Nations Bible

1 Chronicles 21

Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ · Tap a verse to see its cross-references.

Dawuda ya ƙidaya mayaƙansa

1Sai Shaiɗan ya tashi gāba da Isra’ila, ya zuga Dawuda ya ƙidaya Isra’ila. 2Saboda haka Dawuda ya ce wa Yowab da shugabannin mayaƙa, “Ku tafi ku ƙidaya Isra’ilawa daga Beyersheba zuwa Dan. Ku kawo mini labarin saboda in san su nawa ne.”

3Amma Yowab ya amsa ya ce, “ Ubangiji ya riɓaɓɓanya mayaƙansa fiye da sau ɗari. Ranka yă daɗe sarki, dukansu ba bayin shugabana ba ne? Me ya sa ranka yă daɗe yake so yă yi haka? Me zai sa ka kawo laifi a kan Isra’ila?”

4Amma sarki ya nace a kan maganar da ya yi wa Yowab. Sai Yowab ya tashi ya tafi cikin dukan Isra’ila, ya kewaye sa’an nan ya dawo Urushalima. 5Yowab ya ba labarin yawan mayaƙan wa Dawuda. A cikin Isra’ila akwai mutum miliyon da dubu ɗari ɗaya waɗanda za su iya riƙe takobi, haɗe da dubu ɗari huɗu da saba’in a Yahuda.

6Amma Yowab bai haɗa da mutanen Lawi da na Benyamin a ƙidayar ba, domin bai ji daɗin umarnin sarki ba.

7Wannan umarnin mugu ne a gaban Allah; saboda haka ya hukunta Isra’ila.

8Sai Dawuda ya ce wa Allah, “Na yi zunubi ƙwarai ta wurin yin wannan. Yanzu, na roƙe ka, ka ɗauke laifin bawanka. Na yi wauta sosai.”

9Sai Ubangiji ya ce wa Gad, mai duba na Dawuda, 10“Tafi ka faɗa wa Dawuda, ‘Ga abin da Ubangiji ya ce ina ba ka abubuwa uku. Ka zaɓi ɗaya daga cikinsu don in aikata a kanka.’ ”

11Saboda haka Gad ya tafi wurin Dawuda ya ce masa, “Ga abin da Ubangiji ya ce, ‘Ka yi zaɓi, 12shekara uku na yunwa, wata uku na shan ɗibga a gaban abokan gābanka, sa’ad da za su bi suna kakkashe ku, ko kuwa kwana uku na takobin Ubangiji, ranakun annoba a cikin ƙasar, mala’ikan Ubangiji zai hallaka kowane sashe na Isra’ila.’ Yanzu sai ka yanke shawara yadda zan amsa wa wanda ya aiko ni.”

13Dawuda ya ce wa Gad, “Na shiga uku. Bari in fāɗa a hannuwan Ubangiji, gama jinƙansa yana da girma sosai; amma kada ka bari in fāɗa a hannuwan mutane.”

14Sai Ubangiji ya aiko da annoba a kan Isra’ila, mutane duba saba’in na Isra’ila suka mutu. 15Allah kuwa ya aiki mala’ika yă hallaka Urushalima. Amma yayinda mala’ikan yana gab da yin haka, sai Ubangiji ya gani ya kuma yi nadama saboda masifar, sai ya ce wa mala’ikan wanda yake hallaka mutane, “Ya isa! Janye hannunka.” Mala’ikan Ubangiji kuwa yana tsaye a masussukar Ornan mutumin Yebus.

16Sai Dawuda ya ɗaga ido ya ga mala’ikan Ubangiji tsaye tsakanin sama da duniya, da takobi a zāre a hannunsa ya miƙa a kan Urushalima. Sai Dawuda da dattawa, saye da rigunan makoki suka fāɗi rubda jiki.

17Dawuda ya ce wa Allah, “Ba ni ba ne na umarta a ƙidaya mayaƙan? Ni ne wanda ya yi zunubin da kuma abin da ba daidai ba. Waɗannan dai tumaki ne. Me suka yi? Ya Ubangiji Allahna, bari hannunka ya fāɗi a kaina da kuma iyalina, amma kada ka bar wannan annoba ya kasance a kan mutanenka.”

18Sa’an nan mala’ikan Ubangiji ya umarci Gad yă faɗa wa Dawuda yă haura yă gina bagade wa Ubangiji a masussukar Ornan mutumin Yebus. 19Saboda haka Dawuda ya haura cikin biyayya ga maganar da Allah ya yi da sunan Ubangiji.

20Yayinda Ornan yake sussukar alkama, sai ya juya ya ga mala’ika; ’ya’yansa maza guda huɗu da suke tare da shi suka ɓuya. 21Sai Dawuda ya kusato, sa’ad da Ornan ya duba sai ya gan shi, ya bar masussukar ya rusuna a gaban Dawuda da fuskarsa har ƙasa.

22Dawuda ya ce wa Ornan, “Ka ba ni masussukarka saboda in gina bagade wa Ubangiji, don annobar da take kan mutane tă daina. Ka sayar mini ita a cikakken kuɗinta.”

23Ornan ya ce wa Dawuda, “Ka karɓa! Bari ranka yă daɗe, sarki yă yi duk abin da ya ga ya yi masa kyau. Duba, zan ba da shanu domin hadaya ta ƙonawa, da itacen sussuka, da kuma alkama domin hadaya ta gari. Zan ba da dukan wannan.”

24Amma Sarki Dawuda ya amsa wa Ornan ya ce, “A’a, na nace zan biya cikakken kuɗinta. Ba zan karɓi abinka kawai don Ubangiji ba, ko in miƙa hadaya ta ƙonawar da ba tă ci mini wani abu ba.”

25Saboda haka Dawuda ya biya Ornan shekel ɗari shida na zinariya saboda wurin. 26Dawuda ya gina bagade wa Ubangiji a can ya kuma miƙa hadayu na ƙonawa da hadayu na salama, Ubangiji kuwa ya amsa masa ta wurin wuta daga sama a kan bagaden hadaya ta ƙonawa.

27Sa’an nan Ubangiji ya yi magana ga mala’ikan, ya kuma mayar da takobinsa a kube. 28A lokacin, sa’ad da Dawuda ya ga cewa Ubangiji ya amsa masa a masussukar Ornan mutumin Yebus, sai ya miƙa hadayu a can. 29Tabanakul na Ubangiji da Musa ya yi a hamada, da kuma bagaden hadaya ta ƙonawa a lokacin suna a tudun Gibeyon. 30Amma Dawuda bai iya zuwa gabansa don yă yi tambaya ga Allah ba, gama yana jin tsoron takobin mala’ikan Ubangiji.

Artistic illustration — an interpretation, not a historical record.

Did you know?

David's Census and Ornan's Threshing Floor

  • The phrase from Beersheba to Dan was a traditional Hebrew expression denoting the full extent of the Promised Land from south to north, covering a distance of approximately 144 miles.Sources: the Bible text itself · Beersheba
  • The threshing floor of Ornan the Jebusite on Mount Moriah, which David insisted on buying at full price to offer sacrifices, later became the site where Solomon built the temple in Jerusalem.Sources: the Bible text itself · Ornan
  • Although the wilderness tabernacle made by Moses and its bronze altar were located at the high place in Gibeon at this time, David sacrificed at Ornan's threshing floor because he was terrified of the angel of the Lord.Sources: the Bible text itself · Gibeon · Moses

Notes written with AI assistance from open sources (Theographic Bible Metadata, CC BY-SA 4.0; Easton’s Bible Dictionary, public domain) and reviewed before publishing.

Places in this chapter

  • Dan · Today: Tel Dan · 33.249, 35.652 · verse 2
  • Jerusalem · 31.777, 35.234 · verses 4, 15, 16
  • Gibeon · Today: El Jib · 31.847, 35.183 · verse 29

Only places identified with high confidence are shown (90% or more according to the scholarly sources compiled by OpenBible). Period map: DARE (Digital Atlas of the Roman Empire), CC BY 4.0; modern map: © OpenStreetMap contributors; places: OpenBible.info (CC BY 4.0).

Credits and license for this translation
Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™
Hausa: Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ (Bible) of Nigeria
copyright © 2009, 2020 Biblica, Inc.
Language: Hausa
Contributor: Biblica, Inc.
An sami wannan aiki a sauƙaƙe a ƙarƙashin lasisin Ƙasa da ƙasa na Lasisin Creative Commons Attribution-ShareAlike 4.0 na Ƙasa da ƙasa (CC BY-SA). Don a ga kwafin wannan lasisi, a ziyarci: http://creativecommons.org/licenses/by-sa/4.0 ko kuma a aika ta wasiƙa zuwa ga Creative Commons, PO Box 1866, Mountain View, CA 94042, USA.
“Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista ta hannun Biblica, Inc., kuma yin amfani da tambarin Biblica® na bukata rubutaccen izinin Biblica, Inc. A ƙarƙashin sharaɗin lasisin CC BY-SA, za ka iya kwafa ka kuma sāke raba wannan aikin da ba a gyaggyara ba muddin ba ka taɓa tambarin nan na Biblica® ba. Idan ka gyara wani kwafi ko ka juya wannan aiki, ta wurin kirkiro da aikin da aka samu, dole ne ka ka cire tambarin Biblica®. A aikin da aka samo, dole ne ka nuna canje-canjen da ka yi, ka kuma nuna aikin haka: “Ainihi aikin ta hannun Biblica, Inc. yana nan kyauta a www.biblica.com da buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki.”
Dole sharaɗin neman izini ya fita a kan kan magana ko kuma a shafi neman izinin aiki kamar haka:
Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™
Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc.
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™
Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc.
“Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini.
“Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission.
Dole kuma a samo aikin da ka yi daga ainihin aikin a ƙarƙashin wannan lasisi (CC BY-SA).
Idan za ka so ka sanar da Biblica, Inc. dangane da juyinka na wannan aiki, sai ka tuntuɓe mu a https://open.bible/contact-us.
This work is made available under the Creative Commons Attribution-ShareAlike 4‪.0 International License (CC BY-SA). To view a copy of this license, visit http://creativecommons.org/licenses/by-sa/4‪.0 or send a letter to Creative Commons, PO Box 1866, Mountain View, CA 94042, USA.
Biblica® is a trademark registered by Biblica, Inc., and use of the Biblica® trademark requires the written permission of Biblica, Inc. Under the terms of the CC BY-SA license, you may copy and redistribute this unmodified work as long as you keep the Biblica® trademark intact. If you modify a copy or translate this work, thereby creating a derivative work, you must remove the Biblica® trademark. On the derivative work, you must indicate what changes you have made and attribute the work as follows: “The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible.”
Notice of copyright must appear on the title or copyright page of the work as follows:
Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™
Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc.
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™
Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc.
“Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini.
“Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission.
You must also make your derivative work available under the same license (CC BY-SA).
If you would like to notify Biblica, Inc. regarding your translation of this work, please contact us at https://open.bible/contact-us.
This translation is made available to you under the terms of the
Creative Commons Attribution Share-Alike license 4.0.
You have permission to share and redistribute this Bible translation in any format and to make reasonable revisions and adaptations of this translation, provided that:
You include the above copyright and source information.
If you make any changes to the text, you must indicate that you did so in a way that makes it clear that the original licensor is not necessarily endorsing your changes.
If you redistribute this text, you must distribute your contributions under the same license as the original.
Pictures included with Scriptures and other documents on this site are licensed just for use with those Scriptures and documents.
For other uses, please contact the respective copyright owners.
Note that in addition to the rules above, revising and adapting God's Word involves a great responsibility to be true to God's Word. See Revelation 22:18-19.
2025-05-03

Source: http://ebible.org/hausa/ · eBible.org

Talk to us

Tell us where you read from, how the Bible has helped you, or what we could improve. We read every message.