, a wajen kan kuwa akwai gashin akuya.
17Shawulu ya ce wa Mikal, “Don me kika ruɗe ni har kika bar maƙiyina ya gudu ya tsere?”
Mikal ta ce masa, “Ya ce mini, ‘Idan ban bar shi ya tafi ba, zai kashe ni?’ ”
18Da Dawuda ya gudu ya tsere, sai ya tafi wurin Sama’ila a Rama ya gaya masa dukan abin da Shawulu ya yi masa. Da shi da Sama’ila suka tafi Nayiwot suka zauna a can. 19Shawulu ya sami labari cewa, “Dawuda yana Nayiwot a Rama.” 20Sai ya aiki mutane su je su kamo Dawuda, amma da suka ga ƙungiyar annabawa suna annabci tare da Sama’ila shugabansu a tsaye, sai Ruhun Allah ya sauko wa mutanen Shawulu, su ma suka fara yin annabci. 21Shawulu ya sami labari game da wannan, sai ya sāke aiken waɗansu da yawa. Su ma suka shiga yin annabci. Shawulu ya sāke aiken mutane sau na uku, su kuma suka shiga yin annabci. 22A ƙarshe, shi da kansa ya tashi ya tafi Rama. Ya bi ta babban rijiyar ruwan Seku. A can ya yi tambaya ya ce, “Ina Sama’ila da Dawuda suke?”
Suka ce, “Suna cikin Nayiwot a Rama.”
23Saboda haka Shawulu ya tafi Nayiwot a Rama, amma Ruhun Allah ya sauko masa, shi ma ya yi tafiya yana annabci har sai da ya isa Nayiwot. 24Ya tuttuɓe rigunarsa, ya kuma yi annabci a gaban Sama’ila. Ya kwanta tsirara dukan yini da dukan dare. Abin da ya sa ke nan mutane suke cewa, “Shawulu ma yana cikin annabawa ne?”

Did you know?
David's Escapes from Saul
- When Saul sent messengers to kill David at home, David's wife Michal helped him escape through a window. She then disguised a household idol in his bed with goat hair and clothing to delay the messengers and buy David time to flee.Sources: the Bible text itself · Michal
- David fled to the prophet Samuel at Ramah and went with him to Naioth. The name Naioth means dwellings and refers to a settlement near Ramah where a community of prophets lived under Samuel's leadership.Sources: the Bible text itself · Naioth · Samuel
- While pursuing David toward Ramah, Saul stopped to ask for information at the large cistern of Secu, a place located on a hill between Gibeah and Ramah.Sources: the Bible text itself · Secu
Notes written with AI assistance from open sources (Theographic Bible Metadata, CC BY-SA 4.0; Easton’s Bible Dictionary, public domain) and reviewed before publishing.
Places in this chapter
- Secu · Today: between Gibeah and Ramah · 31.937, 35.145 · verse 22
Only places identified with high confidence are shown (90% or more according to the scholarly sources compiled by OpenBible). Period map: DARE (Digital Atlas of the Roman Empire), CC BY 4.0; modern map: © OpenStreetMap contributors; places: OpenBible.info (CC BY 4.0).
Credits and license for this translation
Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Hausa: Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ (Bible) of Nigeria copyright © 2009, 2020 Biblica, Inc. Language: Hausa Contributor: Biblica, Inc. An sami wannan aiki a sauƙaƙe a ƙarƙashin lasisin Ƙasa da ƙasa na Lasisin Creative Commons Attribution-ShareAlike 4.0 na Ƙasa da ƙasa (CC BY-SA). Don a ga kwafin wannan lasisi, a ziyarci: http://creativecommons.org/licenses/by-sa/4.0 ko kuma a aika ta wasiƙa zuwa ga Creative Commons, PO Box 1866, Mountain View, CA 94042, USA. “Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista ta hannun Biblica, Inc., kuma yin amfani da tambarin Biblica® na bukata rubutaccen izinin Biblica, Inc. A ƙarƙashin sharaɗin lasisin CC BY-SA, za ka iya kwafa ka kuma sāke raba wannan aikin da ba a gyaggyara ba muddin ba ka taɓa tambarin nan na Biblica® ba. Idan ka gyara wani kwafi ko ka juya wannan aiki, ta wurin kirkiro da aikin da aka samu, dole ne ka ka cire tambarin Biblica®. A aikin da aka samo, dole ne ka nuna canje-canjen da ka yi, ka kuma nuna aikin haka: “Ainihi aikin ta hannun Biblica, Inc. yana nan kyauta a www.biblica.com da buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki.” Dole sharaɗin neman izini ya fita a kan kan magana ko kuma a shafi neman izinin aiki kamar haka: Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. “Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini. “Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission. Dole kuma a samo aikin da ka yi daga ainihin aikin a ƙarƙashin wannan lasisi (CC BY-SA). Idan za ka so ka sanar da Biblica, Inc. dangane da juyinka na wannan aiki, sai ka tuntuɓe mu a https://open.bible/contact-us. This work is made available under the Creative Commons Attribution-ShareAlike 4.0 International License (CC BY-SA). To view a copy of this license, visit http://creativecommons.org/licenses/by-sa/4.0 or send a letter to Creative Commons, PO Box 1866, Mountain View, CA 94042, USA. Biblica® is a trademark registered by Biblica, Inc., and use of the Biblica® trademark requires the written permission of Biblica, Inc. Under the terms of the CC BY-SA license, you may copy and redistribute this unmodified work as long as you keep the Biblica® trademark intact. If you modify a copy or translate this work, thereby creating a derivative work, you must remove the Biblica® trademark. On the derivative work, you must indicate what changes you have made and attribute the work as follows: “The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible.” Notice of copyright must appear on the title or copyright page of the work as follows: Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. “Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini. “Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission. You must also make your derivative work available under the same license (CC BY-SA). If you would like to notify Biblica, Inc. regarding your translation of this work, please contact us at https://open.bible/contact-us. This translation is made available to you under the terms of the Creative Commons Attribution Share-Alike license 4.0. You have permission to share and redistribute this Bible translation in any format and to make reasonable revisions and adaptations of this translation, provided that: You include the above copyright and source information. If you make any changes to the text, you must indicate that you did so in a way that makes it clear that the original licensor is not necessarily endorsing your changes. If you redistribute this text, you must distribute your contributions under the same license as the original. Pictures included with Scriptures and other documents on this site are licensed just for use with those Scriptures and documents. For other uses, please contact the respective copyright owners. Note that in addition to the rules above, revising and adapting God's Word involves a great responsibility to be true to God's Word. See Revelation 22:18-19. 2025-05-03
Source: http://ebible.org/hausa/ · eBible.org